Mun yaba da azamar sojojin Nijeriya a baya-bayan nan – Zulum

Gwamna Zulum

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yaba da ƙoƙarin sojojin Nijeriya dangane da suke yin azama a baya-bayan nan, inda suka fatattaki mayaƙan Boko Haram a ƙoƙarinsu na shiga garin Gwoza da yunƙurin datse hanyar arewacin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka a wata sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Malam Isa Gusau, a farkon wannan makon tare da bayyana ƙoƙarin da sojojin suka yi na fatattakar mayaƙan daga garin babban abin yabo ne.

“Gwamnan ya jinjina wa sojojin Nijeriya, musamman sojojin Bataliya ta 26 da ke garin Gwoza, a bajintar da suka nuna wajen fatattakar yan ta’addan tare da ƙwace makamai da dama, ranar Lahadin da ta gabata.

“Haka zalika, Gwamna Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojojin da ke aiki a ƙarƙashin Lafiya Dole dangane da nasarar da suka samu a wani artabun kwanton vauna tsakanin su da yan ta’adda a kan hanyar Monguno zuwa Gajiram da ke kusa da ƙauyen Jigalta a ranar Juma’a.

“Sojojin, waɗanda suke raka ’yan kwamitin kula da sake tsugunar da yan gudun hijira a ƙarƙashin Babban Antonin Jihar kana kuma kwamishinan Shari’a na Jihar Borno, sun nuna ƙwarewa, kishin ƙasa mai cike da karsashi a fafatawar da suka yi da yan ta’addan na kimanin awa guda.

A hannu guda kuma, Zulum ya yaba wa sojojin Bataliya ta 112 da ke zaune a garin Mafa bisa ƙoƙarin da suka yi na ceto babbar motar dakon kaya wadda yan ta’adda suka qwace daga hannun jama’a a kan hanyar Monguno zuwa Gajiram a jihar.

“Har wala yau, a wani samamen da sojoji suka gudanar tsakanin Mafa da Dikwa a ranar Asabar da ta gabata, sun yi nasarar damƙe motar da wasu ɓata-gari ke amfani da ita wajen kai wa yan ta’adda kayan abinci da na masarufi a dajin Sambisa da tsakiyar dare. Kana kuma sojojin bataliya 112 sun kama tarin makamai tare da baburan hawa a hannun mayaƙan,’ inji sanarwar.

Gwamnan Bornon ya ƙara da cewa, duk waɗannan nasarori da sojojin suka samu ya na nuna kishin ƙasa, karsashi da himmar da suke da ita wajen shimfiɗa hanyoyin sake dawo da cikakken zaman lafiya a jihar Borno.