Muhimmancin aure a addinin Musulunci da rawar da iyaye za su taka akan tarbiyyar yara (2)

Daga BASHIR ABDULLAHI EL-BASH

A mafi yawan lokuta iyaye ba sa zama su tattauna da ’ya’yansu, domin gano halaye da ɗabi’un waɗanda su ke son aura. Daɗi da ƙari, a mafi yawan lokuta zaɓin iyaye bai cika gamsar da ’ya’ya ba wanda hakan ke haifar da matsalolin da ke haddasa mutuwar aure da dama. Ya na da kyau iyaye su na zama da ’ya’yansu su yi magana da su tunda farko su gano abin da su ke so a ba su dama su yi magana da wanda ake son aura musu su fahimci juna kafin kaiwa ga batun aure. Ya zama wajibi iyaye su kasance a kowane lokaci, ka da su ƙyale yara su kaɗai har sai sun gano shin sun cancanta da juna ko a’a.

A wasu lokutan kuma yara kan samu kansu cikin soyayya da wanda ba Musulmi ba, su kuma faɗawa iyayensu su na son su yi aure, amma iyayen su ƙi sai dai su nemi su tilasta musu auren wanda babu wata soyayya a tsakaninsu. Yanke alaƙar soyayya tsakanin saurayi da budurwa bayan ta jima da ƙulluwa ba abu ne mai daɗi ba tayadda ya ke haifar da matsaloli kala-kala. Domin kuwa ko da an raba an aurar da su ga wanda babu soyayya a tsakani a wasu lokutan akan samu su kan keɓe da juna a wani wurin su yi soyayyarsu. Kenan tilasta aure babu soyayya ba shi ne mafita ba, mafita shi ne abin hanyar laluma a yi musu nasihohi idan sun aikata ba daidai ba domin su dawo hanya.

A wasu lokutan kuma wasu iyayen su kan yi ƙoƙarin ganin wanda ‘ya’yansu su ka faɗa soyayya da su sun Musulunta. Wannan abu ne mai kyau, sai dai duk da haka iyaye su na tabbatar da cewa bayan sun karɓi Musulunci sun kuma maida hankali wajen neman ilimin addinin Musulunci da sanin hukunce-hukuncen aure da dokokinsa domin ganin zuriyar da za a haifa ta zama zuriya ta gari mai cike da imani da tsoron Allah. Sakamakon akwai waxanda su ke Musulunta a sanadiyyar soyayya shikkenan sai su zama Musulmai a suna amma ba sa kiyaye dokokin addinin saboda ba su nemi iliminsa sun sani ba. Wanda daga ƙarshe za a yi ta rigingimu da fitintinu a gidan aure yara su na tashi babu tarbiyya su na zama rabi da rabi cikin addini daga qarshe ma auren ya wargaje.

Saboda haka, wannan na daga cikin abubuwan da ke haddasa yawan mace-macen aure. Idan mu na son aure ya dinga nagarta da ɗorewa dole sai mu na sa Allah a farko mu na jin tsoronsa da kiyaye dokokinsa a duk abin da za mu yi. Hakan zai ba mu damar samun nutsuwa da zaman lafiya da ɗorewar aure cikin girmama juna da ganin kimar juna.

A wasu lokutan kuma mata da dama su kan fara rayuwar aure a cikin gidajen iyayen mazajensu wanda hakan kan haifar da ruɗani da tashin hankali kala-kala. Akan rinƙa samun saɓani da rashin zaman lafiya a tsakanin mata da uwar miji. Wasu lokutan uwar miji kan zamar da matar miji tamkar baiwa duk wani aiki da wahalwahun gida ita za ta jifgawa kuma duk da haka ba za ta gode ba, kuskure kaɗan za ta hauta da faɗa da zage-zage da kai ƙararta gun ɗanta. A wasu lokutan kuma matar mijin ce kan rena uwar mijin ba ta kuma son ko kaɗan mijin nata ya yi wa uwarsa amfani ko na Naira biyar. A wasu lokutan kuma dangin matar ko na mijin su ke shiga tsakani su haddasa fitina da tashin hankali a tsakanin matar da uwar mijin tayadda za ta kai ga gaba da rabuwar auren. Hanya mafi sauƙi ta samun zaman lafiyar aure shi ne kaucewa haɗa zama gida ɗaya tsakanin mata da surukanta.

