Tinubu da ƙurar 2023 a Arewa

Tinubu

Daga FATUHU MUSTAPHA

’Yan makonni da suka wuce ne, Gidan Arewa, wato Arewa House, da yake a Kaduna ya bayar da sanarwar tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai zama babban baƙo mai jawabi a taron da take shiryawa na shekara-shekara, don tunawa da Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, na wannan shekara. Tun bayan da wannan sanarwa ta fito, aka fara cece-kuce a Arewacin ƙasar akan wannan zaɓi na tsohon sanatan.

Jim kaɗan bayan taron kuma sai ga wata sanarwar daga hukumomi na cewa, za a yi bikin taya jagoran na APC murnar zagoyawar ranar haihuwar sa, a jihohi uku na ƙasar nan, waɗanda suka haɗa da Kano, Abuja da Legas. Shi ma wannan shiri da ba a saba ganin kamar sa ba. Don haka ya janyo wani sabon cece-kuce, musamman daga wasu matasa da ke ganin babu wani dalili da zai sa a yi wannan taron a Arewa.

To, amma a haƙiƙanin gaskiya idan aka lura da yadda abubuwa ke tafiya a Nijeriya, za a fahimci cewa, waɗannan abubuwa na da alaƙa da shirin babban zave mai zuwa nan da shekara biyu. Alamu na nuna tun daga yanzu, abubuwa sun fara ɗaukar saiti, musamman in aka lura da yadda waɗannan abubuwa biyu suka faru.

Da farko dai, tsohon gwamnan bisa ga dukkan alamu ya gwada zurfin ruwan ne, kuma akwai shaidu da ke nuni da cewa ruwan ya zo masa iya ƙwauri, wato bai cinye shi ba, musamman in aka lura da yadda zuwan nasa ya samu maraba daga gwamnonin APC da ke Arewa maso Yammacin qasar. Kusan dukkannin gwamnonin APC na yankin, idan banda gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru el Rufa’i, wanda ya tura wakilcin mataimakiyarsa.

Wannan tarba da kuma rakiya da gwamnonin su ka yi masa, ya nuna alamun Tinubu ya yi wa dukkanin ’yan takarar APC a ƙasar tsayuwar gwamen jaki. Bisa ga dukkan alamu shi ne zakaran gwajin dafin da APC ke ganin za ta gabatar ga masu zaɓe a kakar zaɓe mai zuwa.

To, amma kuma wani abu da ya fara janyo hankali shine, ƙin zuwan da Gwamnan Kaduna ya yi. Wannan kuwa ya sanya mutane na ganin lallai da walakin goro a miya. Abin mamakin shi ne, Gwamna el-Rufa’i na cikin ‘yan gaba-gaba wurin kira ga mulki ya koma Kudu a zaɓe mai zuwa. Sai dai ana ganin ƙila gwamnan na ƙoƙarin nema wa abokinsa, Gwamna Kayode Fayemi, takara ne.

Sai dai kuma akwai wasu da ke ganin gwamnan na haka ne, saboda a taya shi da tsada ne, musamman ana ganin yana cikin masu fatan su nemi mataimakin shugaban ƙasa in mulki ya koma kudu. Wannan ya sa wasu ke ganin na cikin dalilan da ya sanya gwamnan ke nuna jan wuya ga takarar ta Tinubu.

To, amma kuma ba anan ta tsaya ba; ana ganin akwai alamun manya a Arewa da dama na ganin tafiyar ta sa akwai alamun sa’a, wanda ya ƙara zama tagomashi ga tafiyar ta sa. A dai lokacin wannan taro an hango tsohon gwamnan Kano, kuma tsohon Ministan Tsaron ƙasar, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, a wurin taron suna ganawa da takwaran nasa. Wannan ma ya qara sanya wa mutane na ganin lallai wannan tafiya akwai alamun nasara a ciki.

Na farko dai ba a san Kwankwaso da halartar irin waɗannan taruka ba. Na biyu kuma ana kyautata zaton da walakin goro a miya, tunda idan ba rami, me ya kawo rami? Wannan halartar taro da Kwankwaso ya yi da kuma barin wurin taron da ya yi a daidai lokacin da Tinubu ya gama jawabin sa, ya tabbatar da cewa, da wata a ƙasa. Mutane na ganin qila dai a yi abin nan da Hausawa kan ce, idan ka ga kare yana shinshinar takalmi, to xauka zai yi.

To, amma wani babban ƙalubalen da mutane ke kallo a wannan batu na ko akwai alaqa tsakanin Kwankwaso da Tinubu shi ne, batun yadda alaqa ta lalace tsakanin tsohon gwamnan da magajinsa, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Wasu na ganin zai wuya abokan tafiyar biyu su ƙara zama a inuwa ɗaya. Don haka zai wuya Kwankwaso ya yi gigin koma wa tsohuwar jam’iyyar tasa ta APC, wacce ya yi ma Sanata. Wasu kuma na ganin, ai ranar biyan buqata rai ba a bakin komai yake ba. Don haka, don wuya ba za a bar daɗi ba. Hasali ma ai ba a yin maƙiyin dindindin ko masoyi na dindindin a siyasa. To, amma dai Hausawa kan ce, dole ne a ci kasuwa da maqiyi. Saboda haka ba wata matsala, don sun sake jonewa a jam’iyyar ta APC.

A wata sabuwa kuma, tun bayan da aka kammala bikin murnar tunawa da ranar haihuwar Jagaban Borgun a Kano, ake ta tada qura. Cikin masu tada wannan ƙura akwai shugaban wata ƙungiya mai rajin kare muradun Arewa, wato Sheriff Nastura. Nastura dai ya nuna takaicin sa bisa ga irin wannan maraba lale da Arewa ta nunawa Tinubu. Ya zargi Tinubu da hannu a dukkan zanga-zangar da ‘yan Kudu ke yi suna kaiwa Hausa mazauna can hari. Wannan zargi mai nauyi dai ya samu goyon bayan wasu manya a Arewa, a yayin da wasu ke ganin wannan kawai zargi ne mara kan gado. Masu wannan ra’ayi na babu hannun Asiwaju a ciki.

Sun yi nuni da cewa, in har da hannun sa mai yasa masu zanga-zangar #EndSars suka fi kai wa kadarorin sa hari?
A yanzu dai Arewa ta rabu akan masu ganin kada ‘yan Arewa su nemi takarar Shugaban Ƙasa da masu ganin kada Arewa ta miqa mulki ga ‘yan kudu. To, amma da ma an ce idan ka ji makaho ya ce zo mu yi wasan jifa, to bisa ga dukkan alamu ya taka duwatsu ne. Ana ganin wannan fitar barden guza da Tinubu ya yi, ko shakka babu akwai alamun da abinda ya taka. Da dama na kyautata zaton lallai tsohon gwamnan ya fara shiri ne tun da kafin dare ya yi masa.

Haka kuma a ɗaya vagaren kuma, akwai masu ganin ba samun takarar Tinubu ce babbar matsalar ba. Babban ƙalubalen da ke gaban sa shi ne daga wane yanki daga yankunan Arewa guda uku zai fitar da mataimakin sa. Domin kuwa a yanzu haka ana kallon wasu gwamnoni sun fara kyarkyara na neman a ba su muqamin mataimakin Shugaban Ƙasa. Akwai dai su Malam Nasiru da ake ganin yana neman wannan muƙami ne. Akwai kuma gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje, wanda ake ganin yana kai gwauro ya kai mari yana ta ina aka saka ina aka aje da ɗan takarar. Ana ganin wannan toshi da gwamnan ke kaiwa, bawani abu bane illa kayan mun gani muna so ne.

Sai dai dama na ganin lokaci ya yi da ya kamata ace an fito da mataimakin daga Arewa maso Gabas. A wannan yanki kuma wasu na hasashen komawar Yakubu Dogara tsohon Sifika na Majalisar Wakilai ta Ƙasa zuwa APC na da alaƙa da burin sa na zama mataimakin shuganan ƙasa. Wa su kuma na kallon cewa, in har so ake a ƙulla wani abin ku zo ku gani, to abu mai kyau daga wannan yanki, a ɗauko tsohon Shugaban Hukumar Hana Cinhanci da Rashawa ta Ƙasa wato EFCC, Malam Nuhu Ribaɗu, musamman saboda an shaida da irin nagartar sa da jajircewar sa akan yaƙi da cinhanci da rashawa.