Gobe Tinubu zai ƙaddamar da taron yaƙi da ta’addanci a Afirka

Daga WAKILINMU

A gobe Litinin, 22 ga watan Afrilu idan Allah y’Ya kai mu, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai buɗe taron yaƙi da ta’addanci a Afirka wanda za a yi a Abuja.

Nijeriya tare da goyon bayan ofishin yaƙi da ta’addanci na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNOCT) ce ta shirya wannan taro wanda aka yi masa laƙabi da “Ƙarfafa Dangantakar Nahiyar Afirka Don Gina Cibiyoyin Taron Dangin Magance Barazanar Ta’addanci”.

Maƙasudin taron na kwana ɗaya shi ne inganta haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci a ɓangarori daban-daban tsakanin ƙasashen yankin, tare da sake fasalin rawar da ƙasashen duniya ke takawa kan batun na ta’addanci a nahiyar, kazalika taron zai jaddada mahimmancin bai wa Nahiyar damar nemo hanyoyin magance matsalolin ta da kanta ba tare da an mata katsalandan ba.

Taron dai zai samar da wani dandali na yin nazari don tantance girman barazanar da ta’addanci ke yi wa nahiyar, da nufin cimma matsaya ta bai-ɗaya kan muhimman matakan shawo kan matsalar.

Har ila yau, taron zai tattauna wasu batutuwan da suka shafi hadin kan nahiyar da haɓaka ƙarfin faɗa-ajin ƙasashen dake mambobin ƙungiyar, da samar da damar yin musayar ilmi da ayyukan ci gaban yankin.

Ana sa ran shugabannin ƙasashe da gwamnatoci da manyan jami’an gwamnati a faɗin Afirka, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da cibiyoyi daban-daban, da wakilan jami’an diflomasiyya, da na ƙungiyoyin fararen hula za su halarci taron.

Malama Amina Mohammed, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, na cikin waɗanda za su halarci taron. Kazalika Mallam Nuhu Ribadu, mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, da Mr. Vladimir Voronkov, mataimakin sakatare-janar a kan yaƙi da ta’addanci na ƙungiyar UNOCT, na cikin masu gabatar da jawabi a ƙarshen taron.