Da Ɗumi-ɗumi: EFCC ta tsare Hadi Sirika kan almundahanar N8bn

Daga BASHIR ISAH

Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC, ta tsare tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama, Hadi Siriki, sakamakon binciken da take gudanarwa kan badaƙalar karkatar da biliyan N8,069,176,864.00 na Kamfanin Nigeria Air.

Jaridar Punch ta rawaito tsohon Ministan ya isa ofishin EFCCda ke Abuja da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Talata, 23 ga Afrilun 2024.

Majiyarmu ta ce, bayan da ya isa ofishin na EFCC, an yi ea Sirika tambayo kan wasu kwangiloli da ake zargin ya bayar bisa ƙa’ida ba ga kamfanin Engirios Nigeria Limited mallakar wani ƙaninsa, Abubakar Sirika.

Majiya ta kusa da EFCC wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce, “Lallai Hadi Sirika ne ke tsare a ofishinmu na FCT. Yanzu haka yana ganawa da jami’an bincike na EFCC kan badaƙalar kwangilar N8,069,176,864.00 da ma’aikatar sufurin jirgin sama ta bayar” a wancan lokaci.

Ana binciken Sirika ne kan ayyukan da ma’aikatar da ya riƙe ta aiwatar wanda ake zargin an aikata ba daidai ba, kama daga haɗin baki zuwa karkatar da kuɗaɗe da sauransu.

Sirika shi ne Ministan Sufurin Jirgin Sama a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.