Buhari ya jajanta wa Sarauniya Elizabeth kan rasuwar mijinta

Buhari

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga Sarauniya Elizabeth II ta Ingila dangane da rasuwar mijinta Yarima Philip wanda ya bar duniya yana da shekara 99.

Buhari ya ce, “rasuwar marigayin alama ce ta ƙarshen wani ƙarni. Yarima Philip ya kasance mutum mai muhimmanci wanda duniya ma ta san da shi, wanda ba za a mance da gudunmawarsa ga ƙasashe renon Ingila ba na tsawon zamunna.

“Yarima Philip ya kasance jarumi ne wanda ya yi amfani da dukiyarsa wajen tallafa wa al’umma musamman ma abin da ya shafi tsare gandun daji da sha’anin matasa a ƙasashe sama da 130.”

Shugaba Buhari ya bayyana marigayin a matsayin miji nagari wanda ya yi auri Sarauniya tun a 1947, tare da cewa wannan muhimmin al’amari ne a fagen zamantakewar aure.

Haka nan, Buhari ya jajanta wa Gwamnatin Birtaniya da ƙasashe renon Ingila dangane da wannan babban rashi da ya shafi duniya baki ɗaya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*