Manufar noma a Arewa: Hannunka mai sanda da gwamnati ke ta yi

Tun lokacin zuwan gwamnatin wannan lokaci a shekara ta 2015 ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, ta karkata manufar tattalin arzikin Nijeriya kusan kacokan daga ɓangaren ɗanyen mai zuwa kan harkokin noma, inda gwamnatin ta buɗe wuta wajen ingaza dukkan wani sha’ani da yake da alaƙa da fannin noma ta fuskar ɗaukar matakai daban-daban.

Gwamnatin Buhari ta samar da shirye-shirye da tsare-tsare kala-kala, domin cimma wannan buri kama daga ƙarfafa samar da rance mai sauƙi ga manoma zuwa ba su tallafin noma. Haka nan gwamnatin ta kuma tabbatar da rufe iyakokin qasar da hana shigo da shinkafa, wanda hakan ya bai wa manoman shinkafa dama mai ɗimbin yawa.

A zahirin gaskiya duk da cewa, an samu ƙorafe-ƙorafe kan wannan manufa ta hana shigo da shinkafa cikin gida Nijeriya, musamman saboda kasancewarta kusan abinci da aka fi ci a faɗin ƙasar, amma wannan wata dabara ce, wacce za ta iya bunƙasa arzikin yankin Arewa da al’ummarta.

Abin nufi a nan shi ne, duk wata wahala da za a sha sakamakon rashin shigo da shinkafa ’yar waje, a ƙarshen al’amari zai taimaki jama’ar Arewa ne, domin kuwa mutanen yankin ne ke noma shinkafa. Don haka duk wani ɗan Nijeriya da zai buƙaci ci ko amfani da shinkafa, tilas ne ya neme ta a yankin Arewa, dole ne ya kawo kuɗin sayenta zuwa ga yankin Arewa. Idan kuma xan Arewa ne, tilas ne ya bar kuɗin sayen a yankin na Arewa. Tabbas hakan zai ƙarfafa arzikin yankin ne ga mutanensa.

Babbar hikimar da ke cikin wannan al’amari ita ce, yadda yankin Kudancin Nijeriya ke bugun ƙirji da ƙafafa akan arzikin man fetur, haka shi ma yankin Arewa zai yi alfahari da bugun ƙirji da arzikin noma matuƙar tsarin da aka ɗauko ya ɗore a yadda ya ke ɗin nan. Za a iya cewa, hakan hangen nesa ne, wanda ko da a yanzu ana jin raɗaɗin matsin tattalin arzikin aljihu sakamakon ɗaukar waxannan matakai, amma a nan gaba tamkar gata aka yi wa Arewa mai tarin yawa, idan aka yi la’akari da yadda tattalin arzikin duniya ke tafiya. Ta yiwu ana shan wahalar ne tare da ’yan Kudu a yanzu, amma tabbas a ƙarshe ɗan Arewa sai ya fi kowa darawa.

Babban abin da ya fi dacewa ’yan Arewa su yi shi ne, su tsaya tsayin daka wajen mayar da hankali ga dogaro kan noma da kuma zuba jari a cikinsa, ba wai kawai su zura wa gwamnati idanu ita kaɗai ba. Noma sana’a ce, wacce kowa zai iya yi, ba sai gwamnati ba, kuma sana’a ce, wacce ke da makoma mai kyau da ɗirewa a ko’ina a duniya. Za a iya cewa, haka ne maƙasudin hujjar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na karkata arzikin ƙasar ga harkokin noma.

Lokaci ya wuce da wata ƙasa za ta zauna tana jira da dogaro arzikin mai ta fuskar kuɗin shiga, idan aka dubi yadda arzikin duniya ke tafiya. Kullum farashi a kasuwar mai yana faman hawa da sauka ne, darajar mai faxuwa take yi kuma kwarijinsa daxa raguwa yake yi a ko’ina a duniya da ma cikin ƙasa. Ta yiwu za a kai munzalin da idan ma an haƙo man, sai dai a sayar da shi a cikin ƙasa kawai, don amfanin yau da kullum, amma wataƙila za a iya rasa ma kasuwar da za a kai shi a duniya.

Idan ɗan Arewa ya yi la’akari da wannan, to lallai ba ƙaramin gata Gwamnatin Tarayya ta yi masa ba, domin hatta kuɗaɗen da take fitarwa, domin bayar da rancen noma ko tallafin noma, kaso mafi yawa sosai yana tafiya hannun ’yan Arewa ne, domin sune suka fi yin noma a yankinsu. Idan kuwa ɗan Arewa ya yi sakaci da wannan dama, to ya sani cewa, gwamnatocin Kudancin ƙasar da masu hannu da shuninsu sun hango wannan lamarin kuma sun fara zuba jarin noma a yankinsu, wanda hakan ke nufin cewa, idan ɗan Arewa bai tashi tsaye ba, za a iya ƙwace masa abin da ke hannunsa, idan ya so sai ya koma ɗan ƙwadago a cikin sana’ar noma kaɗai, kamar yake faruwa a cikin wasu sana’o’in.

Lallai ne ɗan Arewa ya gane wannan gata da Gwamnatin Tarayya ta yi masa a wannan lokaci kuma ya yi amfani da damar da ya samu tun wuri. Idan kuma ba haka ba, kada ya yi kuka da kowa a nan gaba, wato lokacin da wannan zinariyar damar ta riga ta kufce daga hannunsa!