Tarihin Daular Usmaniyya ba zai cika ba sai da Ummarunmu Alkammu – Sa’idu Mu’azu Alkammawa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka yi taro mafi girma a tarukan sada zumunta da ke gudana a Jihar Sakkwato, kasancewarsa taro mafi tara mutane da suka haɗa lungu da saƙo na jihar har ma da baƙi daga wasu jihohi. Dalilin kenan da duk girman ɗakin taron da aka ɗauka bai iya kwashe kashi biyu cikin ukun malaharta taron ba.

Ummarunmu Alkammu bai kasance mutumin da ke buƙatar doguwar gabatarwa ba musanmman ga masana tarihi, wanda za mu iya cewa, duk inda aka juya a tarihin Daular Usmaniyya to fa ya cancanci a ambaci sunan Ummarunmu Alkammu, dalilin kasancewarsa amini, abokin rayuwa, kuma na biyu da yiwa Usman Ɗanfodiyo mubaya’a, don haka za mu iya kiran sa da gwarzon jarumin da aka sha dare da rana tare da shi a ƙoƙarin jadadda kalmar Allah.

Wani abin ban mamaki game da shuxewar wannan bawan Allah shi ne, yadda marubutan tarihi ba su mayar da hankali kansa ba ko ba shi muhimmanci kamar yadda ya cancanta ba. Hakan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa da yawan mutane ba su san irin gudunmuwar da ya bayar a cigaban Musulunci ba.

Wannan ce ta sa wasu masu kishi daga zuri’ar gwarzon jarumin suka yi dogon nazari kan yadda za su samar da haxuwar kai tsakanin zuri’ar da kuma samar da tarihin tsatson nasu ko don ‘yan baya.

Da wannan ne suka miqe ba dare ba rana, suka shiga, suka fita, wurin ganin sun tattaro duk wani da ke da jinin Ummarunmu Alkammu a jikinsa. Kuma za mu iya cewa, zuwa yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu, domin sun tattaro gidaje masu dama ciki da wajen Sakkwato, wato bayan mazauna Sakkwaton, har da reshe a mutanen Jihar Bauchi, baya ga Ƙasar Sudan da aka samo wasu, kuma ake kan nema har kawo yanzu.

Taron wanda aka gudanar a ɗakin taro da ke cikin makarantar Sultan Maccixo Institutes for Ƙur’an and General Studies, ya soma da buɗe taro da addu’a daga bakin ɗan shahararren malamin nan marigayi Malam Muhammadu Bello Gyalgyal, malam Muhammadu Kadashi. Kafin karatun Al’ƙur’ani mai tsarki ya biyo baya, daga bakin ɗaya daga cikin ɗaliban makarantar Ummarunmu Alkammu da ke ƙarƙashin kulawar Magajin Rafi marigayi, kafin sabon Magajin Rafi ya gaji wannan nauyi na alkhairi da ya gada daga marigayi mahaifinshi Alhaji Bello Mai Wurno.

Jawabin maraba, wanda shugaban wannan tafiya, Alhaji Mu’azu Bello Mai Wurno, ya bayar ya fara da godiya ga Allah kan samun damar kaiwa ga wannan taron, da kuma gode wa mahalarta tun daga manyan baƙi zuwa sauran jama’ar da suka samu halarta bakiɗaya.

A cikin jawabin nasa, shugaban ƙungiyar, ya bayyana gagarumar nasarar da suka samu na asassa gidauniyar Ummarunmu Alkammu da ke da shalkwata a cikin faɗar Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Mu’azu ya ƙara da cewa, “Ina so in sheda maku cewa, wannan taro da aka soma irinsa na farko bai kasance abinda aka fara don a tsaya ba, don haka ƙalubale ne gare mu bakiɗaya.”

Daga ƙarshe ya miqa saƙon godiya ga dukka jagororin tafiyar kan irin shawarwari da suka bayar tare da gudunmuwarsu.

Kafin ya yi jinjina ga ‘yan uwa na Bauchi waxanda suka samu halartar taron duk da ta’azzarar matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya.

An gabatar da wa’azi kan sada zuminta daga bakin malam Muhammad, kafin ɗaliban makarantar Umurunmu Alkammu su gabatar da qasida ta makarantar da kuma Mai girma Magajin Rafi, wato uban makarantar tasu.

Tarihin Ummarunmu Alkammu ya fito ne daga bakin Sa’idu Mu’azu Alkammawa, inda ya gabatar da takardar da Magajin Rafi ya gabatar a baya.

A cikin jawabin nasa ya bayyana Ummarunmu Alkammu a matsayin wanda ya kasance mafi kusanci ga Shehu Ɗanfodiyo a abota, kuma ya bayar da bayanin yadda asalinsa na farko ya kasance Ƙasar Mali, da yadda zuri’arsa ta gauraya da ta Ɗanfodiyo ta hanyar auratayya, kafin ya bayyana manyan gidajen da zuri’ar tasa ta haifar, ciki kuwa har da wani vangare na zari’ar sarkin Musulmi wanda Mai Alfarma Sa’ad Abubakar ya fito daga ciki.

A nasa jawabin, Sarkin Fulanin Bauchi, Allhaji Ishaq Sambo, ya nuna jin daɗinsa na ganin ‘yan uwa, sannnan ya bayar da tarihin yadda ya kasance asalin Basakwacce, kuma zuri’ar Ummarunmu Alkammu, inda ya bayyana asalin nasa da “Salihu yayarsa ta auri sarkin Bauchi, sai aka haɗa ta da shi ta tafi, ya taso a can, kuma Sarkin Bauchi ya masa aure.” har ya kai ga zuri’ar wadda ya tabbatar suna da yawa yanzu haka.

Daga cikin waɗanda suka yi jawabi akwai, mai girma Magajin Rafi, Ɗan Malikin Achida, Sadaukin Sakkwato, wakilin Sarkin Musulmi da sauransu.

Taron ya tashi bayan an bayar da shawarar ƙarfafa gidauniyar Ummarunmu Alkammu Foundation don taimakon ‘yan uwa da ke cikin halin rayuwa, da kuma bayar da shawarar canza wurin taro a zama na gaba don ganin dukka mahalarta sun samu damar zama.

By Editor