Yaƙi da Ta’addanci: Akwai buƙatar samar da dakarun yanki don daƙile safarar makamai — Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya jaddada kira kan samar da dakarun yanki masu zamn ko-ta-kwana a matsayin kayan aikin magance dukkan matsalolin tsaron da ake fuskanta a yanzu da ma waɗanda ka iya tasowa a gaba a yankin Afirka

Kazalika, ya ce samar da dakarun zai taimaka ainun wajen daƙile safarar makamai a tsakanin ƙasashen Afirka.

Tinubu ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen buɗe babban taron yaƙi da ta’addanci a Afirka wanda aka shirya ranar Litinin a Abuja.

Shugaban ya ƙara da cewa, ya zama wajibi a kawo ƙarshen ta’addanci a yankin Afirka duba da yadda matsalar ta zama babban ƙalubalen da ke hana manoma zuwa gona, yara zuwa makaranta da kuma mata ‘yan kasuwa zuwa harkokinsu wanda hakan ya jefa al’umma da gwamnati cikin mawuyacin hali.

Haka nan, ya ce, yaƙi da ta’addanci abu ne ya shafi kowa wanda sai an haɗa hannu sannan an tinkari magance matsalar daga tushe.

A nasa ɓangaren, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Kan Sha’anin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya vmce Nijeriya ta dawo da ci gaba da shari’ar ‘yan Boko Haram ɗin da ake tsare da su a Kainji.

Ribadu ya ƙara da cewa, Nijeriya na tattara bayanan sirri a kan ayyukan Boko Haram mayaƙan ISWAP da zummar dakushe ƙungiyoyin ‘yan ta’addar.

Mahalarta taron sun haɗa da, Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, Nana Akufo-Addo da Shugaban Togo, Faure Gnassingbé da sauransu.