ASUU ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sake kafa Majalisar Gudanarwar Jami’ar Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sake kafa Majalisar Gudanarwar Jami’ar.

A wata sanarwa da shugaban reshen, Farfesa Mohammed Almustapha, ya fitar, kuma ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a, ASUU ta yi Allah-wadai da rusa dukkan kwamitin jami’ar da gwamnatin tarayya ta yi, saboda karya dokar jami’o’i.

Sanarwar ta bayyana damuwa kan rusa shugabannin jami’o’in tarayya ba bisa ƙa’ida ba a watan Yunin 2023 da Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa ta yi, biyo bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar.

ASUU ta jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin da aka kafa da kuma cin gashin kansu na waxannan cibiyoyi.

Bugu da ƙari, ASUU ta nuna rashin amincewa da tallata guraben aiki ba tare da izini ba na ofisoshin mataimakan shugabannin jami’o’in tarayya da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya, wanda ta ga ya sava wa ƙa’idojin da suka dace da kuma barazana ga ’yancin karatu.

Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin tabbatar da gaskiya, daidaito da kuma cancantar zaven shugabannin jami’o’in, inda ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa daga shugaban qasa, Ministan Ilimi, da sauran masu ruwa da tsaki.

Ƙungiyar ASUU-UDUS ta yi kira da a sake fasalin Majalisun Hukumomin Jami’o’in Gwamnati, da kare haƙƙin Jami’o’i, bin ƙa’idojin da aka kafa, da kuma binciki duk wani sava doka da aka yi a Jami’o’in a baya-bayan nan.

Ƙungiyar ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen kare ’yancin cin gashin kai da mutuncin jami’o’in gwamnati domin cigaban tsarin ilimi da kuma makomar aasa.