Gwamnan Zamfara ya bayyana takaici kan gallaza wa ’yan Arewa

Gwamna Matawalle

Daga FATUHU MUSTAPHA a Abuja

A Alhamis da ta gabata Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Bello, Matawallen Muradun, ya fitar da wata doguwar ƙasida da yake nuna takaicinsa a game da yadda abubuwa suke tafiya a Nijeriya musamman kan yadda ake gallaza wa ’yan Arewa wasu yankunan ƙasar.

Ƙasidar da aka raba ta ga manema labarai, tana ɗauke da sa hannun gwamnan na jihar Zamfara kai tsaye ne, inda ya nuna yana cike da alhini a game da yadda abubuwa suke ƙara tavarɓarewa a ƙasar.

“Na rubuta wannan ƙasida ne a matsayina na jagora kuma ɗan Arewa, domin wannan ba lokaci ba ne da za mu bari bambancin siyasa ya rufe mana ido mu ƙi faɗar gaskiya, musamman ganin masu yi wa ƙasar nan zagon ƙasa sun tashi haiƙan wurin ganin sun kawo rikici da rarrabuwar kai.

“A yadda mu ke tafiyar da siyasar ƙasar nan a karkace, wasu za su yi zaton waɗannan kalamai bai kamata su fito daga bakin gwamnan da ya fito daga jam’iyyar adawa ba. Amma na zavi na tsage gaskiya, duk kuwa da Ina sane da matsayina na ɗan PDP, saboda fatan da nake na ganin Nijeriya ta kafu a matsayin qasa ɗaya mai ɗorewa.”

Da ya ke nuna takaicinsa akan yadda aka maida rayuwa da dukiyoyin ‘yan Arewa ba a bakin komai ba a kudancin ƙasar, Gwamna Matawalle ya koka akan rashin dattako da ya ce manyan Kudu ke nunawa, savanin yadda takwarorin su na Arewa ke ƙoƙarin ganin sun kare mutanen Kudu da ke zaune a Arewa.

“Abu ne mai ciwo irin yadda ake gallaza wa Arewa da ‘yan Arewa a kudancin ƙasar nan. A yayin da mu muke ƙoƙarin ganin mun kare ƙima, mutunci, rayuka da dukiyoyin mutanen Kudu da ke zaune a Arewa, su a can abin ba haka ya ke ba. Abin takaicin shi ne, yadda duk da wannan abin takaicin da ke faruwa akan ‘yan Arewa a Kudu, amma kuma manyan Arewa sun ja bakin su sun yi gum sun ƙi magana. Ba kamar takwarorin su na Kudu ba da ba sa ganin zarau sai su tsinka.”

Gwamnan kuma ya gargaɗi dattawan da ke kudanci da su sani fa shiru shiru fa ba tsoro bane, gudun magana ne. Ya bayyana cewa in har ɗan Arewa ba shi da damar ya zauna a duk inda ya ga dama a Kudu, to su sani mu ma fa a nan Arewa ba za mu zauna mu zura ido na ku mutanen na harkar su ba tare da wata matsala ba. Ya kamata su sani, in ji gwamnan, mai tsoron ta mutu shi ke maho.

Ya ƙara da cewa “A kan Idon mu aka riƙa kashe Hausawa a Sasa, aka ƙona dukiyoyin su aka kore su daga wuraren sana’ar su, kuma don rashin kunya ma aka nemi a ɗaura musu laifin. Ba a jima ba yau kuma sai ga shi wasu ‘yan ta’adda sun kashe wasu Hausawa a Imo. Ya kamata a sani, duk da yake muna fatan zaman lafiya a ƙasar nan. Amma fa wannan abu ba zamu yadda ya cigaba da faruwa ba. Domin kuwa rai bai fi rai ba. Ya kamata ‘yan Kudu su sani, in har wata rigima ta ɓarke, su za su fi kowa asara, saboda sun zuba kadarorin su a Arewa, fiye da yadda ‘yan Arewa ke da kadarori da jari a Kudu.

Gwamnan ya kuma ƙara bayyana cewa, abin takaice ne cewa duk da an san waɗannan ‘yan ta’adda amma kuma ana kallon su an bar su sun zama wasu shafaffu da mai, har ma hukumomi sun kasa ɗaukar wani mataki da za iya zama izna ga na gaba.

Da yake bayyana ra’ayin sa akan zanga-zangar da wasu suka gabatar a birnin Landan akan zuwan Shugaba Buhari asibiti, ya bayyana cewa, “a matsayi na na ɗan Arewa, Ina Allah wadai da yadda wasu ɓatagari suka nemi cin zarafin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, waɗanda kowa ya san tsananin qiyayyar su ga Arewa ce ta sanya suka yi wannan abu. Abin da su ka yi ya sava da ƙa’ida, ƙauyanci ne, kuma bai hau doran tsarin dimokaraɗiya ba. Sam wannan ba hanyar da dimokaraɗiya ta tanada domin mutum ya nuna rashin amincewar sa ba ne. Zanga-zanga ta dimokaraɗiya, tana magana ne akan abu ba akan mutum ba.”

Daga ƙarshe ya yi kira ga manyan Arewa da su tashi su kare yankin su, kamar yadda takwarorin su na Kudu su ke yi. Ya kamata mu sani daga wannan lokaci ba sani ba sabo, kowa ya yi mana kan kara, to kuwa za mu yi masa na itace, domin ya shekara yana ƙonawa.