Ta’addanci na haifar da illa musamman ga mata — Amina Mohammed

Daga WAKILINMU

Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta jaddada muhimmancin magance matsalolin ta’addanci da tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa a faɗin Afirka.

Mataimakiyar ta bayyana haka ne a yayin da aka yi wani taro na yaƙi da ta’addanci da aka gudanar a ranar Litinin a Birnin Tarayya Abuja.

Ofishin Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA) tare da hadin gwiwar ofishin yaƙi da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya UNOCT ne suka shirya. Taron ya aka yi wa taken ‘Karfafa Hadin Gwiwar Yanki Da Ci Gaban Cibiyoyi Don Tinkarar Barazanar Ta’addanci a Afirka’.

Amina ta qara jaddada illar ta’addanci da munanan illolin da yake haifarwa ga al’umma, musamman mata da ‘yan mata wadanda galibi su ne irin ke fuskantar cin zarafi A wannan ta’addanci.

Bugu da ƙari, ta yaba wa Nijeriya bisa kiran taron ƙolin don magance matsalolin mata, masu rauni, da waɗanda ta’addanci ya shafa.

“Dole ne mu samar da ingantattun dabaru da za su magance waɗannan ƙalubale, tare da mai da hankali kan halin da mata da ‘yan mata ke ciki waɗanda rashin tsaro ya shafa,” in ji ta.

Da take bayyana muhimmancin saka hannun jari ga matasa, Amina ta buƙaci kasashen Afirka da su samar da yanayi mai kyau don ci gabansu da wadata.

Ta ƙara da cewa muhimmancin taron ya wuce Nijeriya, inda ta yi kira da a yi ƙoƙarin haɗin gwiwa daga ƙasashen Afirka a fadin nahiyar, ciki har da Ghana da Togo, domin samun ci gaba mai ma’ana wajen yaƙar ta’addanci da kuma tallafa wa al’ummar da abin ya shafa.

A halin da ake ciki, mataimakiyar babban sakataren ta bayyana takaicinta da damuwa game da yadda ake yin watsi da al’amuran mata da ‘yan mata a manyan tarurrukan duniya.

“A manyan tarukan da shugabannin ƙasashen duniya ke tattaunawa, an mayar da hankali ne bisa ƙarfafa gwiwar matasa da matakan yaƙi da ta’addanci, tare da kawar da matsalolin da suka shafi mata.

“Sai dai a yanzu, abin farin ciki ne ganin yadda al’amuran mata ke samun karɓuwa a irin waɗannan dandali,” in ji ta.