Marubuci tamkar wata mikiya ce a cikin al’umma – Lantana Ja’afar

*Ni ce mace ta farko da ta fara lashe gasar ‘Gusau Institute’- Lantana

Daga AISHA ASAS

A wannan makon jaridar Manhaja ta tattauna da Lantana Ja’afar, mace ta farko da ta taɓa cin gasar rubutun labarai ta cibiyar ‘Gusau Institute’ da suke shiryawa duk shekara. A wannan hirar masu karatu za su ji yadda Lantana ta fara rubutu da kuma ƙalubalen da ta fuskanta a harkar rubutun tare da wasu batutuwa da idan ku ka biyo mu za ku ji su:

Mu fara da jin tarihin ki.
Assalamu alaikum. Suna na Lantana Ja’afar, an haife ni a shekarar 1988 a cikin garin Jos Jihar Filato ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Na yi makarantar boko da islamiyya duk a cikin garin Jos. Yanzu haka ina zaune a garin Kaduna.

Wace shekara ki ka fara rubutu?
Na fara rubutu a shekarar 2009.

A fahimtar ki wane ne marubuci?
Marubuci dai tamkar wata mikiya ce a cikin al’umma, wanda ke hango nesa da kuma hasashen abinda ka iya faruwa a shekarun gaba.

Za mu iya sanin littattafan ki?
Na rubuta littattafai guda biyar, kamar: ‘Raihan’, da ‘Inuwa Ɗaya’, da ‘Haƙƙi ko Ƙaddara’, da ‘Matar Matafiyi’, sai na ƙarshen kuma ‘Illar Almajiranci’.

Wane littafi ki ka fara rubutawa?
‘Raihan’ shi ne littafin da na fara rubutawa.

Waɗanne nasarori ki ka samu a harkar rubutu?
Alhamdu lillah na samu nasarori da dama, domin ko wannan hirar da ake yi da ni tana ɗaya daga ciki.

Akwai ƙalubale?
Ƙalubalen da na fuskanta a shekarun baya ne, lokacin ina rubuta ‘script’ wato labarin fim, ya zamana idan na yi rubutu aka karɓa to sai a tuntuɓe ni sau ɗaya daga nan ba na sake jin komai daga gare su. Hakan kuma ba zai hana gobe in sake yin wani rubutun ba. Kuma ba na iya tuntuɓar su. Sai a shekarar 2009 tunani ya zo min in koma yin rubutun littafi. Da haka na juya wasu daga cikin zuwa littafi.

Me ya sa ake cewa marubutan baya sun fi na yanzu, shin me su ka fi su?
Saboda sun fi inganta rubutun su ta hanyar tsaftace shi, hakan ya sa ake girmama su tare da ganin ƙimar su a idon duniya fiye da wasu kaɗan daga cikin na yanzu.

Mene ne burin ki kan rubutu a nan gaba?
Burina rubutu ya zama hanyar sama wa al’umma mafita domin warware matsalolinsu na yau da kullum.

Cikin marubuta wace ce gwanarki?
Ba ni da zaɓi, domin ina kallon kowace marubuciya a matsayin gwana.

Wace shawara za ki ba wa marubuta da su ke tasowa?
Su kasance ma su yin nazari haɗi da bincike a kan abinda za su rubuta, su guje wa kalaman batsa ta yadda rubutun su zai zama mai ma’ana wanda al’umma za su amfana da shi.

Me ya janyo lalacewar kasuwar littattafai?
Abinda ya janyo lalacewar kasuwar littafi bai wuce zuwan wayar salula ba, wanda yanzu ta yawaita a hannun al’umma da kuma kafar sadarwar da yanar gizo-gizo (Internet) . Hakan ya haifar da koma baya sosai a cikin harkar littafi. A da sai ka cire kuɗi ka siya kafin ka karanta sai ya kasance a yanzu a na samu a kyauta ba tare da ka biya ko sisi ba.

Ta wani fannin kuma ta haifar da cigaba domin an samu ƙarin wasu sabbin marubuta waɗanda ba a san da su ba kuma suna da baiwar rubutu sai dai ba su san hanyar da za su bi ba, ba tare da an fitar da shi a matsayin littafi ba. Saboda ba kowa ke da kuɗin da zai buga littafi ba.

Ta ya ki ke ganin za a iya hana rubutun batsa?
Ta hanyar janyo su a jiki tare da yi masu nasiha, kuma muna musu addu’a Allah ya shirye su ya sa su gane illar da rubutun batsa ke haifarwa ga ƙannenmu da kuma ‘ya’yanmu.

Shin ana iya koyon rubutu?
Eh a na iyawa amma akwai wasu matakai da ya kamata abi.

Wane lokaci kika fi son yin rubutu?
Na fi yin rubutu cikin dare irin ƙarfe 2 zuwa huɗu gabanin asuba, saboda lokacin an fi samun natsuwa babu hayaniya.

Kin taɓa samun wata karramawa ta ɓangaren rubutu?
E na samu karramawa a shekarar 2020 na gasar ‘Gusau Institute’ wanda na zo ta biyu kuma mace ta farko da ta fara lashe gasar tun bayan da aka fara gudanarwa a duk shekara da labari na mai taken ‘Illar Almajiranci’.

Ko kina da iyali?
Ina da iyali bayan mijina akwai yaranmu guda huɗu: Abubakar, Maryam, Sinan da kuma Muhammad.

Wace shawara za ki ba wa marubuta?
Shawarar da zan bai wa marubuta ita ce su dinga jan sauran ‘yan’uwa marubuta ma su tasowa a jiki haɗi da ba su shawarwari ma su amfani yanda za su gudanar da ayyukan rubutun su ta hanyar rubuta abinda zai amfani al’umma har su zama madubin gobe da kuma nuna masu kuskuren su cikin hikima ba tare da ɓatanci ga junan su ba.

To madalla mun gode.
Ni ma ina godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *