Kotun Tarayya ta soke dakatarwar da aka yi wa Ganduje

*Ɗan Ganduje ya yaba wa gwamnatin Kano bisa tuhumar mahaifinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta jinjine dakatarwar da aka yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a mazabarsa.

Mai Shari’a Abdullahi Liman ya umarci shugabannin Mazaɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, kada su yi aiki da umarnin babbar kotun jihar na dakatar da shugaban jam’iyyar.

Umarnin Babbar Kotun Tarayyar na zuwa ne awa 24 da babbar kotun jihar ta amince da bukatar shugabannin mazavar ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, saboda gwamnatin jihar mai ci na zarginsa da almundahana.

Alƙalin ya hana duk waɗanda umarnin kotun jihar ya shafa bin umarnin, har sai ya saurari ƙarar da Ganduje ya shigar gabansa ne neman adalci a saurari ɓangarensa.

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan nan na Afrilu domin sauraren buƙatar ta shugaban jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Kano.

Shugabannin APC na mazaɓar Ganduje da lauyan shugaban na APC, Jazuli Mustapha, ya shigar ƙara su ne Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da kuma Abubakar Daudu.

Sauran waɗanda ake ƙara kuma su ne hukumomin tsaro da shugabanninsu.

Ɗan Ganduje ya yaba wa gwamnatin Kano bisa tuhumar mahaifinsa:

Abdulazeez Ganduje, babban ɗan shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya kai wa shugaban Hukumar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Muhuyi Magaji ziyara a ofishinsa.

Abdulazeez ya ziyarci Magaji ne a yammacin Laraba domin nuna goyon bayansa ga yunqurin shugaban na yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya kuma bayyana amincewarsa da tuhume-tuhumen da hukumar ta yi wa mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma ɗan uwansa.

Abdulazeez ya bayyana damuwarsa ga shugaban hukumar bisa rashin adalci da aka cire shi daga muƙamin darakta na ɗaya daga cikin cibiyoyin da ake shari’a, inda ya nuna damuwarsa kan yadda aka kore shi ba tare da amincewarsa ba.

A watan Satumbar 2021, Abdulazeez ya kai ƙara ga Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) kan mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje, inda ya zarge ta da cin hanci da rashawa. A cikin koken, ya yi cikakken bayani kan yadda wani ma’aikacin kadarori ya tuntuɓe shi domin ya taimaka wajen samun fili a Kano kan maƙudan kuɗaɗe.

An bayyana cewa Abdulazeez ya biya wa mahaifiyarsa Hafast Ganduje kuɗaɗen da aka ƙayyade a dalar Amurka. Duk da haka, daga baya maginin kadarorin ya gano cewa filin da ya biya an ware shi ne ga wasu masu saye kuma ya nemi a mayar masa da kuɗaɗensa.

A baya dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta ɗauki matakin shari’a kan Ganduje, da matarsa, Hafsat Umar, da ɗansa Umar Abdullahi Umar, da wasu mutane biyar bisa zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗe da suka kai biliyoyin naira. Sauran mutanen da lamarin ya shafa sun haɗa da Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Limited.

Don dakushe Tinubu a Kano ake ƙulla makircin dakatar da ni – Ganduje:

Shugaban Jam’iyyar APC ta Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a ranar Laraba, ya bayyana matakin dakatar da shi daga muƙaminsa a ranar Litinin ɗin da ta gabata, a matsayin makirci domin dakushe tasirin shugaban ƙasa, Bola Tinubu wajen samun qƙuri’u kafin zaven 2027.

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar zartarwa na mazaɓarsa 27 a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da ’yan kwamitin ayyuka na ƙasa da kuma shugabannin zartarwa na jam’iyyar APC na Kano.

Duk da ya tsallake rijiya da baya daga dakatarwar da aka yi a ranar Litinin ɗin da ta gabata, a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya caccaki tsohon shugaban jam’iyyar tare da hana shi bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar. Wata babbar kotun jihar Kano ce ta ba da umarnin.

A yayin da ya ke mayar da martani kan lamarin, Ganduje ya shaida wa tawagar a ranar Laraba cewa binciken da ya gudanar ya nuna cewa makircin da aka ƙulla masa na fitowa ne daga jam’iyyar NNPP da Gwamnan Kano, Abba Yusuf.