Yana da kyau marubuta su ƙirƙiro da hanyar mayar da rubutunsu kan sauti – Farfesa Sufyan Wase

“Ya kamata marubuta su riƙa tafiya da zamani”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuta sun kasu kashi daban-daban. Akwai marubutan labaran hikaya, akwai marubutan tarihi, akwai marubutan faɗakarwa, akwai kuma na ilimi. Sufyanu Adamu Yakubu mai laƙabi da Farfesan Marubuta, marubucin kalmomin hikima ne da faɗakarwa, musamman abin da ya shafi zamantakewa da tarbiyya. Kasancewarsa malamin makaranta, hakan ya taimaka masa wajen yin rubuce-rubuce da suka shafi ilimi da cigaban rayuwa. A zantawarsa da Abba Abubakar Yakubu, Farfesan ya bayyana burinsa na zama cikakken Farfesa na gaske, kuma mawallafin littattafan kimiyya. A yi karatu lafiya.

MANHAJA: Zan so ka fara gabatar mana da kanka. Wane ne Farfesa Sufyan?

FARFESA SUFYAN: Asalin sunan dai shi ne, Safiyanu Adamu Yakubu. Sai dai kamar yadda ka faɗa ana kirana da Farfesa Sufyan. Amma a kafafen sada zumunta an fi sanina da Sufyan Adams Yaqub (Angon Bultuwa).

Wacce ce kuma Bultuwa?

Bultuwa ƙirƙirarren suna ne. Na ƙirƙiro shi ne tun kafin na fara soyayya da wacce yanzu na yi wa laƙabi da sunan. Lokacin da na fara rubuce-rubuce akan soyayya, sai na ga buƙatar in qara wa rubutun armashi, shi ne sai kawai na alaƙanta rubutun da sunan Bultuwa.
Babban manufar ƙirƙirar sunan shi ne, sanya nishaɗi kan fuskar mai karanta saƙonnin soyayyar da nake rubutawa. Kuma hakan ya taimaka sosai wajen ɗaukar hankalin masu bibiyar rubutuna.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarka.

An haife ni a Unguwar ɗanburam, da ke ƙaramar Hukumar Wase, a Jihar Filato. Ni ne ɗa na biyu ga mahaifana, bayan Nura, sai ni, sai kuma Salima. Sunan mahaifina, Malam Adamu Yakubu. Mahaifiyata kuma ana ce mata Rabi’atu Muhammad. Na yi karatuna na firamare makarantar Pilot Central Primary School Wase, wanda yanzu ake kiranta da “Model”, daga 2001 zuwa 2007. Bayan nan na wuce Wase Community Secondary School (WCDSS) wacce tafi shahara da UBE, daga 2007 zuwa 2013. Sannan na yi gwagwarmayar rubuta jarrabawar neman shiga jami’a wato JAMB, amma ban samu nasara ba sai a 2018, inda na samu gurbin karatu a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Yanzu haka ina shekara ta 4 wato 400 Level.

Na tava karatun addini kaɗan, ina kuma da haddar Alƙur’ani mai girma. Na sauke wasu ƙananan littattafan addini kamar irin su, ‘Ta’alimul Mutaɗallib Ɗariƙatu Ta’alim’, ‘Ahdari’, ‘Ƙawa’idi’, ‘Muƙarrarut Tauhidi’, ‘Arba’una Hadith’, da sauransu.

Ni malamin makaranta ne, ina koyar da darussan kimiyya da lissafi a makarantar sakandire, sannan kuma ina koyarwa Madarasatu Imamu Malik Bn Anas. Ina kuma tava wasu harkoki na kasuwanci.

Wanne abu ne ya faru da kai tun kana ƙarami zuwa yanzu, wanda za ka iya cewa shi ne ya inganta tunaninka har rayuwarka ta zama haka?

Ingantuwar tunani shine silar ingantuwar rayuwata. Abinda ya faru, har ya yi sanadiyyar inganta tunanina, babu sama da gorin karatu da mahaifin wata ɗaliba da nake koyarwa ya tava min, sakamakon ladabtar da ƴar sa a makaranta, sai yake ce min, “Yaushe ka yi ilimin da har za ka fara koyarwa?” Wannan kalmar ta yi matuƙar tasiri wurin angiza tunanina kan duƙufa karatu.

Ba mu labarin yadda ka fara sanin cewa kana son zama marubuci?

Tun lokacin da na fara karance-karance, na ji ina son na fara rubuce-rubuce. Na fara karanta littattafai, karatunsa kai tun 2011, a lokacin a Facebook kawai nake karatu. Na karanta littattafai sama da 40 a Facebook. Sannan daga bisani na koma kan ainihin littattafai na takardu, kuma tun daga wancan lokacin, na ji ina son in zama marubuci.

Waye ya fara nuna maka yadda ya dace ka yi rubutu?

Mai muqamai uku gare ni. Surukata, malamata, kuma Antina. Wato Sanah Sulaiman Matazu (Oum Beenah). Ita ce take nutsar da ni yadda zan yi rubutu. Kuma har yanzu bata daina gyara min kura-kuraina ba.

Waɗanne irin rubuce-rubuce ka ke yi, hikayoyi ne ko faɗakarwa?

E, dukka ina yi. Kodayake na fi yin rubuce-rubucen faɗakarwa, amma kuma ina tava na hikayoyi, masu ɗauke sa darussa na faɗakarwa.

Shin kana rubuta littattafai ne ko a ina ka ke fitar da rubutunka?

Ba na rubuta littattafai. Ina yin gajerun rubuce-rubuce ne na faɗakarwa a kafafen sada zumunta.

Ba mu labarin yadda ka ƙirƙiro da basirar zauren Fitilar Makaho, kuma me hakan ke nufi?

Na ƙirƙiro da Fitilar Makaho ne a ranar 14-2-2021. A karance karancen da nake yi na karanta wannan labarin wani makaho da aka taɓa yi a wani zamani da ya gabata, cikin wani ƙaramin ƙauye. A kowanne dare in wannan makaho zai fita yawonsa, sai ɗauki wata fitila mai haske ya riƙa a hannu, ya fita da ita.

Rannan da daddare, akan hanyarsa ta dawowa gida, bayan ya kammala cin abincin dare a waje, sai ya biyo ta inda wasu matasan matafiya suke zama. Lokacin da waɗannan matafiya suka ganshi, sai suka fara tofa albarkacin bakinsu akansa, suna masa dariya, suna barkwanci ga wannan dattijo.

Sai ɗaya daga cikinsu ya ce wa dattijon nan, ‘Kai makaho ne, ba ka ganin komai, amma duk da haka ka ke yawo da fitila?”

Dattijon ya ce, “E! Tabbas ni makaho ne, kuma ba na ganin komai, amma ina yawo da fitila ne saboda irin ku masu gani, a cikin duhu baza ku iya ganin makaho ba, sanadin haka sai ku je ku ture ni.”

Wannan ya sa dukkan matasan suka ji kunya, suka nemi dattijon ya musu afuwa akan dabi’unsu.

Wannan labarin ne ya ingiza ni, na ƙirƙiro da shafin Fitilar Makaho, a matsayin wani dandali da ake amfani da hasken ilimin don haskaka wa wanda ba shi da shi, ko da ba za ka samu wani tagomashi ba.

Menene ra’ayinka game da yadda matasa suke nisantar karatu da rubuce-rubuce irin wanda ka ke yi?

Babbar asara ce mutane suke tafkawa. Duk da mafi akasarin mutane suna da lalacin karatu, musamman wanda zai ilmantar, ya faɗakar kuma ya wa’azantar. Amma tabbas ba ƙaramin asara ba ne, kaucewa rubuce-rubucen faɗakarwa, da za su amfani rayuwar mutane duniya da lahira.

Ta yaya marubuta za su yi amfani da alqalaminsu wajen kawo sauyi a cikin al’umma?

Akwai hanyoyin yadda marubuta za su bi wurin kawo sauyi a cikin al’umma, musamman a wannan zamani da dukkan al’umma, ta mayar hankali zuwa ga shafukan sada zumunta. Marubuta za su iya karkatar da hankalin su wajen isar da saƙonninsu ta hanyar taƙaita yawan rubutun da za su yi domin al’umma ta ƙaru. Saboda mutane yanzu ba su da juriyar karanta dogon rubutu, malalata matuƙa a fannin karatu.

Sannan yanzu akasari mutane sun fi mayar da hankali sauraron sauti, maimakon karantu saboda lalaci. Don haka yana da kyau marubuta su ƙirƙiro da hanyar mayar da rubuce-rubucensu kan sauti, musamman a manhajar YouTube, amma duk da haka a gajarta.

