Yadda rabuwar aure ke kawo damuwa ga iyalai

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Zaurukan sada zumunta sun ɗauki hankali a makon da ya gabata, sakamakon wasu maganganu da fitaccen jarumin Kannywood kuma mawaƙi Adam A. Zango ya yi a wani ƙaramin bidiyo da ya ɗora a shafinsa, a matsayin martani ga masu yaɗa maganganu marasa daɗi a kansa. Tun bayan da jarumin finafinan Hausan ya sanar da rabuwa da matarsa ta baya-bayan nan surutai suke yawa a kansa, ana zarginsa da rashin iya riƙon aure, ko kuma auri-saki, kasancewar duk matan da ya aura ba sa jimawa tare da shi ake rabuwa, bisa wasu dalilai daban-daban.

Ɓacin ran da yake fuskanta na irin maganganu marasa daɗi da zarge-zarge marasa tushe, ya sa shi mayar da martani ga wasu daga cikin batutuwan da yake ganin ba a yi masa adalci ba, ko ana kallon matsalar a baibai. Kamar yadda ya fafa a wani bidiyo na baya-bayan nan da ya sake yana mai bayyana cewa, maganganun da mutane ke yi a zaurukan sada zumunta kan ko yana fuskantar matsalar damuwa ko karayar zuciya ba gaskiya ba ne.

Lafiyarsa qalau, babu abin da ke damunsa, tura ce kawai ta kai bango! Yana ganin daga cikin waɗanda suka san gaskiyar abubuwan da suka faru, babu wanda ya fito ya kare mutuncinsa ko fayyace haƙiƙanin abubuwan da suka faru, don jama’a su daina vata masa suna, sun yi shiru ba sa cewa komai. Don haka ya ɗaukarwa kansa alhakin ya mayar da martani, domin waɗanda suka damu su san gaskiya su fahimci me ya sa ya yi abubuwan da ya aikata a baya, musamman game da rabuwa da matansa da ya yi.

Sai dai a wajen wasu daga cikin ’yan uwansa na Kannywood da masu nazarin rayuwar jaruman finafinai da mawaƙan Hausa suna ganin lallai biri ya so ya yi kama da mutum, dangane da zargin matsalar damuwa da Adam A. Zango ke fuskanta, saboda yadda suke ganin yana fitar da maganganun da za a iya cewa sirri ne na iyalinsa. Bai kamata ya bari ma wani ya san me ya faru ba, saboda kimarsa da ta ’ya’yansa masu tasowa.

Na karanta wasu rubuce-rubuce ko sharhi da bidiyo da wasu suka fitar game da batun waɗanda suke ƙoƙarin ba shi shawara ko kwantar masa da hankali, kan ƙalubalen rayuwa da yake fama da shi. Kowanne da yadda yake kallon matsalar, amma wanda ya fi ɗaukar hankalina shi ne na wata marubuciya kuma mai bai wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan tallafawa mabuƙata, Fauziyya D. Suleiman wacce ita ce ta fara jawo hankalin makusantan Adam A. Zango kan matsalar.

Surutai da jita-jita kan rayuwar jarumai ko fitattun mutane ba sabon abu ba ne, musamman a wannan lokaci na soshiyal midiya, inda ake samun sauri da sauqin yaɗa saƙonni na gaskiya da na ƙarya, don jan ra’ayin jama’a ko mabiya. Ko da kuwa masu yaɗa saƙonnin sun san ba gaskiya suke yaɗawa ba, amma don dai a ce su ne suka fara fitar da saƙon ko kuma a wajensu aka ji.

Ba ma kawai ga rayuwar Adam A. Zango kaɗai ba, dubban mutane ne a duniya ke fama da matsalolin da suka shafi damuwa da karayar zuciya, sakamakon wasu damuwoyi da suke fuskanta daga iyalansu, ko kuma bayan sun samu matsalar rabuwar aure. Mutum kan samu kansa a matsalar yawan ɓacin rai, fushi, fitar da rai daga gyaruwar al’amura ko yawan kaɗaici, da yawan zargin kansa kan wasu abubuwa da suka faru ko suke faruwa, sakamakon yadda yake ganin abubuwa na faruwa a kan idanunsa, amma babu yadda zai yi ya gyara. Ko kuma yadda rayuwar iyalinsa ke lalacewa saboda wasu kurakurai da ya aikata a baya, hakan zai riƙa sa ya riƙa jin ƙunci a ransa da takaicin sakacin da ya yi a rayuwa.

Kowa zai iya samun kansa a irin wannan yanayi, gwargwadon zurfin yadda mutum ya samu kansa a cikin wannan matsala, da ƙarfin ƙwaƙwalwarsa wajen iya jurewa matsala ko damuwa. Mujallar Holmes-Rahe Life Stress Inventory ta gudanar da wani bincike game da yadda rabuwar aure ke sa damuwa a rayuwar ma’aurata, inda ta gano cewa, ‘Rabuwa a tsakanin ma’aurata ita ce matsala ta uku da ke haifar da lalurar damuwa a zukatan ma’aurata.’

