Majalisar Dokokin Kano ta amince da naɗin Lawan Badamasi matsayin Kwamishinan KANSIEC

Daga RABIU SANUSI

Kwamitin tantance abinda ya shafi harkokin zaɓe a Majalisar Dokokin Jihar Kano ƙarƙashi shugabancin Rt. Hon Jibrin Falgore, ta kammala tantace Alhaji Lawan Badamasi, wanda aka ambata a mastayin sabon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano ta miƙa dukkan bayanai ga zauren majalisar don dubawa.

Majalisar ta bayyana hakan ne a lokacin da take zamanta, a yayin da shugaban kwamitin, Hon Murtala Muhammad Kadage mai wakiltar Garko ya ce, wanda aka wanda naɗin ya shafa ya cancanta da matsayin kwamishinan zaɓen na jiha.

Injiniya Murtala Kadage ya kuma ce, cancantar Badamasin yana dai-dai da abin da kundin tsarin mulkin majalisar dokokin da aka samar sashe na 4(a) da kuma (b) na Dokar zaɓen 2001, da ta ce “wanda ake tantancewar ya cancanta a amince masa a matsayin da ake buƙatar ya kasance na wannan ofishin hukumar zaɓen jihar Kano.”

Haka zalika, dukkan sauran ‘yan Majalisar sun goyi baya tare da nuna amincewar tabbatar da shi kamar yadda Hon Kadagen ya bada bayanai a kan aikin da kwamitin ya gabatar wa majalisar.

A nasa ɓangaren, shugaban Majalisar, Rt. Hon Jibrin Isma’il Falgore, ya yaba da aikin da kwamitin zaɓen na majalisar dokokin ya yi.

Sannan Falgore ya tabbatar da cewa buƙatar tantace Badamasi a matsayin Kwamishinan Zaɓen na ƙunshe ne a wata takarda da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike wa Majalisar a ranar 25/03/2024, inda ya buƙaci majalisar ta duba yiwuwar canza Garba Ibrahim Tsanyawa da yake cikin tawagar ma’aikatan na KANSIEC.