NDE ta horas da matasa 50 dabarun noma da kiwo a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Hukumar Samar da Aikin yi ta Ƙasa, NDE, reshen Jihar Jigawa, ta zaɓo matasa maza da mata su 50 daga sassan jihar tare da ba su horo a kan harkar noman rani da kiwon dabobi da kiwon kaji da noman kifi da nufin inganta rayuwarsu.

Matasan da suka ci gajiyar shirin sun haɗa maza 20 da mata 30.

Shugaban NDE a jihar, Alhaji Sa’adu Iya Yarima, shi ne ya shaida wa manema labarai haka jim kaɗan bayan kammala bai wa matasan da lamarin ya shafa horo a cibiyar hukumar da ke Jigawa .

Yarima ya ce shirye-shirye ya yi nisa na ƙaddamar da cibiyar bai wa matasa horo mallakar Hukumar wadda ake sa ran za a buɗe nan ba da daɗewa ba.

Ya ƙara da cewa gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa shi ne ake sa ran zai ƙaddamar da sabon ofishin ya zuwa makon gobe.

Haka nan, ya ce waɗanda ake bai wa horon za su yi tsawon makonni biyu suna karɓar horo, da kuma waɗanda za su shafe makonni 10 ana koyar da su dabarun kiwon kaji domin su zama ƙwararru a ɓangaren kiwo da noma.

Daga nan, ya hori matasan su tsaya stayin daka wejan koyon aikin, kana ya gargaɗe su da su guji yin fashi ko zuwa a makare.

Ya ce Hukumar za ta bai wa waɗanda suka fi ƙwazo rancen tallafin kuɗi don assasa sana’arsu domin su zama masu dogaro da kai.