Ina ‘ya’yanku suka je yawon sallah?

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da yau, barkanmu da ganin ƙarshen watan alfarma, kuma barkanmu da sallah. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya sa mun dace, Ya kuma maimaita mana.

A satin farko na sallah aka samu wata ‘yar muhawara game da yawon sallah da yaranmu ke yi musamman ma mata. Inda wani ya yi zancen tururuwar da yara maza da shekarunsu bai haura 17 zuwa 19 ke yi wurin siyan kwararon roba a lokacin abin tayar da hankali ne.

Da wannan ne wasu suka yi wa wannan kalaman ca, inda suke ƙaryata shi tare da nisanta yaran da abinda ake kallon sun aikata a lokacin bukukuwan sallah.

Ya ke uwa! Ba wai zan tabbatar da sahihancin wannan zancen ko akasin shi ba, zan so kafin ki tada jijiyoyin wuya kan wannan furucin ki fara da tambayar kanki ina yaranki suka je yawon sallah? Ko me suka aikata a lokacin bukukuwan sallah?

Idan ba ki ba wa kanki wannan amsar ba to ba ki cancanci shiga layin masu sukar maganar da wataƙila wanda ya yi ta sana’arshi ce.

Idan muka yi duba da yadda rayuwa ta koma a yanzu, da yadda a kullum tarbiyyar da muke ba wa ‘ya’yanmu ta zama muna tubka zamani na mana warwara, za mu fahimci cewa ba abin mamaki ba ne idan aka ce sheɗan ya shiryawa yara ƙanana wannan mummunar ɗabi’a ba. Duba da irin hotuna da bidiyon batsa da rubutun batsa suka zama ruwan dare, ba yaro ba babba.

Don haka shawata ta gare ki ya ke uwa, ki ajiye musu, ki koma bibiyar ababen da ‘ya’yanki ke yi a bayan idonki, kamar yadda ake cewa, ba a shedar ɗan yau.

Yayin da aka ta shi bukukuwan sallah, ki kasa, ki tsare, ki tabbatar kin san inda ya’yanki za su yi shagulgulan murnar sallah, musamman ma ‘ya’ya mata, domin wallahi waɗannan ababe da ku ke gani tamkar almara suna faruwa, har ƙasa da shekarun da aka ambata ana samu.

Don haka mu yi iya yin mu, domin duk yadda zamani ya ɓullo da hanyoyin lalata tarbiyya, akwai hanyoyin gyara ko sa ido ga iyaye.

Amma idan ki ka naɗe hannaye, ki ka toshe kunne daga jin gaskiya, to fa nadama ce za ta biyo baya.

Allah Ya shiryar mana ‘ya’yanmu da na Musulmi bakiɗaya.