Kowane ɗa aljannarsa tana ƙarƙashin ƙafar iyayensa. A saboda haka idan lalura ta kama ba makawa sai an zauna gida ɗaya da iyayen miji to akwai buƙatar uwar miji ta zama mai kula sannan ita ma matar miji ta zama mai kula. Kowa ya yi ƙoƙarin sauke haƙƙin kowa babu cuta ba cutarwa. Uwar miji ta rime matar ɗanta a matsayin ‘yarta. Matar miji ta riqe uwar mijinta a matsayin Uwarta. Domin an riga an zama ɗaya kowa ya zama ɗan’uwan kowa. Auratayya ta shiga an samu haɗakar zuriya da dangi an zama ‘yan uwan juna. Mu’amalantar juna cikin girmamawa da mutunta juna bisa gaskiya da adalci shi ne masahala da zaman lafiyar ahalin biyu. Iyaye su guje wa yin katsalandan cikin zamantakewar auren ɗansu da matarsa idan gida ɗaya ya haɗa sai dai a matsayinsu na iyaye su zamto masu ba su shawara da ɗora su akan hanyar da ta dace.

Mafi yawan aure a wannan zamani matsalolinsa na faruwa ne sanadiyyar biyewa son ƙyale-ƙyalen duniya wanda ya ke lalata alaqarmu da Allah. Ba shakka mu ne mutane mafiya muhimmanci ga ‘ya’yanmu, akwai buƙatar mu ɗora su akan hanya mai kyau wacce rayuwarsu za ta zama mai inganci a lokaci na gaba. Mu ba su ilimi mai inganci na addini da na boko mu ba su ‘yanci yadda ya kamata mu kula da rayuwarsu daidai iko mu sanya musu su riqa jin tsoron Allah da ganin girmansa a cikin zukatansu su ɗoru akan tarbiyyar bin umarnin Allah da hanuwa da haninsa, sanyawa yara son duniya babu abin da zai haifar mana sai lalata gobensu. Mu sanya musu son Allah da Manzonsa (SAW) su ginu akan tarbiyyar addininmu na Musulunci shi ne zaman lafiyarmu da kyautata rayuwarsu ta gobe.

Idan ba mu tarbiyantar da ‘ya’yanmu akan tsoron Allah da bin tafarkin addinin Islama ba, to a duk lokacin da su ka taso mu ka tura su cikin al’umma su ka fara zuwa jami’a da kamfanoni wurin aiki to za su haɗu da abokai waɗanda ba ma Musulmai ba ne za su kuma ɗora su akan irin tarbiyyar da su ke kai, kafin mu ankara yara za su zama fasikai mashaya ƙwayoyin maye da ɓata lokutansu a gidajen rawa da wuraren holewa da shaƙatawa da zinace-zinace, wanda daga nan za a fitine su akan addinin su, zuciyarsu za ta bushe. Amma idan mu ka ba su tarbiyyar addinin Musulunci mu ka kuma nusar da su muhimmancin zaɓar mata nagari, ba shakka rayuwa za ta yi kyau.

Allah ya faɗa cewa: “Mata nagari su ne masu biyayya da tsare sirrin mazajensu da neman kariyar Allah”. Su na yin aiki tuƙuru akan biyayyar aure sannan kuma su kan yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan matsalar gida.

Saboda haka iyaye su zamto a ankare game da buƙatun ‘ya’yansu. Idan yara su ka zo da buƙatar aure to a tsaya a tsinake a taya su nemo abokan zama nagari. Waɗanda kuma ba su nuna sha’awar yin aure akan lokaci ba saboda su na son su cimma wasu buruka a rayuwarsu to ka da a matsa musu a ce sai sun yi aure somin hakan zai iya haifar da matsala, a ƙyale su a duk lokacin da su ka shirya sai a taya su nema musu abokan zama nagari.

Iyaye su sani yaransu maza su kan haɗu da mata da dama a makarantu da wuraren aiki. Kowa a cikinsu ya na da sha’awa da buri ga kowa, kowa ya kan yi shiga da ado ya burge kowa. A irin wannan yanayi gina su akan taƙawa da tsoron Allah shi ne mafita tayadda za su haƙurƙurtar da kansu buƙatar juna sai ta hanyar da shari’a ta yarda. Ka da iyaye su dage sai ‘yarsu ta yi karatu ta samu aiki mai kyau kafin su yi mata aure domin duk matakin da za ta kai dole dai ƙarƙashin namiji za ta dawo.

Saboda haka iyaye su himmatu wajen yi wa ‘ya’yansu zaɓi nagari wanda ko da bayan auren inda dama za su yi karatunsu su na da aurensu su ma mazan za su samu nutsuwa da kauda kai ga matan da ba nasu ba sannan za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da zuri’a tagari a cikin al’umma. Wannan wasu ne daga cikin haƙƙi da nauyin da ke kan iyaye game da ‘ya’yansu, ba wai su samar da tarbiyyar Musulunci ba a gidajensu har ma da tarbiyyantar da ’ya’yan nasu su ma su wanzar da tarbiyyar Musulunci a gidajensu.