‘Yan bindiga sun kashe sojoji shida a Neja

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a jihar Neja sun bindige sojoji guda shida da wani maharbi ɗaya.

Hakan ya faru ne sakamakon hare-haren da ‘yan bindigar suka kai yankunan Karaga da Rumace a gundumar Bassa da ke cikin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar.

Majiyarmu ta ce lamarin ya ritsa da wasu manoma biyu da suka mutu, sai kuma gidaje da rumbuns’a da babura da aka ƙona yayin harin.

Bayanai sun ce harin ya fara ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sauran yankunan jihohin da suka yi fama da hare-haren ta’addanci sun haɗa Allawa, Bassa da Madaka dukkansu a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro.

Jihar Neja na ɗaya daga jihohin Nijeriya da ke mafa da matsalar tsaro, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da ɗimbin dukiya.