Yana da kyau marubuta su yawaita rubuce-rubuce akan abinda ake ganiyar cin kasuwarsa, ba wanda ya shuɗe ba. A yi rubutu akan abubuwan da za su taimaka wajen samar da mafita, ko masalaha ga matsalolin da ke damun rayuwar ɗan’adam. A kuma kaucewa rubuta labaran batsa, shaci-faɗi da sauran rubuce-rubucen assha.

Shin kana cikin wata ƙungiya ta marubuta ne, kuma yaya zamanka a ƙungiyar ke taimaka maka a rubuce-rubucen da ka ke yi?

Ina cikin ƙungiyoyi daban-daban irin su Arewa Media Writers, da kuma ƙungiyar marubuta ta Jos Writers Club. Wannan ƙungiya tana taimaka min wajen kaifafa ƙwaƙwalwata matuƙa. Tana kuma ƙara min qwarin gwiwa a game da rubuce-rubucen da nake yi.

Wanene madubinka a cikin marubuta, wanda ka ke ganin salonsa na burgeka?

Marigayi Alhaji Bashir Othman Tofa, mawallafin littafin, ‘Tunaninka Kamanninka’.

Su wane ne abokan hulɗarka a cikin marubuta, kuma yaya zumuncin marubuta yake?

Babu shakka ina abokan zumunci da dama a cikin marubuta, amma waɗanda na fi kusanci da su sosai su ne Sanah Sulaiman Ismail Matazu, Malam Abba Abubakar Yakubu, Ayuba Muhammad ɗanzaki, da kuma Muttaqa A. Hassan.

Gaskiya zumuncin marubuta ba shi da tamka. Har yau ban ga masu zumunci cikin girmama juna kamar su ba.

Ka taɓa shiga wata gasa ta marubuta, wanne sakamako ka samu a gasar?

Sau biyu na tava shiga gasa. Na shiga gasar gajerun labarai ta ƙungiyar Kainuwa Authors Forum! Kasantuwar wannan ne karo na farko, ban yi nasara ba, sai dai na samu takardar karramawa daga ƙungiyar. Sannan sai kuma gasar rubutun insha’i da ƙungiyata ta Arewa Media Writers reshen Jihar Filato ta shirya, a wannan karon na yi nasarar zuwa na 2.

Menene burinka nan gaba a matsayinka na marubuci?

Ina da burin rubuta littattafai masu yawa, musamman kuma ina son in yi rubutu kan ilimin ma’adinan ƙasa wato Geology da harshen Hausa, domin faɗakar da jama’a.

Wacce nasiha za ka yi wa ƴan’uwanka matasa game da neman ilimi da sana’a?

Nasiha ta ga ƴan’uwa matasa, kan neman ilimi da sana’a. Ina kira ga matasa a matsayin ku na ƙashin bayan al’ummar nan, dukkan abinda ku ka bayar shi ake amsa, idan ba ku da ilimi, kenan jahilci za ku bayar, kuma shi za a karva, kuma shi za a gani. Idan ba ku da sana’a, ƙarshe ci ma zaunen al’umma za ku haifar. Ku taimaki ƙarni mai zuwa, ku ƙawata kawunan ku da ilimi da sana’a.

Wanne lokaci ka fi samun natsuwar yin rubutu ko karatu?

Nakan samu natsuwar yin rubutu ne a yayin da na samu maudu’in da ke tashe, nakan yi rubutu da safe ko bayan sallar Azahar. Nakan samu natsuwar yin karatu a yayin da aka titsiye ni, ko in ce nake binciken wani abinda aka tambaye ni. Na fi samun natsuwar karatu bayan kowa ya yi barci cikin dare da bayan sallar Asuba.

Wanne abu ne ranka yake so a rayuwa, amma har yau ba ka cimma nasara a kansa ba?

Ina son na samu ilimi mai zurfi na addini, da na boko. Har na kai matakin zama farfesa, kamar yadda ake min laqabi. Gaskiya ina matuqar son in yi ilimi sosai. Shi ne abinda har yau na kasa cimmawa, amma ina hanya.

Wanne ƙudiri ka ke da shi na ganin ka cimma nasara kan duk wani ƙalubale da ke fuskantar rayuwarka?

Duk wani ƙalubale, na buqatar jajircewa, juriya, addu’a da kuma haƙuri kafin a cimmasa. To, waɗannan su ne abubuwan da nake ƙudirtawa akan dukkan abinda nake son cimma.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Ɗan hakin da ka raina, shi ke tsole maka ido.

Na gode.

Masha Allah. Ina godiya matuƙa.