Kama muggan makamai a Nijer don safarar su zuwa Maiduguri

A kwanan nan ne jami’an tsaro na Jamhuriyar Nijer suka damƙe wasu muggan makamai da ake yunƙurin shiga da su Nijeriya, don kai su Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda aka fi fama da balahirar yaƙin Boko Haram.

Jami’an qasar Nijer ɗin ne suka bayyana hakan, inda suka ce sun kama wata mota ƙirar Toyota Hilux danlare da muggana makaman da suka haɗa da harsashi da bindigogi ƙirar AK-47, inda aka cafke su a Agadez bayan sun tsallako daga kan iyakar Ƙasar Libya da nufin tunkrar Nijeriya, domin kai su.

Sashen tsaro na Birnin Agadez da ke Nijer shine ya tabbatar da daƙile wannan mugun nufi na yin fasa-qwaurin makamai zuwa yankin Borno da ke Nijeriya, inda sashen ya ce, an yi nufin raba su ne zuwa wasu sassan Arewa maso Gabas na Nijeriya, kamar yadda wata majiya ta tabbatar a ranar Talatar da ta gabata.

Jami’an sun kama masu fasa-ƙwaurin kuma baya ga harsashin bingigogin AK-47 guda 77 da mizayil na roket guda biyu da kuma makamin RPG guda bakwai.

Majiyar ta qara tabbatar da cewa, “Jami’an tsaron Nijer da suke sashen Ingal a Agadez sun kama muggan makamai a cikin mota ƙirar Toyata Hilux da ta ke kan hanyarta ta zuwa Tarayyar Nijeriya daga ƙasar Libya, amma an kama mutum huɗu, waɗanda suke aikata wannan fasa-ƙwauri, yayin da aka damƙe sauran makaman a tare da su, ciki kuwa har da makamin roket.”

Majiyar ta kuma ƙara da cewa, “su na kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri a NIjeriya ne, inda suka keto suka biyo ta Agadez, kuma waɗanda suke aikata fasa-ƙwaurin da aka kama suna kai wa ’yan ta’addar Boko Haram makamai ne.”

Haqiqa wannan ba qaramin abin tsoro ba ne, kuma a lokaci guda babban abin farin ciki, domi kuwa a baya ba a cika samun irin waɗannan bayanai da suke nuna yadda Nijeriya ke aiki tare da maƙotanta wajen ganin an cimma nasarar kawo ƙarshe ko kuma karya lagon masu tayar da ƙayar baya ta hanyar kai hare-hare da kashe al’umma.

A baya kamar ba a samun haɗin kai da ke nuna cewa, maƙotan ƙasashe suna iya sanya idanu yadda ya kamata akan harkokin tsaro ko da kuwa wasu qasashen ya shafa waɗanda ke maƙotaka da su. Babban hatsarin shi ne, yadda hanyar Jamhuriyar Nijer zuwa Tarayyar Nijeriya ta yi ƙaurin suna wajen safarar motoci daga Kwatano. Ta yiwu a baya an sha amfani da wannan safarar ana giftawa da makamai ba tare an ankara ba.

A nan za a iya cewa, lallai Nijeriya ta yi hangen nesa a lokacin da ta rufe kan iyakokinta duk da surutun da aka riƙa yi mata na lallai ta buɗe, domin ana shan wahala daga ciki da wajen ƙasar. Ashe dai gaskiyar Gwamnatin Taraya, domin tana sane da cewa, ana amfani da iyakokin maƙotan ƙasashe ana shigo da makamai. Wannan kamen ya tabbatar da hakan.

A wancan lokacin da iyakokin ke buxe ruf! ƙasashen da ke maƙotaka da ita sun yi ta kukan cewa, hakan zai karya tattalin arzikinsu, saboda yadda gwamnatocinsu da al’ummarsu suka dogara da sgife da fice a Nijeriya, amma sai ta yi kunnen uwar shegu. Da alama bayan kowa ya ji a jikinsa, to yanzu sun tashi tsaye suna kare muradun Nijeriya ta fuskar tsaro.

Ta yiwu ba za su sake bari a yi amfani da lasarsu a shigo da makamai cikin NIjeriya ba, domin sun san cewa, a shirye ƙasar ta ke wajen sake rufe ƙofofinta. Da ma an ce, abin da babba ya hango, yaro ko yah au rimi ba ya iya hango shi.

Lallai sai ’yan Nijeriya su yi murna da farin cikin cewa, wahalar da suka sha ta rufe kan iyakokin ƙasar fiye da tsawon shekara guda, bai tashi a banza ba.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*