Gwamnan Kano ya isa Amurka don halartar taron zaman lafiya

Daga RABIU SANUSI

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya isa ƙasar Amurka domin halartar babban taron tattaunawa da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya a ranar Talatar da ta gabata

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar da Darakta-Janar mai kula da harkokin yaɗa labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu.

Bature ya ce, taron na kwanaki uku da gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Plateau ke halarta, an shirya shi ne domin magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya da kuma mafi kyawun zaɓi na daƙile ƙalubalen.

“Haɗin kai mai zurfi zai baiwa Gwamnonin wasu jihohin da ke fama da rikici zurfafa fahimtar yanayin barazanar tsaro, yanayin tattalin arziki, da kuma damar da za a yi kusa da shi don samar da kwanciyar hankali a Arewacin Nijeriya.”

“Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka kuma za ta faɗaɗa ilimi kan ƙarfafa riga-kafin rikice-rikice a yankin, ta hanyoyin da ba na tashin hankali ba na shigar da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a matsayin madadin warware duk wata matsalar tsaro.

Sanarwar ta ce, shirin dabarun da aka ƙulla a ƙarƙashin kulawar Dokta Joseph Sany, mataimakin shugaban Cibiyar Aminci ta Afirka ta Amurka, zai kuma mai da hankali kan daidaita manufofi da gudanar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

Taron wanda zai ƙare a ranar 25 ga Afrilu, 2024, na daga cikin ƙoƙarin Gwamnonin Arewa musamman na Arewa maso Yamma na tsara manufofin cigaban yankunan ta fusakar zaman lafiya.