Gwamnatin Tinubu za ta haramta wa ɗalibai ‘yan ƙasa da shekara 18 neman gurbin karatu a manyan makarantu

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta ce tana shirin haramta wa ɗalibai ‘yan ƙasa da shekara 18 nan gurbin karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu da ke faɗin Nijeriya.

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske a lokacin da yake zagayen duba yadda jarrabawar UTME ta 2024 ke gudana a wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar ranar Litinin a Abuja.

Ministan ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa ƙarancin shekarun wasu daga cikin ɗaliban da ya gani suna rubuta jarrabawar, yana mai cewa shekarunsa ba su kai na shiga jami’a ba.

A cewar Mamman, “Daga cikin abin da muka lura da shi, shi ne yawan shekarun masu neman gurbin karatu a jami’a. Wasun shekarunsu ƙanana ne.

“Za mu duba wannan batu, saboda sun yi ƙananan da za su fahimci abin da ilimin jami’a ya ƙunsa.”

Ya ƙara da cewa, bai ɗalibai masu ƙaranci shekaru gurbin karatu a jami’o’i da akan yi hakan na daga cikin dalilan da ke haifar da matsalolin da jami’o’i ke fuskanta a yau.

Daga nan, Ministan ya yaba da tsarin da aka bi wajen gudanar da jarrabawar wanda a cewarsa, tsarin ba ya tattare da wata wahala.