Maza masu dukan mata

Tare da AMINA YUSUF ALI

Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu mai albarka, Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Yanzu za mu ci gaba a kan maudu’in da muka saba kawo muku wato nasiha kan zamantakewa, wato a wani maudu’inmu mai suna Maza masu dukan mata. Mun fara kawo muku wasu daga dalilan da suke jawo maza su yi duka, da muma dalilina na ganin bai kamata a ɗora musu laifi ba. Yanzu za mu ci gaba daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya.

To dalilin na biyu da nake ganin madoka mata ba su da laifi shi ne, ba mu mai da shi abin ƙyama a tsakanin al’umarmu ba. Misali, idan mutum yana dukan matarsa kuma kowa ya san hakan mutane sukan cigaba da mu’amala da shi ba tare da wariya gare shi ba. Za a gaisa da shi, wani ma ya ja Sallah a bi shi, a ci abinci da shi ba tare da an yi la’akari da cewa ya tashi daga sahun mutane ya shiga na dabbobi ba. Abin takaicin ma, idan ya sake neman wani auren za a iya ba shi dai a cikin wannan al’umma da yake rayuwa.

Musamman idan ya samu ɗiyar marasa galihu, balle a ce yana da abin hannunsa. Ai talakawan unguwa rububin aura masa yaransu suke yi don kwaɗayin abin Duniya. Sai an yi auren matsaloli sun taso a zo a yi ta maganganu, daga ƙarshe ya sako ta, kuma a sake ba shi wata ya aura! Kuma dukan dai ba zai fasa ba duk wacce ya aura. Sannan kuma ba za a samu wani ko wasu da za su yi masa nasiha ba. To meye laifinsa a nan? Wa zai ga wannan garaɓasa ya ƙyale? Idan an hana shi matar aure ina zai samu wacce zai aura ya yi wa duka?

Sannan dalilina na uku shi ne, iyayen matar su suke ba wa maza goyon baya ya doke ta. Da farko ma dai an aurar da ita ga namijin da ba a yi cikakken bincike a kan rayuwarsa da mu’amalarsa ba. Ko an yi bincike an gano yana duka, iyayen su ƙaryata. Idan yana da kuɗinma su ce ana musu baƙin ciki ‘yarsu za ta huta.

Idan kuma a unguwarsu ma yake, kuma kowa ya san halinsa, sai ka ga suna alaƙarta laifin da mata ko matansa da yake duka. Suna aibata su, suna nuna laifinsu ne ya sa ake dukan. Amma abinda yarinya da iyayenta suka manta shi ne, bulalar da ta doki uwargida, tana nan tana jiran amarya. Ita ma sai ya dake ta yadda ya daki sauran ko ma fiye da haka. Sai a yi hattara makwaɗaita.

Sannan abu na huɗu, rashin faɗa masa gaskiya daga dangi zuwa iyaye. Sai ka namiji madokin mata ne, amma kaf danginsa musamman idan yana da hali ba wanda zai tsawatar masa ko ya yi masa nasiha ya daina. Sai ma ka ji suna goyon bayansa a kan matansa ne ba su da hali. Ya ilahi, duk matan Duniya ba su da hali sai shi, madokin mata?

Wannan tsabar son zuciya ne. Su kansu ba za su so a yi wa ‘ya’yansu mata ba. Me ya sa kuma kake goyon bayan a yi wa ɗiyar wani? Wallahi da wani zai taimaka ko da da nasiha ne a samu ya daina, zai sami ɗimbin lada. Bugu da kari kuma kun ceto ɗanuwanku daga uqubar Ubangiji. Domin zaluntar mata ta hanyar duka ba koyarwar musulunci ba ce, kuma Allah ba zai bari ba.

Kuma sannan kada mu manta, akwai illoli da yawa tattare da dukan mace kamar, yi mata Lahani ko kisa, ɓata tarbiyyar yaran da kuka haifa, zubar da mutuncinka da nata a makwabta da iyayenta da sauran dangi, yaranta za su ƙullace ka kuma ba za su taɓa sonka ba, sannan watarana ma su rama ko su tsawatar maka. Ko su juya maka baya.

Da a ce al’ummarmu za ta gane, da ta ware masu wannan ɗabi’a wajen girmamawa, ko ba da wani shugabanci, ko zaɓensu a siyasa ko kuma a ba su auren ‘ya’yansu. Yin shiru da rashin ɗaukar matakai a kan abinda suke aikatawa yana sa wa su dinga ganin kamar Duniya ta ba su goyon bayan cigaba aiwatar da wannan mummunar ɗabi’ar tasu.

Sannan iyaye su daina tilasta wa yaransu mata da su koma su cigaba da zama da maza masu dukan mata. Domin shi aure ba dole a cikinsa idan da cutarwa musulunci ya yarda a raba. Gara ku karɓe ta a bazawara a kan matacciya. Domin dukan na iya halakar da ita.

Kai kuma madokin mata ka sani, Lusari ne kai wanda ba ya bin sunnar Annabi (SAW). Kuma dukan iyali yana rusa gida. Iyalinka su daina ganin mutuncinka. Watarana ma yaranka za su iya ƙalubalantar ka. Sannan yaranka maza za su ɗauki wannan ɗabi’ar su cigaba da aikatawa ga nasu matan.

Kuma sannan ka sani, duka ko ga ‘yayanka bai kamata ba, balle ga matarka da ka aura da amana don kana son ta, tana son ka. Duk girman laifin da za ta yi maka ba zai wuce ka yi mata faɗa ko nasiha ba, ku zauna ku fahimci juna.

Idan abu ya faskara, rabuwar aure fa halas ce. Sai a rabu ba tare da an ci mutuncin juna ba. Da fatan Allah ya yi mana jagora. A nan za mu dakata, mu haɗu a wani makon, idan Allah ya kai mu.