Jigawa za ta yi wa yara miliyan ɗaya allurar riga-kafin shan inna

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya tsab don yi wa ƙananan yara su miliyan ɗaya da rabi allurar rigakafin shan inna a matsayin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na hana cutar ɓulla a jihar.

Darakta a hukumar lafiya matakin farko, Dakta Shehu Sambo, shi ne ya sanar da hakan ga taron manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da shirin allurar na bana a fadar Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammed Sunusi a ranar Litinin.

Jami’in ya ce yara miliyan ɗaya da rabi ake sa sunasa ran za su amshi allurar a fadɗn Jihar.

Ya ƙara da cewa, an ɗauki ma’aikatan wucin gadi sama da mutum dubu don tabbatar da shirin ya cimma nasara.

Ya ce shirin zai zai shafi yara ‘yan ƙasa da shekara biyar, kuma an sako masu ruwa da tsaki kamar sarakuna da malamai cikin shirin domin tabbatar da ba a samu matsala ba.

A cewarsa, Mataimakin gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Muhd Rolla, shi ne zai zama shugaban shirin rigakafin a matakin Jihar, yayin da shugabannin ƙananan hukumomin 27 da jihar ke da su za su kasance iyayen shirin.