Ilimin ‘ya’ya mata a zamanin da ke wanzuwa

Daga AMINA HASSAN ABDULSALAM

A tarihin duniya mata na da wani irin tasiri da muhimanci a rayuwa kasancewarsu iyaye mata ko matan aure, ko ‘ya’ya mata ko kuma dai a taƙaice iyayen al’umma. Gudunmawar mata a cikin al’umma na da dumbin yawan gaske saboda waxan can dalilan da na ambata a sama. Ta hanyar auratayya da su ake haɗa nasaba mai kyau ake kuma faɗaɗa nasabar nan zuwa inda ma ba zata ba. Gudunmawar mata ga cigaban al’umma yana da faɗin gaske kama tun daga lokacin Annabawa zuwa yanzu.

A dalilin haka ne ya kyautu a baiwa mace duk wani ilimi da zai amfane ta ya kuma amfani al’umma, domin masu iya magana sun ce idan aka ilimantar da ɗa namiji guda xaya, shi ka ilimantar amma idan aka ilimantar da ‘ya mace guda ɗaya al’umma aka ilimantar saboda dalilai da dama.

Mene ne ilimi, ilimi shi ne mutum ya waye da abinda bai sani ba, ko ya tashi daga rashin sani izuwa sani ko kuma ya sami haske game da abinda ya shige masa duhu .Hanyoyin samin ilimi sune koyo daga wanda ya sani, ko kuma zama domin ɗaukar karatu daga wanda ya sani wato malami kenan. Shi ilimi ana ɗaukarsa ne a bisa wasu tsari da aka yarda da su, ko a hukumance ko akasinsa wato a gida ko wani gurin taruwa. Shi kansa koyo da koyarwa duk ilimi ne ba sai lallai mai koyo ne za a ce yana ɗiban ilimi ba, har da mai koyarwar ma saboda kullum ya koyar zai sake samin ƙwarewa tare da ƙaruwa da wani ilimin. Bayan an sami ilimin kuma za a sami sauyin yanayi a tare da wanda ya sami ilimi wato kenan ba za asame shi da jahilci ba domin zai bayyanar da wasu ɗabi’u ta masu ilimi ko ta wanda ya sami wayewa, hatta tunanin mai ilimi daban ne da na wanda ba shi da ilimi, yanayin gudanar da al’amuransa ma za su kasance cike da ilimi za su bambanta da na wanda ba shi da ilimi. Mutum ya sami horo akan wani aiki domin samin qwarewa shi ma ilimi ne domin in ba ka da ilimin abu ba za ka iya tafiyar da shi ba.

Tafiya ta yi tafiya zamanunnuka suna ta shuɗewa, maimakon cigaban da muka fara hangowa ya xore, sai kuma ya fara komawa baya saboda talauci da rashin tsaro sun kassara ilimin mata wanda a da can ake ganin kamar an dawo daga rakiyar barin ‘ya’ya mata a baya. Tabbas shekarun da dama baya an bar mata a baya, sai aka fara wayewa a hankali a na baiwa ‘ya’ya mata ilimi, amma a yanzu haka ilimin mata ya fara samin tasgaro. Ilimi ko wanne iri ne ilimi ne walau na addini ko na zamani, kowanne yana da matsayinsa kuma ɗaya ba ya hana ɗaya. Zan xauki Arewa a misali, a da can an yi fama da iyaye domin ganin sun bar ‘ya’yansu mata su yi boko, a wancan lokacin wasu daga cikin talakawa sun amince ‘ya’yansu mata su yi boko, har ta kawo cewa ‘ya’yan waɗan can talakawa sun zama wasu jigogi abin kwatance a cikin al’umma. Rukuni na biyu kuma sune ‘ya’yan sarakai da ‘ya’yan masu arziƙi sun samu sun ci gajiyar ilimi.

Cikin ɗan ƙanƙanen lokacin an sami sauyin lamura wanda ka iya mayar da hannun agaogo baya domin talauci da rashin tsaro ya daƙile ilimin ‘ya’ya mata har ta kai wasu daga cikin iyayen yara mata mara sa gata ke cewa ai daman ilimin ‘ya mace ba tilas ba ne bare kuma an fara kame musu yaran makaranta ana garkuwa da su. Shi kuwa xa namji duk rintsi yana da damammaki da yawa da suka fi na ‘ya mace, ita ita ce dai abin ji .

Kamar yadda na faxa a baya koyon wani abu kamar sana’ar hannu shima ilimi ne da zai kai ga mace ta dogara da kanta har ta ba da tata gudunmawa ga al’umma, cimma hakan na da alaƙa da zama lafiya da kwanciyar hankali, a ya yin da aka rasa waxan nan abaibaɗai babu yadda za ayi a yaxa ilimi a wuraren da ake zaman fargabar abindda zai iya faruwa ga lafiyar ɗalibai mata.

Lokaci ya yi da gwamnatocin yankin da abin ya shafa za su kawo larshen talauci da rashin zamaan lafiya ko don a sami al’umma ingantacciya. A yau masu gatan cikinmu suna da sukunin kai ‘ya’yansu mata ƙasar waje su yi karatu hankali kwance, ‘ya’yan masu madafan iko da na sarakuna duk ba su da matsalar karatun ‘ya’yansu tunda ya zama al’ada karatu a ƙasar waje amma ‘ya’yan mara sa gata fa waxan da ba su da mai taimakonsu ta kowanne fanni walau daga ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyi ko daga uwa-uba gwamnati wace ta kasa ba su tsaro da duk wata damar da za su cigaba da karatu.

Kowa ya san cewa babu yadda za a haxa mace mai ilimi da wace ba ta da ilimi ko kaɗan ta fannoni da dama. Yaran mace mai ilimi za su taso cikin ilimin da za su fara samu daga uwarsu, mai ilimi tana da saurin warware matsala cikin hikima, kulawa da iyali da dangi a neme shi daga mace mai ilimi. Iya jagoranci da wakilci a ba wa mace mai ilimi. Ilimi daɗi ne da shi wanda amfaninsa kan yi naso zuwa ga wanda ya raɓe shi.

Shi dai ilimin nan ba a taƙaita shi ga na zamani ko na addini ba, ko na samin ƙwarewa a wata sana’a ta hannu ba, duk ilimi, ilimi ne mai ɗumbin amfani ga mai shi da kuma sauran jama’a.

A ƙarshe manufa dai a nan ita ce kowanne mai hali da iko ya duba muhallinsa ya hanga ya hango ya ga wace yarinya ce take da rangwamen gata ta kuma cancanci ta sami ilimin nan kamar yadda ‘yan gatan suka samu. Idan aka yi haka za a sami daidaton da zai inganta ƙauna tsakanin talaka da masu shi, zai rage ƙiyayyar da talaka ke yi wa mai shi ba, sannan zai sanya masu ƙyamar talaka su yi koyi da taimakon na ƙasa.

Ba tare da jiran gwanati ba, Arewa ta rungumi tsarin taimakekeniya domin cigaban yankinta, domin muna baya sosai ta fannin ilimin zamani, na addini kuwa sai son barka amma abin tambaya a nan shine ana ko amfani da na addinin da aka samu ko kuwa ilimi ne na jeka na yi ka, ma’ana an dai yi amma ba a amfanawa juna da shi. Amsa na gareku, da ni da ma masu tasowa.

Bisssalam sai mun haɗu a wani jiƙon.