Rundunar Ebube Agu ma ta fara cara!

Tawagar Gwamnonin Kudu-maso-gabas

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
 
Sabuwar rundunar ’yan banga da gwamnonin Kudu maso Gabashin Nijeriya suka kafa mai taken “Ebube Agu” da harshen Igbo ta fara cara, saboda jagororin kafa ta na da babban muradin farko na hana kiwo a fili, kamar yadda Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Otom, ya zartar, duk da cewa shi ɗan mabilar Tibi ne kuma daga Arewacin Nijeriya.

A lokacin da na ga labarin gagarumin tsaron gwamnonin na Igbo a garin Owerri, sai na tuno da kafa irin wannan runduna da tun farko gwamnonin yankin Yarabawa suka yi mai taken “Amotekun” da muradin hana kiwon ko sa ƙafar wando ɗaya da makiyaya ko ma jama’ar Arewa da ke kasuwanci a Kudu, musamman idan na tuna abun da ya faru a kasuwar Sasa da ke Ibadan.
Abun da ya zama dabarar siyasa ce, gwamnonin sun yi sauri sun yi tir da hare-haren da ’yan bindiga suka kai kwanan nan a Jihar Imo da lona ofisoshin ’yan sanda.

Kazalika wata logar ta siyasa ita ce mara baya ga matakan da Gwamnatin Tarayya ta ke ɗauka, don inganta lamuran tsaro. Sai dai idan da gaske ne ba siyasa ba, gwamnonin sun yaba ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya ta Shugaba Muhammadu Buhari, me ya sa sai sun ƙara da kafa rundunar ’yan banga da sunan kula da tsaro?

Ya nuna ’yan sanda, sojoji da jami’an tsaron lafiyar farar hula na tarayya ba su gamsar da buƙatun su ba kenan, domin ba mamaki ba za su kare muradin wani yanki su bar muradun ƙasar su ba, da ke da bambancin labila, addini da yanki.
Gwamnonin na Igbo sun ƙaddamar da  rundunar Ebube Agu wato (Damusa Mai Ban Mamaki) don yin dirar mikiya kan duk abun da ya savawa muradun al’ummar Igbo.

Ebube Agu za ta zama ƙungiyar ’yan banga kamar yadda Amotekun ta ke a yankin Kudu maso Yamma.
Gwamnonin sun zaɓi gudanar da taron a garin Owerri ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Ebonyi Dave Umahi. Hakan bai rasa nasaba da zafin masu rajin aware na IPOB da kan kai hare-hare ga waɗanda ba sa ƙauna a jihar.

Haka ma buxe wuta kan wata ƙabila a Orlu da Omuakwa ba wani sabon labari ba ne.
Gwamnonin sun nuna cewa rundunar za ta riƙa sintiri domin inganta lamuran tsaro a yankin na akasarin ƙabilar Igbo, kuma babbar cibiyar ta za ta kasance ne a garin Enugu.

Yanzu dai ya nuna sassan Nijeriya na ɗaukar matakan tsaro don kare muradun yankunan su.

Kwanan nan wasu ’yan bindiga a Jihar Imo suka harbe ’yan kasuwa na arewacin Nijeriya guda bakwai. Zai iya yiwuwa saboda kaucewa ƙarfafa ƙiyayyar ƙabilanci ya sa tsohon Babban Sufeton ’Yan Sanda, Muhammad Adamu ya tura zaratan rundunar zuwa Imo, amma ba don binciko kisan Orlu ba sai dai don hare-hare kan ofisoshin ’yan sanda.

Haƙiƙa sai gwamnatin tarayya ta miƙe tsaye ta haɗa kan yankunan Nijeriya bakiɗaya, ta hanyar ƙarfafa tasirin jami’an tsaron ƙasa da fifikon su, bisa jami’an tsaron wata ƙabila. Barin ƙabilu su riqa kafa runduna don kare ƙabilanci ba zai haifar wa Nijeriya ɗa mai ido ba, domin ai ba manyan ƙabilun nan uku Hausa, Yoruba da Igbo ne ke zaune a ƙasar ba. Kowace jiha ta na da fiye da ƙabila ɗaya da ke cin kasuwa ɗaya da zuwa asibiti xaya da hawa kan titi ɗaya.

Tsawatawa da wuri na da muhimmanci don kar a wayi gari rundunar ƙabila ta fi ta gwamnati kayan aiki da albashi. Ko kuma rundunar ƙabila ta riƙa aiki tamkar ta ’yan sanda ta hanyar kamawa, tsarewa ko kafa dokar duk wanda ta kama sai ya samu mai belin sa kafin a sake shi.

Abun tambaya a nan, yanzu ga rundunar Ebube Agu ta Igbo, tuni dama an kafa Amotekun ta Yarbawa, ina wacce matasan Arewa suka kafa mai taken “Shege Ka Fasa” ko sun fasa ne? Haƙiƙa haɗin kan Nijeriya shi ne mafi a’ala, inda dukkan ɗan ƙasa zai zauna a duk gari ko yankin da ya ke so ba tare da fuskantar wani ƙalubale na bambancin ƙabilanci, addini ko wata gadara ba.