Yadda bikin Hawan Daushe ya laƙume rayuka huɗu a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Mutane huɗu ne cikinsu har da ɗan wani fitaccen hakimi aka kashe a wani taho-mugama da ya auku a tsakanin wani gungun abokan adawa biyu yayin da ake yin Hawan Daushe na ƙaramar Salla a garin Bauchi.

Taho-mugamar ta kuma haifar da raunuka ga wasu jama’a mabiya tawagar mahaya dawaki dake cikin jerin gwano hawan na daushe, wadda mai Martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu yakan yi kashegarin sallah, walau Eid-el fitr ko Eid-el Kabir na kowace shekara.

Gungun abokan adawar biyu sune da ta ‘Yan-Babeli, wacce zaunanniya ce dake bayar da gudummawa kan yaƙi da ‘yan ta’adda, da kuma ta mafarauta wacce take tafe tare mahaya dawaki na tawagar hawan daushe ta Hakimin Miri dake cikin Ƙaramar hukumar Bauchi.

Taho-mugamar dai, kamar yadda wani tushe mai ƙarfi ya habarta, ya faru ne lokacin da jerin gwanon mahaya dawaki hakimai, masu littafi ko dagatai da masu riƙe da sarautun gargajiya suke cikin tawagar hawan daushe da Sarkin Bauchi yake jagoranta zuwa Gidan Gwamnati da komawarsa zuwa fada.

Kamar yadda mahabartar ta ruwaito, su ‘yan-babeli ne suka yi tseko wa jerin wasu dawakai dake cikin tawagar na hawan daushe bisa wani dalili da ba’a fayyace ba, daga nan sai rigima ta kaure tsakanin su da mahaya dawaki, har ta kai ga doke-doke a tsakani, lamarin da bai yi daɗi ga tawagar hakimin ba.

Wannan hargitsi ne ya tilasta wa mafarauta dake cikin tawagar hakimin suka shiga mayar da martani ta hanyar harba bindigogin toka sama, hayaƙi ya tirniƙe, yadda kowane ɗan adawar tawaga ke cewa, in baka yi, bani wuri, kuma wuri ya rincaɓe, kamar yadda maruwai ci ya habarta.

A cikin wannan tirka-tirka ne aka ce an bugi ɗan hakimin da wani makami, data kai ga sulwantar ransa, yayin da wasu mutane suka samu raunuka dabam-dabam, kafin da jami’an tsaro suka yi wajen tsinke tare da kawo ƙarshen tarzomar, har ma da kame wasu daga cikin masu faɗan.

Yunƙurin da wannan manemin labari yayi domin samun tabbacin aukuwar wannan lamari daga kakakin rundunar ‘yan-sanda ta jiha a lokacin aukuwar wannan mummunan lamari yaci tura domin layin tangaraho na kakakin, Sufuritandan ‘Yan-Sanda Ahmed Mohammed Wakil ta cunkushe.

Tuni dai, Gwamnan jiha, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya ziyarci gidan hakimin na Miri inda ya yi masa ta’aziyar rasuwar ɗan nasa mai suna, Muhammadu Ghani.

Gwamna Bala Mohammed wanda ya nuna takaicin sa bisa faruwar wannan mummunar lamari, ya bayyana cewar, bincike yana kan gudana domin samo dalilan da suka haddasa mutuwar wannan matashi.

Sanata Bala, wanda ya jagoranci jiga-jigan gwamnati zuwa wannan ta’aziyya, ya bayyana lamarin a matsayin abin kaico daya faru a ranar da ake murnar kammala azumin sharu Ramadana mai kwanakin wata 30 ko 29.

Dugunzu-mamme Bala Mohammed ya bayyana cewar, ya umarci rundunar ‘yan-sanda da sauran hukumomin tsaro su gaggauta yin cikakken bincike da zummar zakulo waɗanda suka aikata wannan aika-aika daya tayar da hankalin al-umma.

Gwamnan ya kuma sha alwashin cewar, duk wani maluƙi da aka samu cikin aikata wannan taɓargaza, babu ko shakka zai ɗanɗana kudar sa.

Ya yi addu’ar Allah ya turɓuɗa ran mamacin a cikin Jannatul Firdaus, yana mai baiwa iyakan haƙurin jure wannan babban rashi mai sanyaya zukata.

Da yake mayar da jawabi, hakimin na ƙasar Miri, Mallam Hussaini Abubakar ya godewa Gwamna bisa nuna damuwar sa Alan abinda ya faru, yana mai roƙon sa da’a tsanan ta bincike domin zaƙulo waɗanda suka kashe masa ɗa.

Tun da farko dai, a ranar Sallah sai da babban Limamin Bauchi, Alh. Bala Ahmed Baban-Inna a cikin huɗubar sa, a madadin gwamnati, gwamna da sarki, yayi kira ga kowane uba da uwar dasu kula da tarbiyyar ‘ya’yayen su domin kasancewar su cikin al’umma ta gari.

Alh. Bala Baban-Inna ya bayyana takaicin sa matuƙa-gaya yadda matasa ‘yan sara-suka sukayi tacin karnukan su babu babbaka a cikin Azumin Sharu Free Ramadana a Unguwanni cikin gari dabam-dabam, musamman a Kwanar Ƙwaila, Unguwannin Hardo da Mahaukata da sauran su, yadda da zaran ansha ruwa, sai a tsumduma cikin ta’addancin sara-suka har zuwa ƙarshen watan na azumi.

Baban-Inna ya jaddada a cikin wa’azin nasa da cewar, “Mu dai namu mu faɗa ne, masu sadarwa ne. Gwamnati ce tace idan mun faɗi, ta faɗi, wanda ya gani babu daɗi ya zargi kan sa”.

Babban Limamin ya kuma gabatar da koken jama’a wa gwamnati da cewar, “Suna roƙon gwamnati ta fito da wani tsari wanda zai yi maganin rashin tarbiyyar yara ko matasa, musamman kan halayen sace-sace, shaye-shaye, da duk abubuwa da zasu ɓata zamantakewar al’umma.”

Har ila yau, jama’a sun ƙara da cewa, “Muna roƙon gwamnati ta ɗauki mataki akan masu sayen kayan sata domin, kamar yadda suka ce, idan ba’a samu mai saye ba, ba za’a samu masu yin satar ba. Don haka, gwamnati ta sami wani mataki mai ƙarfi da zata ɗauka kan wannan lamari.

Jama’a kuma sun nemi gwamnati ta shigo cikin lamarin tsadar kayayyakin ayyukan noma ta yadda talaka zai samu damar yin noma domin ciyar da kai, suna masu cewar, yana da kyau gwamnati ta bijiro da wasu tsare-tsaren noma da za’a tsumduma matasa a cikin da zummar rage masu zaman kashe wando, da rage ta’addanci a tsakanin su.

Babban Limamin na Bauchi sai ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki daya baiwa jama’a ikon cigaba da yin addu’o’i, kamar yadda Gwamnatin jiha, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed da Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu suka yi kira da cewar, a cigaba da addu’o’i na zaman lafiya da kore masifu a cikin al’umma.

Baban-Inna ya kuma yi nuni da wani hadisi na Manzon Allah, Muhammad (SAW) inda ya ce, “Babu abinda ya rage wa duniya face masifu masu bibiyar juna, waɗanda basu da magani face addu’o’in bayin Allah”, ‘Addu’a itace makamin mu, don haka, ake kira a cigaba da yin addu’o’i, da kuma addu’o’i wa shugabanni domin su zartar da adalci a tsakanin mabiyan su.”