Bayan shekara 26, tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ya fice daga PDP

Daga BASHIR ISAH

Bayan shafe shekara 26 a matsayin mabiyin jam’iyyar PDP, tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar zuwa wata.

Ihedioha ya ce ya fice daga jam’iyyar ta PDP ne bisa ra’ayinsa.

A cewarsa, abin takaici ne ganin yadda PDP ta ɗare kan turbar da ta saɓa wa ra’ayinsa.

Ya ce, “Duk da ƙoƙarin da na yi na bai wa jam’iyyar shawarwari, jam’iyyar ta kasa samar da sauye-sauyen cigaba a cikin gida, tabbata ra da kiyaye dokokinta, ko kuma zama ‘yar hamayya mai ƙarfi ga jam’iyyar APC mai mulki.

“Bisa wannan dalili ne na rage ba ni da wani zaɓi face yin murabus daga Jamhuriyar PDP nan take,” in ji shi.

Ya bayyana haka ne cikin wasiƙar da ya aike wa shugaban PDP na Mazaɓar Mbutu Ward da ke yankin ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar.