Manyan ’yan siyasa sun kira ni sanadin maganata, inji Adam Zango

Daga AISHA ASAS

A satuka buyu da suka gabata, fitaccen jarumi a Masa’antar Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana a kafar sada zumunta na TikTok da bayyanai da za mu iya kira da tura ta kai bango, duk da cewa wasu da yawa na kallon faifan bidiyon na Zango a matsayin ishara ga abinda zai iya faruwa da shi nan gaba idan ba a ɗauki mataki ba, wanda wannan tunanin ne ya sa hankullan masoyan jarumin suka ta shi, yayin da suka shiga aika masa da saƙon nuna soyayya da goyon baya gare shi.

Jarumi Adam ya nuna takaicinsa ta yadda Masana’antar Kannywood ba ta kasance uwa ɗaya uba ɗaya ba, inda ya yi iƙirarin waɗanda ya taimakawa da dama sun juya masa baya, tare da maganganu masu zafi kan abinda ya jivinci masana’antar. Har ta kai ya ce waɗanda ya taimaka ba sa tare masa sharar da ake zuba masa sanadiyyar shahara.

A ɓangare ɗaya jarumin ya bayyana kallon da mutane ke masa na mai auri-saki, inda ya bayyana wasu ababen da matan nasa suka yi masa ya kuma yi haƙuri, duk da cewa ba kafai ka ke samun mazan da za su iya haquri da su ba, ciki kuwa har da kama matarsa da ɗan uwansa, da kuma kama matarsa da aikata laifin maɗigo.

Maganganun na Zango sun tayar da ƙurar da aka kwana biyu ba a same ta ba, wanda ta yi sanadin shafe duk wani abu da ke tashe a lokacin.

Abin mamaki game da wannan faifan bidiyon shi ne, ba a iya abokanen sana’ar tasa mayar da martanin ya tsaya ba, domin an samu malamai da suka tattauna wasu daga kalaman na jarumin a cikin lokutan karatukansu, sai kuma zaurukan mata da maza na kafafen sada zumnuta ɗaɗaiku ne ba su yi zancen ba tare kuma za ɗumama shi na tsayin lokaci ba.

A wani ɓangare idan ka waiwaya kuwa, za ka tarar da dogayen muhawara da ke kacamewa tsakanin masoya da mabiyan jarumin, yadda kowanne daga ciki ke ƙoƙarin bayyana fahimtarsa ko ra’ayinsa kan lamarin ya sa ya zama tamkar a lokacin yaqin neman zaɓe, domin har faɗace-faɗace ba a bari baya ba.

A fahimtar da na yi wa lamarin, koda neman janyo hankalin mutane kansa ne jarumin ke yi kamar yadda wasu ke zargi za mu iya cewa haƙarsa ta cimma ruwa.

Idan za mu koma kan musababbi ko dalilan da ake hasashen ya sanya jarumin yin wannan zazaffan bidiyo, mutane sun karkasu har ba iyaka. Sai dai waɗanda suka fi rinjaye su ne, masu ganin ciwon damuwa ne ke tare da jarumin wanda ɗaya daga cikin alamomin sa akwai irin abinda jarumin ya yi. Sai kuma wasu ke ganin matsalar aljihu ce ta girgia shi har ya furta abinda ya faɗa.

Idan na yi duba da yadda aka yi ta tada jijiyoyin wuya kan ƙoƙarin tabbatar da matsalar damuwa ke damun jarumin ko matsalar aljihu sai na ga kamar iska ne ke wahalar da mai kayan kara, domin dukkansu biyu boka ɗaya ne suke yi wa tsafi.

Matsalar damuwa kan faru ta dalilai da dama ciki kuwa har da rashin kuɗi, don haka dukkan waɗanda ke musun za a iya cewa sun yi gaskiya.

Ɗaya daga cikin dalilan da suka ƙara ruwa wutar tashen wannan lamari na jarumi Adam A. Zango akwai rashin sani kan ita kanta cutar damuwa.

Kamar yadda wani likita ya tava fada a shekarun baya, yayin da muke wata tattaunawa, cewa, cutar damuwa a wurin mutumin Arewa ƙarya ce, don haka ya yi wa cutar gurbi a ɓangaren matsalar asiri ko jifa da makamantansu.

Har a lokacin da ake tattauna wannan lamari wasu suna bijirewa yarda da cuta wai ita cutar damuwa, inda suke ganin wata hanya ce ta bada kariya ga wanda ya yi san ransa.

