‘Yan sandan Kenyan sun cika hannu da shugaban Binance da ya tsere daga Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Yaƙi da Manyan Laifuka na Ƙasa da Kasa, sun damƙe shugaban kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla, a ƙasar Kenya.

MANHAJA ta tattaro cewar, ‘yan sandan na nan suna shirin miƙa Anjarwalla ga Gwamnatin Nijeriya bayan kammala ɓangarensu.

Majiya ta kusa da gwamnati wadda ba ta amnince a ambaci sunanta ba, ita ce ta tabbatar da kama Anjarwalla ran Lahadi da daddare.

Idan za a iya tunawa, MANHAJA ta rawaito Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa ta gano inda tserarren shugaban Binance da ya tsere, Nadeem Anjarwalla ya ɓoye.

Gwamnatin ta ce, ta gano Anjarwalla yana ƙasar Kenya bayan tserewar shugaban Binance daga kulle Nijeriya a kwanakin baya.

Dalilin haka ne ma ya sa hukumar EFCC da rundunar ‘yan sandan Nijeriya da na Kenya suka fara tattaunawa kan yadda za a dawo da shi Nijeriya.

Anjarwalla bayan tserewarsa ya gudu ne ƙasar Kenya domin gujewa hukunci.

Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da haka inda ta ce ana ƙoƙarin dawo da shi Nijeriya.

“Mun same shi, mun san inda ya ke, ya na ƙasar Kenya, muna aiki da wasu hukumomi domin tabbatar da cewa ya dawo Nijeriya,” inji majiyar.

Hukumomin tsaron Nijeriya da rundunar ‘yan sandan ƙasa da ƙasa sun haɗa kai da ‘yan sandan Kenya domin dawo da shi Nijeriya ya fuskanci hukunci.

Hukumar EFCC na zargin Anjarwalla kan wasu laifuffuka biyar da suka shafi rashin biyan haraji da badaƙalar kuɗi kimanin dala miliyan 35.4 da sauransu.

Ɗaya daga cikin abokan aikin Anjarwalla, Tigran Gambaryan ya na hannun jami’an EFCC tun a kwanakin baya.

Idan dai ba a manta ba, shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga kulle da ake masa a birnin Tarayya Abuja.

A na zargin Anjarwalla da sava dokokin ƙasa da suka haɗa da rashin biyan haraji da sauran laifuffuka.

Daga bisani, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce sun ɗauki mataki kan waɗanda tsaron Anjarwalla ke hannunsu.