Hankalina na tashi idan na ga wanda baya da abin ci da iyalinsa – Aunty Sadiya Kaduna

“Burina in ga maraya cikin farin ciki kamar kowa”

Daga AISHA ASAS

Hajiya Sadiya Abdullahi wadda mutane da yawa suka fi sani da Antin KD, kuma wadda ta kasance ‘yar gwagwarmaya da fafutikar ganin marayu da gajiyayyu sun ɗanɗana irin daɗin da masu iyaye da masu hali suke ji a rayuwarsu, ta fuskar tallafa masu da abinci, suturu, da kuma ƙoƙarin inganta lafiyarsu ta hanyar gidauniyar ta. A cikin tattaunawar ta da jaridar Blueprint Manhaja za ku ji wacce ce ita, gwagwarmayar ta da kuma sirrin shaharar ta.

MANHAJA: Bari mu fara da jin taƙaitaccen tarihinki.

SADIYA KADUNA: Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Sadiya Muhammad Abdullahi Tsoho Kudan, wacce aka fi sani da Aunty Sadiya Kaduna, wato Antin KD. Ni haifaffiyar garin kaduna ce a Unguwar Tudun Wada.

Na yi Firamare ɗina a nan Tudun Wada Bantis, ban ƙarasa a nan ba aka mayar da ni Chawai da ke Unguwar Sunusi, a nan na yi aji uku zuwa shida. Daga nan da na gama sai na shiga Sakandare ta Maimuna Gwarzo, har na kai SSS 1 aka yi min aure. Saboda haka ko da na je ɗakin mijina ban bar karatun ba, sai na shiga makarantar Salamatu Institute nan na kammala Sakandare ɗina tare da difiloma a ɓangaren koyon harshen Larabci, sannan kuma na je kwalejin horas da malamai ta ƙasa a nan Kaduna NTI. Alhadulillahi ina da aure da yara bakwai yanzu haka.

Ke ce shugabar gidauniyar Ummaty Foundation. Menene takamaiman ayyukan gidauniyar?

E ni ce CEO ta gidauniyar Ummaty Foundation, na ƙirƙiri gidauniyar ce don tallafawa ƙananun yara da mata da gajiyayyu, gidauniya ce wacce ta daɗe wajen shige da fice don ganin ta maida hankali wajen tallafawa mabuƙata musamman marasa lafiya da ƙananun yara waɗanda iyayensu suke da rauni wajen samar masu da abubuwan more rayuwa tare da tarbiyyarsu, haɗi da faɗi-tashi wajen nema wa marayu mafita ta wajen ganin su ma sun ci sun sha sun ƙoshi kamar yadda sauran yara masu iyaye ko masu gata ke kwanciya ba tare da kishirwa ko yunwa ba a cikin su.

Waɗanne irin nasarori ki ka cimma musamman ta hanyar wannan gwagwarmaya da ki ke yi?

Nasarori gaskiya alhamdu lillahi zan ce ina samu, tun da duk abin da na sa gaba Allah yana cika min burina, sai ki ga na samu yadda zan yi cikin sauƙi ba tare da wata tirjiya ba. Sannan kuma babban abun farin ciki na shi ne yadda wannan gidauniya ta soma aikace-aikacen ta, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sai ga shi tana tallafawa gajiyayyu da marasa lafiya masu yawa, wanda ban yi tunanin gidauniyar za ta iya ɗawainiya da mutane masu yawa kamar yadda muke yi yanzu ba, a cikin ƙanƙanin lokacin nan. To gaskiya babu abin da zan ce sai godiya ga Allah.

To wane ƙalubale ki ke fuskanta?

Ƙalubale kam akwai su da yawa, amma ina ɗaukar su a matsayin jarrabawar rayuwa, saboda shi ɗan adam dama Allah ya halicce shi ne cike da ƙalubale, Allah zai iya jarrabtar sa da ƙaddara mai kyau ko maras kyau, kin ga wannan ma babban ƙalubale ne a rayuwa. Saboda haka ni ina ganin duk wani ƙalubale da na fuskanta ko zan fuskanta ba wani abu ba ne, dama haka Allah ya tsara.

Shin wannan gidauniyar ta ki tana samun tallafi daga gwamnati ne?

A’a ba ta samu gaskiya, in ma mun nema ba ma samu, sannan kuma waɗanda za su yi mana hanya ko mun masu magana sai su ce ana bin layi ne. To muna ta dai iya bakin ƙoƙarin mu na ganin mun samun tallafi ta wurare mabambanta, wanda muke faɗi-tashi a tsakanin mu masu kishin gidauniyar da kuma tausayin marayu da gajiyayyu, haka muke harhaxa ɗan abin da muke da shi don taimaka masu.

Zuwa yanzu mutane nawa ne ke amfana da wannan gidauniyar?

Bazan iya cewa ga adadi ba, sai dai muna iya bakin ƙoƙarin mu na ganin mun tallafawa waɗanda suka iso gare mu da waɗanda muka je muka gansu da idanunmu daidai gwargwadon abin da za mu iya. Ba ma cikawa saboda yanayin ƙarfin mu. Wani sai mun je wajen masu hali waɗanda muka san suna da kishin taimakawa mu yi ‘Allazi Wahidi’ abin da muka samu sai mu ba wanda muka ga yana da matuqar buƙatuwa musamman ta rashin lafiya da abin da za a ci.

Shin wannan gidauniyar ta Ummaty Foundation tana shirya taron wayar da kai ga mata kan waɗansu matsaloli?

