Biafara na barazana ga Wazobia

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kawo ƙarshen yaƙin basasar Nijeriya a 1970 bai zama ƙarshen muradin masu son raba Nijeriya don neman kafa ƙasar Biafara ta ƙabilar Igbo a Kudu maso gabashin Nijeriya ba. Wannan ya nuna dakarun Nijeriya sun ci nasarar wargaza ɗamarar yaƙin ’yan Biafara ne amma waɗannan masu son kafa ƙasar ’yan aware na nan da muradin su.

Da alamu su kan ma gadar da muradin ga ’ya’yan su ko da bayan sun mutu masu tasowa su ɗora daga inda suka tsaya har sai sun cimma muradin nasu. Ɓullowar ƙungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu ta zama sabuwar tafiya ta yunƙurin kafa wannan ƙasa. Duk da an haramta ƙungiyar tare da ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci, hakan bai hana wasu ci gaba da aiki a madadin ƙungiyar ba, ta hanyar tada fitina da ma kashe duk wanda suka samu dama musamman ’yan Arewa da ke zaune a yankin Kudu maso Gabas.

Haka nan shi ma madugun ƙungiyar Kanu duk da an ce ya yi hijira zuwa Isra’ila amma yana amfani da kafar sadarwa da rediyon yanar gizo wajen kambama wannan manufa tare da zuga magoya bayan sa da su ɗauki duk matakan da za su kunna wuta har sai Nijeriya dunƙulalliya ta ƙone ƙurmus!.

Irin wannan salo da IPOB ta ɗauka na fifita ƙabilanci kan komai ma, na da babban hatsari a Nijeriya mai yawan ƙabilu da bambancin addini da ɓangare. Kamawa ko hukunta duk mai rura wutar ƙiyayyar addini, ƙabilanci ko ɓangaranci na da muhimmancin da ya ke aji ɗaya da samar da abinci da ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa.

Domin ina amfanin baɗi ba rai in har ga tuwo da miya amma ba inuwar da za a zauna a ci?. Tsaron rayuka, dukiya da mutuncin ’yan ƙasa nagari ya zama wajibi ga gwamnatoci musamman Gwamnatin Tarayya. Wani abun takaici shi ne zafin ƙiyayyar ƙabilanci ya kan gallabi haɗin kan ’yan jam’iyya ɗaya tsakanin tarayya da wasu jihohi, inda za ka taras gwamnatin tarayya na ambata wata matsaya, amma wasu gwamnoni ’yan jam’iyyar ta na ɗaukar mataki akasin hakan don tsananin wutar ƙiyayyar ƙabilanci.

Babban misali shi ne a wajen kafa rundunar Yarbawa zalla ta Amotekun wacce akasarin gwamnonin da ke bayan ta ’yan APC ne, amma sam ba su kula kururuwar gwamnatin su, ta APC ta tarayya ba wajen rage kaifin wannan runduna. Yanzu wannan runduna ta zama ta sabuwar ’yan sanda mallakar Yarbawa da kare muradun Yarbawa maimakon na duk mazauna yankin Kudu maso yammacin Nijeriya.

Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya na wancan lokaci Muhammadu Adamu ya tura tawagar ƙwararru don bincikar miyagun hare-hare kan shalkwatar rundunar a Jihar Imo da wasu sassa na ’yan sanda a jihar.

Jihar na daga ta kan kaba mai mallakar dakarun ’yan awaren Biafara/IPOB da ke tunanin ta hanyar kashe ’yan Arewa za su cimma burin su na kafa kasa kamar yadda madugun su marigayi Odumegwu Ojukwu ya gadar mu su muradin.

Sanarwar ba ta yi magana kan kashe wasu ’yan kasuwa 7 ’yan Arewa a jihar ta Imo ba.

Harin dai ya faru ne a yankuna biyu da su ka haxa da Orlu mai hatsari inda ’yan bindiga su ka buxe wuta haka kawai kan ’yan kasuwar Arewa. Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan harin ke aukuwa a yankin ba.

Hakanan masu rajin kafa qasar ’yan aware ta Biafara kan kai hare-hare da kashe mutan Arewa a yankin don tada fitina.

ɗaukar matakin gaggawa kan wannan yanayi na da muhimmanci don hana ramuwar gayya a wasu sassan Nijeriya kan waɗanda ba su da laifin komai.

Gwamnan Jihar Hope Uzodinma ya nuna damuwa ga kisan gillar da bayyana ɗaukar matakan kwantar da hankali.

Gaskiya inda za a ma kwantar da hankalin ta hanyar daina aukuwar irin wannan kisan gilla, da kuwa da sauƙi. Abun da zai zama babbar mafita shi ne adalci ta hanyar cafko waɗanda suka yi kisan da zartar mu su hukunci daidai laifin da suka aikata. Bayan nan sai a duba biyan diyyar rayuka da dukiyoyin da a ka salwantar haka siddan.