Masanin halayyar ɗan adam Malam Aliyu Alƙasim ya bayyana cewa, daga cikin halayen da za a gane mutum ya shiga cikin matsalar damuwa bayan rabuwarsa da matarsa ko mijinta sun haɗa da fitar da rai daga samun kwanciyar hankali, rashin walwala, yawan zubar da hawaye, rashin samun isasshen barci, yawan kwanciya, yawan jin kasala, rashin cin abinci, rashin sha’awar jima’i, da kuma ramewa.

Bincike ya nuna cewa, ma’auratan da suka rabu da juna za su iya fuskantar yawan tunani, yawan jin takaici, shaye-shaye, tunanin kashe kai, don tsira daga takaicin rayuwa, da sauran alamomi da ke nuna mutum na cikin tsananin damuwa.

Wasu na ganin daga maganganun da ake ji Adam A. Zango na furtawa, akwai alamomin da muka ambata a sama. Shi ya sa suke ganin lallai yana buƙatar taimakon makusantansa, abokansa, da na ƙwararru. Kodayake shi dai ya dage kan cewa, ƙalau yake, tura ce ta kai shi bango. Sai dai duk da haka, masana halayyar ɗan adam na ganin ba lallai ne shi ya fahimci haƙiƙanin halin da yake ciki ba. Amma yanayin sa da kalamansa sun nuna lallai akwai matsala.

Farfesa Aishatu Armaya’u, Darakta mai kula da Babban Asibitin Ƙwaƙwalwa na Ƙasa da ke Kaduna ta bayyana cewa, ta bayyana cewa kashi 23 cikin ɗari na mutanen da ke samun kansu cikin damuwa a dalilin matsaloli na rabuwar aure, suna kashe kansu ko aikata wani abu da zai cutar da rayuwarsu. Musamman ga mutanen da suke da tarihin yawan nuna damuwa ko tunani, don haka ƙalubalen rabuwar aure kan sa wasu shiga tsanani damuwa. Kodayake wasu na ganin matsalar Adam A. Zango na da matsala ne da koma-baya da yake fuskanta a harkokinsa na waƙa da finafinai. Suna ganin tauraronsa yana dusashewa shi ya sa yake jin ƙunci a zuciyarsa.

Wasu makusantansa irinsu Abdullahi Amdaz sun ƙaryata hasashen da mutane suke yi. Kan cewa halin da Adam A. Zango yake ciki ba shi da nasaba rabuwarsa da matarsa ko dusashewar tauraronsa a masana’antar Kannywood. Kodayake ba su fito sun bayyana gaskiyar abin da ke faruwa ba, wanda hakan ya bai wa wasu damar shaci-faɗi, kan abubuwan da suka faruwa.

Sai dai wasu na ganin yadda jama’a ke sharhi da faɗar maganganu na zargi da sukar halin da yake ciki, suna ƙara ta’azzara damuwar da yake fama da ita. Kamar yadda Farfesa Aishatu Armaya’u ta faɗa, idan ana ɗora laifin abubuwan da suka faru a kansa, zagi ko aibata shi zai ƙara harzuƙa shi, har ya sa shi cikin wata damuwa

Jama’a da dama dai na bayar da irin nasu shawarwarin game da yadda suke ganin ya kamata shi Adam A. Zango ya kula da kansa. Kamar ƙara kusantar ubangiji, lazimtar karatun Alƙur’ani Mai Girma, don ya samu natsuwar zuciya, da rage yawan tunani. Sannan ya tattaunawa da wani wanda ya yarda da shi, da kuma nisantar mayar da martani ko maganganu na ɓacin rai a kafafen sada zumunta.

Farfesa Aishatu Armaya’u, ta ba da shawara kan ya kamata masu irin wannan matsala su tuntuɓi ƙwararru da za su taimaka musu don su fita a wannan matsala, kuma su saki zuciyarsu, su fahimci cewa hakan ba shi ne ƙarshen rayuwa ba, akwai damar da za a gyara abubuwan da suka lalace a gaba, ko kuma a samu wani sauyi ma fi alheri da ya fi wanda ya gabata.

Wata shawara da ta ɗauki hankalina kuma ita wacce wata mai ba da shawara kan zamantakewar iyali, Hajiya Uwa Giɗaɗo Idris ta wallafa a shafinta na Facebook, inda take ba shi shawarar cewa, nan gaba idan har Adam A. Zango ya huce kuma yana so ya sake wani auren to, ya guji kallon kyakkyawar mace, ya nemi mai kyan hali. Kuma ya nemi wacce sonta ya fi wanda take masa yawa.

Mama Uwa, kamar yadda aka fi kiranta, ta buƙaci jarumin da in zai sake aure nan gaba, kada ya yi aure a gidan da sun fi shi wadata, ba waɗanda ke jira shi ya basu ba. Kuma ta ce, kada ya yi aure a qasa da watanni shida da haɗuwar sa da mace! Sai ya tabbatar da ingancin halayyar ta tukunna.

Waɗannan shawarwari ba na Adam A. Zango kaɗai ba, namu ne duka. Domin kamar yadda na yi bayani a sama, kowa zai iya fuskantar wannan matsalar, kuma zai so a bashi shawarwari masu tasiri irin waɗannan. Da fatan ubangiji Allah Ya bamu zuciya mai ƙarfin jure duk wata jarabawa da za ta fuskanto mu, a gida da waje.

Ya Allah Ka ƙara rufa mana asiri duniya da lahira.