Muryar Jama’ar Jigawa ta buƙaci a taimaka wa ‘yan sintiri

Gwamna Badaru

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
 
Muryar Jama’ar Jihar Jigawa, wato Jigawa Forum tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki a jihar sun yi wani gagarimin taro da nufin taimaka wa ƙungiyar ‘yan sintiri ta jahar.

An gudanar da taron ne a ɗakin taro na otel ɗin Three Star da ke fadar Gwamnatin Jihar ta Jigawa, Dutse, a makon jiya.

Ƙungiyar Muryar Jama’ar Jigawa wato Jigawa Forum ta bakin shugaban ta Farfesa Muhammed Tabi’u ta buƙaci gwamnatin jihar ta Jigawa da ta agaza wa ƙungiyar sintirin da kayan aiki da suka haɗa da kayan sarki wato kaki da motocin hawa da baburan hawa da kekunan da kuma cocilan.

Tabiu ya ce akwai buƙatar gwamnatin jihar da masu hannu da shuni su agazawa ƙungiyar saboda irin gudunmawar da su ke bayarwa wajan tsaron dukiya da lafiyar al’umma.
Ya ƙara da cewar ‘yan sintiri su ne su ka fi kusa da jama’a sun fi duk sauran jami’an tsaro sanin masu aikata laifi kasancewar sune su ke kusa da jama’a.

Da yake na sa jawabin a wajen taron gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya ce gwamnati ta na sane da irin ƙoƙarin da ‘yan sintirin suke yi ta fuskar samar da tsaro a jihar.

Ya ci gaba da cewa gwamnati za ta yi iyakacin bakin ƙoƙarin ta wajen taimakawa qungiyar tsaron ta sintiri ta jiar ta jigawa.

A nasa jawabin kwamandan ƙungiyar sintirin na ƙasa Kwamared Usman Muhammed Jahun ya yaba wa ƙungiyar Muryar Jama ar jihar Jigawa da ta shirya taron da kuma ita kanta gwamnatin jihar bisa namijin ƙoƙarin ta na taimaka wa ƙungiyar.