Bazoum ya naɗa sabbin ministocin sa a Nijar

Shugaba Bazoum

Daga UMAR M. GOMBE

Sabon Shugaban Ƙasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya naɗa sabbin ministoci da za su yi aiki a gwamnatin sa, kamar yadda sanarwar da Sakataren Gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Larabar da ta gabata.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an naɗa sabbin ministoci 33, kuma shida daga cikin su mata ne. Hakan na nufin adadin ministocin ya ragu idan aka kwatanta da ministoci 43 da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaba Mahaman Issoufou.

Naɗin ministocin ya faru ne a yayin da sabon Fira Ministan Jamhuriyar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadu ya sha rantsuwar kama aiki.

Ministocin su ne kamar haka:

Ministan Harkokin Waje – Hassoumi Masaoudou

Ministan Ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa – Rhissa Ag Boula

Ministan Tsaro – Alkassoum Indattou

Ministan Cikin Gida – Alkache Alhada

Ministan Koyon Ayyukan Hannu – Kassoum Mahaman Moktar

Ministan Illimi Mai Zurfi – PHD Mamoudou Djibo

Ministan Kiwon Lafiya – Dr Illiassou Idi Mainasara

Ministan Ma’adanai – Mme Ousseini Hadizatou Yacouba

Ministan Sadarwar Hanyoyin Zamani -Hassane Baraze Moussa

Ministan Sufuri – Oumarou Mallam Alma
Ministan Agajin Gaggawa – Lawan Magaji

Ministan Kiwo Kakakin Gwamnati – Tijani Abdukadri

Ministan Gine-Gine – Hamadou Adamou Souley

Ministan Shari’a – Dr Biubacar Hassan

Ministan Yaɗa Labaru da Hulɗa da Sauran Hukumomi – Zada Mahamado

Ministan Kuɗi – Ahmat Jidoud

Ministan Kasuwanci da Masana’antu – Gado Sabo Moktar

Ministan Ayyukan Noma – Dr Alambedji Abba Issa

Ministan Zane-Zane, Gidaje da Tsaftar

Muhali – Maizoumbou Laoual Amadou

Ministan Fasali – Abdou Rabiou

Ministan Man Fetur da Makamashi – Mahamane Sani Mahamadou

Ministan Kula da Al’adu, Yawon Bude Ido da Ayyukan Hannu -Mohamed Hamid

Ministan Inganta Ƙasa da Cigaban Cigaban Karkara – Maman Ibrahim Mahaman

Ministan Kula da Mata Da Kariyar Ƙananan Yara – Mme Allahoury Aminata Zourkaleini

Ministan Illimin Qananan Makarantu – Dr Rabiou Ousman

Ministan Albarkatun Ruwa – Adamou Mahaman

Ministan Qwadago – Mme Ataka Zaharatou Aboubacar

Ministar Muhalli da Yaqi da Kwararar Hamada – Mme Garama Saratou Rabiou

Ministar Kula da Ayyuka da Kariyar Al’umma – Dr Ibrahim Boukary

Ministan Matasa da Wasannin Motsa Jiki – Sekou Doro Adamou

Ƙaramin Minista a Ma’aikatar Kuɗi – Mme Gourouza Magaji Salmou

Ƙaramin Minista a Ma’aikatar Cikin Gida – Dardaou Zaneidou

Ƙaramin Minista a Ma’aikata Harkokin Waje – Youssouf Mohamed Almoktar.