Yadda wasu yara biyar suka mutu lokaci guda a Neja

Daga BASHIR ISAH

Wasu yara biyar sun mutu a cikin wata mota da suka shiga suna wasa, inda motar ta kulle kanta suka kasa fita.

Lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi, an ce an sha famar neman yaran a unguwa alhali ba a san cewa suna kulle cikin motar ba, daga bisani aka gano su baki ɗayansu a mace.

Shafin Tsalle Ɗaya ya ce iftila’in ya faru ne a Unguwar Albishiri da ke daura da yankin Gurara a hanyar Bida, Minna, Jihar Neja.

Majiyarmu ta ce huɗu daga cikin yaran mata ne, sannan ɗaya namiji.

An ce uku daga cikin yaran, yaran mutum guda ne wanda kuma su ke nan da Allah ya azurta iyayen da su.