Idan muka yi duba da wasu ababe a rayuwar jarumin da yadda ababe suka koma, za mu iya cewa ba shakka yana da abinda zai iya kaishi ga cuta ta damuwa, ba wai ina goyon bayan hakan ba, sai dai bisa hujjoji da zan zayyano.

Adam A. Zango ya yi tashe a Masana’antar Kannywood ta yadda duk wani fim da zai amsa sunansa to tabbas sai an haska fuskarsa a ciki, wanda hakan ya sa ayyuka sai ya ture, ko na ce sai ya zava, don haka a nan za mu ce kuɗi da suna sun zauna. Ita kuma shuhura tamakar giya ce, idan ta sarƙe ka, ka shagaltu da ita, yayin da ta nemi rabuwa da kai za ka iya zautuwa.

Zango ya kasance mutum da ya damu da ra’ayin mutane kansa, za ku yarda da hakan idan kun yi duba da yadda yake kawo wasu ababe da ya shafi rayuwarsa a kafafen zadarwa a ƙoƙarin wanke kansa, wanda da yawa daga cikin jaruman ba sa yin hakan, dalilin sun fahimci shahara ce ta janyo masu, kuma abin zai wuce. Wataƙila hakan ba zai rasa nasaba da yadda aka mayar da shi kwandon shara ba, don idan an taɓo shi zai mayar da martani. Dama mai tokana ya fi son mai tankawa.

Jarumi Adam ya miqa rayuwarsa ga harkar fim ko ince Masana’anatar Kannywood, don haka ya shagaltu daga tunanin zamani riga ce, yau za ka saka, gobe wani ne za ka ganta a jikinsa, kenan zai iya samun kansa a matsanaciyar damuwa yayin da masana’antar ta fara ajiye shi a gefe, ko ta durƙushe ta kasa samar masa abinda ta saba ba shi a baya.

Sai zance na rabuwar aurensa da matarsa ta ƙarshe Hafsat, wanda wasu ke ganin tsananin damuwar rasata ne ya jefa shi a damuwa, har ta kai shi ga wannan ciwo. Hakan zai iya yiwa, kuma zai iya yiwa ko don gudun zagin mutane ya so auren nasa ya zauna don kar a ci gaba da kiransa mai auri-saki, wanda ya bayyana tun a farkon fara sakin matan nasa yana mayuqar ɓata masa rai. 

Daga ƙarshe masu azancin zance sun ce, gida biyu maganin gobara, wataƙila wannan kalmar ba ta samu wurin zama a tunanin jarumin ba, don haka ne ya kalli harkar ta fim a matsayin abinda zai iya riƙe shi har qarshen rayuwarsa, inda rashin samun haka ya sa ya karkata kan waɗanda ya taimakawa don a rama taƙwarƙwara, saidai fahimtar ba su shirya yi masa abinda ya yi masu ba ya ƙara masa damuwa kan wadda yake tare da ita. 

Mai karatu zai iya tafiya da fahimta ta idan ya yi duba da goge faifan bidiyon da jarumin ya yi, wanda ke nuni da aiki ne na ingizawar zciyar da ke cike da damuwa ko fushi.

Abu na biyu kuwa sabon faifan bidiyon da ya saki daga baya, wanda ya bayyana nadamarsa kan ababen da ya faɗa a wancan bidiyon.

A cikin kalam jarumin ya bayyana abinda ya yi a matsayin kuskure, saidai kuskuren da zai iya kai ga gyara, inda ya sanar ta sanadiyyar wannan bidiyon da ya yi wasu manya-manyan ‘yan siyasa da ma bai san su ba sun kira shi, kuma sun ba shi shawarwari da sauransu, kunga a nan idan dai zancen bushewar aljihu ne, akwai yiwar an yi masa wanka.

Idan kun saurari kalaman jarumin har zuwa ƙarshe, za ku fahimci zancen da nake yi na dukka abinda ake gardama kansa abu ɗaya ne, domin ba inda ya musanta rashin taimakon da yake zancen abokanen sana’arsa da ya taimakawa na yi masa ba zance ne yake na kuɗi ba, kuma bai musanta ba zance ne na da kai ne a sama a baya, yanzu kuma waninka ne sai ka nema a harkar sana’ar tasu. Don haka ya bayyana neman taimakon a matsayin “ko na kuɗi ko kuma na wani abin daman.”