EFCC na son tsoma sojoji a dambarwa EFCC da Yahaya Bello

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Larabar da ta gabata ne dai tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya yi kira ga Shugaban Qasa Bola Tinubu da ya ja wa Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa ta EFCC kunne bisa zargin ƙin bin umarnin kotu, wacce ta hana a kama shi.

To, sai dai kuma a ranar Alhamis Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, ta na duba yiwuwar tsoma rundunar sojojin Nijeriya a cikin dambarwar, don kamo shi ɗin.

Tsohon gwamnan, a wata sanarwa da jami’in yaɗa labaransa, Mista Onogwu Muhammed, ya fitar a Abuja, ya ce “Nijeriya ba ƙasa ce maras doka”.

Sanarwar ta cigaba da cewa: “da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar yau (Laraba), 17 ga watan Afrilu,  wasu waɗanda suka bayyana kan su a matsayin jami’an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC sun isa unguwar Wuse Zone 4 gidan Alhaji Yahaya Bello domin kama shi.

“Wannan ya biyo bayan umarnin da babbar kotun shari’a ta Lokoja ta bayar a ranar 9 ga watan Fabrairun 2024 a ƙara mai lamba HCL/68M/2024 tsakanin Alhaji Yahaya Bello da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, tare da hana hukumar ko dai ta hanyar ita kanta ko jami’anta daga cin zarafi, kamawa, tsarewa ko gurfanar da Alhaji Yahaya Bello, har zuwa lokacin da za a saurare shi da kuma yanke shawarar aiwatar da muhimman haƙƙoƙi.

“Hukumar EFCC ta cika da wannan umarnin a ranar 12 ga Fabrairu 2024 da kuma ranar 26 ga Fabrairu 2024; Hukumar EFCC ta shigar da ƙara (Qara Mai lamba:

CA/ABJ/CV/175/2024: Hukumar Yaqi da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati) da Alhaji Yahaya Bello, bisa wannan umurni da aka ce ga Kotun ɗaukaka ƙara ta Abuja.

“An ɗaukaka ƙara ne tare da buƙatar a cigaba da aiwatar da umarnin babban kotun da kotun ɗaukaka ƙara ta ɗage cigaba da sauraren qarar har zuwa ranar 22 ga Afrilu 2024.

“Bugu da ƙari kuma, za a yanke hukunci kan ƙarar da ke tsakanin Bello da EFCC da tsakar rana a Lokoja.

“Sabanin abubuwan da aka ambata a baya, yanzu hukumar EFCC ta killace gidan tsohon gwamnan inda take neman kama shi wanda ya sava wa umarnin da aka ba ta!

Ministan Shari’a ya buƙaci Yahaya Bello da ya miƙa kansa: Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta gargaɗi ‘yan Nijeriya da kada su hana hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta’annati (EFCC) gudanar da ayyukanta da ya dace.

Wannan gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) ya fitar a Abuja ranar Alhamis.

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, na cigaba da kawo cikas ga ƙoƙarin da jami’an hukumar ke yi na cafke shi kan al’amuran da suka shafi cin hanci da rashawa.

Umarnin kotuna sun ci karo da juna yayin da yunƙurin EFCC na kama Yahaya Bello ya samu tsaiko:

A wata arangama da aka yi na umarnin kotu, babbar kotun jihar Kogi da ke Lokoja da kuma babbar kotun tarayya Abuja a ranar Laraba sun bayar da umarni masu cin karo da juna kan hukumar yaqi da masu yi wa tattalin arzikin qasa zagon ƙasa ta EFCC bisa ikonta na cafke tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Daga babban kotun jihar Kogi ya zo da umarnin hana EFCC tauye haƙƙin ɗan Adam na Bello.

Sai dai babbar kotun tarayya ta bayar da wata doka ta hanyar bai wa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ikon kama tsohon gwamnan.

Umarnin da ke cin karo da juna ya zo ne yayin da jami’an EFCC suka kai farmaki gidan tsohon gwamnan Abuja a ranar Laraba.

Yadda EFCC ke duba yiwuwar neman taimakon sojoji: Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron qarar da hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta shigar kan tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ɗage ƙarar zuwa 23 ga watan Afrilu ne bayan lauyan EFCC, Kemi Phinro, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin bai halarci zaman ba saboda “wani wanda yake da kariya na ba shi mafaka”, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ruwaito.

Lauyan ya ƙara da cewa hukumar na duba yiwuwar haɗa kai da dakarun soja don ganin sun kama tsohon gwamnan.

Tun a ranar Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Adodo ne ya fice da Yahaya a motarsa lokacin da jami’an hukumar suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Nijeriya ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo: Hukumar EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa-a-jallo.

Matakin hukumar na zuwa ne ‘yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar ta shigar saboda wanda take zargin bai halarci zaman kotun ba.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC mai suna Kemi Phinro ya faɗa mata cewa “wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka.

“EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2,” inji hukumar cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na zumunta ɗauke da hoton tsohon gwamnan.

Tun a ranar Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Adodo ne ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami’an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin.

Lauyan hukumar ya kuma ce suna duba yiwuwar neman taimakon rundunar sojin Nijeriya wajen kamawa tare da gurfanar da shi a gaban kotun.