Wake ɗaya ɓata gari: Allah sarki ’yar jarida!!!

Daga KWAMRED IBRAHIM ABDU ZANGO

Akwai wata ’yar jarida wacce ta koyi aikin jarida a wata kafa ta rediyo da wani hamshaƙin ɗan jarida ya koya mata, wato aikin jaridar rediyo. Kullum ka je za ka same ta a ƙasa, shi kuma yana kan kujera! Ya kan ba su damar hirar siyasa da irin ’yan siyasar baka ɗin nan. Ta haka waccan ’yar jarida ta koyi yadda ake hira ta cikin radiyo!

Ni a tunanina gani nake cewa, a makaranta ake koyar da wannan babbar sana’a ta jarida tunda akwai fannin wani darasi da ake kira Maskom, wato ‘Mass Communication’. Wannan sashe ne na koyon ƙwarewar zama dan jarida kuma akwai difloma har zuwa digiri da kuma digirin-digirgir. Wannan na san haka, domin Ina da malamina Marigayi Farfesa Balarabe Maikaba, Allah Ya jiƙan bawan Allah mai ƙoƙarin ganin dukkan ɗalibinsa ya zama kamar yadda yake. Gaskiya kasancewa ta tare da Marigayi Maikaba shekara da shekaru sai ya ba ni damar gane waye ɗan jarida da kuma yaya ya kasance ɗan jarida!

Na faɗi haka ne ganin yadda na ga wata ’yar jarida takan ɗauki aikin kamar ita ce ’yar siyasar da ke mahawara da wanda take rikodin da shi! Na kan ji tana tambayoyi waɗanda gani take kamar ana yin wani abu da ake kira ‘debate’ a turance tsakanin ’yan siyasa a junansu.

Ni ce nake aikin jarida ya kan ba wa kowa damar kare kansa ko bayyana ababen kirki da ya yi wa jama’a ko wanda yake cikin ƙudurorin jam’iyyarsa ko wani zargi da aka yi masa, domin kare wannan zargi? Misali; lokacin wani gwamna an rarraba gidajen gwamnatin jiha an kasa su gida biyu, wannan kusan shekarar 1992 – 1993, an bar kaso ɗaya na gwamnati, kaso ɗayan an ba wa abokai da yan’uwa.

Akwai filaye da suke yamma da gidan gona da kuma katafaren filin nan na bajekoli shi ma duk an yi watanda da su cikin ’yan lokuta ƙalilan. Sannan shi dai wancan mai mulki a lokacinsa ya sayi wani otel ya maida shi asibiti, wanda a wannan tsawon lokaci ana amfanar sa sosai da sosai. Ka ga haka lamari yake, kuma kowa da zamaninsa.

An yi Gwamnan da ya yi ƙanƙanin lokaci, amma ya yi amfani da damarsa wurin mayar da wata sinima cikin ƙwaryar birnin Kano wacce muka samu labarin gina ta tun shekarar 1952 – 1955, wacce a da jama’a sun yi juyayin yin ta, amma babu yadda za su yi, domin lokacin masu jan kunnuwan ne; wane Nasara balle Afunu?

Amma duk da haka, wani gwanda shi ma da bai daɗe ba, ya yi awon gaba da sinima ɗin duk da cewa ta hamshaƙan mutane ne masu faɗa-a-ji, domin kyautata wa jama’a da suke yi. Wannan kowa ya sani. Wannan sinima kamar waccan da ke wajen birni ita ma an mayar da ita asibiti mai inganci na mata, wato na haihuwa. Ka ga babu tantama kowanne mai mulki yana da daftarin ikonsa kuma lokacinsa. Na kan ga shi dai wancan gwamna wanda ya yi abin kirki ya so ya ƙwace wani katafaren fili a can yamma da otel ɗin nan da ake kira ‘Daula Hotel’.

Shi wannan fili Turawa ne da ’yan gata suke wani wasa wai shi ‘Hokey’. Haka ne sunan, oho! Kalmar Turanci ce, ba ni da masaniya sosai akansa, amma dai abin ya gagari Kundila cewar Bahaushen Kano!

To, a taƙaice dai ’yar uwa ’yar jarida tana takura maganganunta bai sa wai filin idi da badala da dai wurare kamar Gidan Zoo, dukkan abubuwan da ɗan jarida yake nema na hujja an bayar. Misali; an samo lokacin da aka rushe masallatai barkatai, amma babu wanda ya ce uffan har gobe.

To, idan an yi kantuna a masallacin idi laifi ne bayan an ga shaguna da otel-otel a masallacin da ya fi ko’ina daraja da xaukaka a duniya, wato Ka’aba? Masallacin Fagge, Janar Gowon ya zo buɗe shi kuma an yi kantuna fiye da kuma shekaru 40 a bayansa. Shi ma wannan laifi ne? Kuma mene ne laifin cewa, yanzu Kano ta zama wata Dubai a Nijeriya. Laifi ne? Mene ne ilimi, kuma ba a koyar komi a Nijeriya sai an fita, domin almubazzaranci kawai?

Tun kafin a haifi uwar baduku borin turke yake da jaka, haka tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta.
Ashe tunda haka shine ma’ana ya zama dole a sanda cewa, kowanne Allazi da nasa Amanu. Kuma da wuya komi namu na Kano ya fice salim-alin ba tare da tsangwama ba. Duk Gwamnan da ya zo tun daga 2003 zuwa yanzu ya kan samu suka, kususan daga ’yan dagaji, domin wataƙil tallan kansu suke yi, domin samun abin sawa a baka.

Fatana ga sabuwar ’yar jarida shine, ta tsaya domin su wane an yi, ya yi lokacin NPN yau sai buzunsu, inji Baba…

Kwamred Zango ya rubuto ne daga Kano a Tarayyar Nijeriya. Za a iya samun sa a wannan lamba; 08175472298.