Mun tava shiryawa sosai kuwa musamman wajen wayar wa da mata kai da iyayen mu na ganin sun jawo yaran su a jiki, suna tambayar su matsalolin su da ba su shawarwari ta yadda za su zama wayayyu wajen gujewa lalatattun mazan da ke ƙoƙarin yi musu wayo ko su kai ga yi musu fyaɗe da sauransu. Sannan kuma su kansu iyayen yaran mukan tara su mu dinga jawo hankalin su a kan kar ki zama bagidajiya a gidanki, ki dinga tuntuvar yaranki akan duk wani sirrin da zai zama yaran suna ɓoyewa akan kar ki bari ta bar komai a zuciyarta, ta faɗa miki komai kaitsaye, wannan yana samuwa ne ga iyayen da suka jawo yaransu a jiki.

Kun tava koyar da mata sana’ar hannu, ko tallafa masu da jari?

E, mun taɓa koya masu sana’o’in hannu kamar irin koyon sabulu, turaruka da sauransu. Amma gaskiya ba mu da ƙarfin da za mu tallafa masu in mun koya masu, akwai dai wanda ya taɓa mana alƙawarin mu koya masu in mun gama zai tallafa, daga baya mun bi shi har mun gaji amma bai tallafa ɗin ba.

Me ya ba ki sha’awar buɗe wannan gidauniyar?

Wallahi ba komai ba ne face tausayi. Allah ya sani ina tausaya wa wanda na ga ya shiga wani hali na damuwa, kin ga in ga mutum ba shi da halin ciyar da iyalinsa wannan abin na tayar min hankali. Gara ma makaranta gwamnati na ɗauke wa al’umma, akwai ta kyauta za a baka littafi da kayan sawa kyauta, to kin ga fannin ilimi komai talaucin ka yaron ka zai je ya yi karatu, to amma fa sai ciki ya cika ake iya gudanar da sauran abubuwa. To gaskiya ba na so in ga mutum cikin halin yunwa sannan uwa uba rashin lafiya, ga shi ba yadda za ka yi tun ba ma in ciwon babba ne ba wanda sai an nemi tallafin jama’a.

Menene burinki a yanzu?

Burina shi ne in ga na gama da duniya lafiya, na gama da iyayena kuma lafiya, ina kuma da burin in ga na faranta ran mahaifana. Sannan kuma in ga maraya cikin farin ciki da jin daɗi kamar kowa. To hakan yana birge ni a rayuwata.

Mutane na cewa kin iya ado, menene sirrin?

Ai mace da ado aka san ta, mace ‘yar kwalliya kuma ‘yar ƙwalisa ce mai son ƙyalƙyali, komai tsufan ta sai dai in ta zama kucaka, to wannan ita ta rako mata duniya. Amma ni gaskiya ko a cikin gida na bana son qƙazanta, ba na son in ga wuri kaca-kaca da datti, sai in ji tsigar jiki na na tashi.

Ƙasashe nawa ki ka taɓa ziyarta a duniya?

Na ɗan leƙa ƙasashe kamar su London, Dubai, Saudiyya, Cotonou, Cameroon da dai sauransu.

Me ya fi birge ki?

Abin da ya fi burge ni a rayuwata shi ne in waiga in ga ko’ina ina da masoya, haƙiƙa wannan abin yana birge ni, ina son masoya na sosai suna saka ni farin ciki a rayuwata.

Me ki ka fi tsana a rayuwarki?

Na tsani rainin hankali da butulci da ganin ƙyashi, tare da girman kai. Sannan kuma ba na son gulma da annamimanci, shi ya sa na tsani mai duk wannan ɗabi’un.

Abincin da ki ka fi so?

Ina son ɗanwake da dambun shinkafa.

Wacce shawara za ki ba mata ‘yan uwanki musamman masu tasowa da shawarar taimakawa wasu?

Shawara ta ga masu tasowa ko yanzu ko nan gaba ga wanda ke sha’awar ya buɗe gidauniyar tallafawa mabuƙata shi ne sai ya haɗa da haƙuri tare da juriya da jajircewa da kuma kawar da kai, in dai har tana so ta yi ɗin domin Allah, to za ta yi ta haɗuwa da ƙalubale iri-iri, amma in dai ta yi haƙuri ta daure tun da abin sa kai ne sai a dace da abin da ake burin samu. Abun akwai wahala sosai akwai tashin hankali cikin sa, musamman za ki haɗu da masu buƙata cikin mawuyacin hali, hankalin ki zai tashi ki haɗu da masu ciwo kala-kala, wani ciwon ma in ya tsaya maki a rai ko barcin kirki ba ki iya yi. Saboda haka sai an jure sosai.

Sunanki ya yi tambari sosai, ko’ina aka shiga za a ji zancen Antin KD. Shin kin tava siyasa ne?

Ba na siyasa amma na ɗan taɓa ɓaɓatu a soshiyal midiya wani zaure na ‘yan siyasa. Sannan kuma shi kansa sunan mutane suka saka min shi wanda har ya zo yana neman ya danne sunana, ya zama kusan kowa a yanzu da haka suke kira na.

To menene sirrin wannan shahara?

Ni kaina ban san menene sirrin shahara ta ba, a hakan an sha min wannan tambayar ni kuma ganin ban san amsar ba na taɓa tambayar Nasir G Ahmad na ce ana tambaya ta mene ne sirrin shahara ta sai ya ce ke ba ki sani ba? Na ce ai in ka juya baya ba ka iya ganin menene a bayan ka sai dai wani ya gani. Ya ce to ki riƙe wannan, sirrin shaharar ki son mutane da kuma nuna kowa na ki ne da haba-haba da mutane. Na ce masa au haka ne? Ya ce ƙwarai kuwa, to ban sani ba gaskiya sai dai waɗanda suke tare da ni su ne za su bada amsar shahara ta.

To mun gode ƙwarai da gaske.

Ni ma na gode.