Gwamna Lawal ya jaddada buƙatar amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da rashin tsaro

Daga NASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada buƙatar da ke akwai ta amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da rashin tsaro a Jihar da ma yankin Arewa baki ɗaya.

Lawal ya bayyana haka ne a wajen taron da shi da wasu takwarorinsa suka yi da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed, ranar Juma’a a Washington, D.C.

Mahalarta taron sun haɗa da gwamnonin Zamfara da Benue da Jigawa da Kaduna da Katsina da Kebbi da kuma Neja, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.

Sulamain ya ce Amina ta yaba wa ƙoƙarin da gwamnonin ke yi na samar da maslaha ta din-din-din game da matsalolin da suke addabarsu a yankunansu.

Da yake yi wa Amina bayani kan halin da Zamfara ke ciki Gwamna Dauda Lawal ya yi ƙarin haske kanirin tasirin da amfani da fasahar zamani za ta yi wajen bunƙasa tsaro da kuma buƙatar haɗa ƙarfi wajen aiki da fasahar zamani da ya haɗa da amfani da jirgin sama mara matuƙi da kyamarorin bincike da sauransu, wajen ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a sannan Nijeriya.

“Mun zo nan ne da buƙata guda. Babbar matsalarnu ita ce rashin tsaro, kuma ya kamata a yi wani abu a kai.

“Rashin tsaro ya sa aikin gona ba ya gudana. Muna buƙatar tallafi don ficewa zuwa tsarin noma na zamani ta yadda za mu yi amfani da fasaha wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro,” in ji Lawal.