Zan yi murabus muddin ba a hukunta Yahaya Bello ba — Shugaban EFCC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya lashi takobin bin diddigin zargin almundahanar Naira biliyan 80.2 da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, State Yahaya Bello har zuwa ƙarshe.

Olukoyede ya furta haka ne a hirar da ya yi da manema labarai a Babban Ofishin hukumar da ke Abuja, inda ya ce babu makwa zai yi murabus muddin ba a hukunta Bello ba.

“Idan ni da kaina ban ga ƙarshen wannan binciken game da Yahaya Bello ba, zan a jiyen’ muƙamina a matsayin Shugaban EFCC Chairman,” in ji Olukoyede.

Ya ce Bello ya ciri kuɗaɗe har $720,000 daga asusun gwamnati don biyan kuɗin makarantar ɗansa.

Kazalika, Olukoyede ya sha alwashin hukunta dukkanin waɗanda suka yi babakere wajen hana kama tsohon gwamnan.