Shugaba Ouattara ya ce Gbagbo da Ble za su iya dawo wa gida

Alassane Ouattara

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasar Kwaddebuwa, Alassane Ouattara ya ce tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo da kuma jagoran matasa ’yan gani-kashe-ni da ke mara masa baya wato Charles Ble na iya komawa gida a duk lokacin da suke buƙata, bayan da kotun duniya ta ICC ta wanke su daga laifukan da ake zargin su da aikatawa.

Shugaba Ouattara, wanda ke jagorantar taron majalisar ministocin ƙasar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce bayan dawowar sa a gida tsohon shugaba Laurent Gbagbo zai ci moriyar illahirin haƙƙoƙin da doka ta ce a bai wa tsohon shugaban ƙasar.

A game da ɗaukar nauyi da kuma ɗawainiyar tsohon shugaban da iyalan sa domin komowa gida kuwa, shi ma wannan zai fito ne daga Baitul-malin ƙasar a cewar shugaba Ouattara.

To amma sai dai shugaban ƙasar bai bayyana makomar hukuncin ɗaurin shekaru 20 da wata kotu ta yanke wa Laurent Gbagbo bayan samun sa da hannu a fashin da aka kai wa bankin ƙasashen yammacin Afirka na BCEAO, a lokacin da ake tsakiyar yakin basasar ƙasar ba.

A ranar 31 ga watan jiya ne kotun ta ICC ta wanke Laurent Gbagbo da kuma Charles Ble Goude daga illahirin zarge-zargen da ake yi masu, matakin da ke share masu fagen komawa gida Kwaddebuwa idan suna buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *