Game da rikicin ganin jinjirin wata a Nijeriya

Daga ALIYU SAMBA

A kusan kowacce shekara ana samun taƙaddama tsakanin Musulmi kan bayyanar jinjirin watan Ramadana da kuma watan Shawwal. Musulmai a duniya suna saɓawa wajen ƙirgen azumi. A sanda wasu su ke ɗaya, wasu su na biyu, wasu kuma su na uku ga watan Ramadan.

Akwai buƙatar mu san cewa, dukkanmu na rayuwa ne a duniya guda (Earth), wacca take da wata guda ɗaya a sama, rashin rungumar ilimin kimiyya ya taimaka wajen faɗaɗar saɓanin nan a tsakanin mutane, domin ita ce hanya mai sauƙi da za a gane bayyanar hasken wata a sarari ko fakuwarsa.

Wasu na zaton wata fitowa yake daga matakin jaririn wata har ya yi ta girma har ya cika, sannan ya dawo mitsitsi har ya ɓace. Lamarin ba haka ya ke ba. Shi ya sa ake ta tafiya cikin ruɗani da kuma duhun kai.

Wata a bayanin kimiyya ba shi da haske a karan kansa; karva ya ke daga rana, kamar ka ce (absorbing) ya ke yayin da ya samu ɗosanen haske daga rana. Yana karɓar (Absorbing) hasken daidai gwargwadon sashensa da hasken ya riska. Shi ya sa ya ke somawa da kaɗan, ya yi ta faɗi har ya kai mustawar da zai cike a kewaye gaba dayan sa da haske, ya kuma riƙa raguwa har hasken ya daina fuskantar sa saboda kewayawar duniya.

Baya sake samun sabon ɗosane na haske sai bayan kwana 29 ko 30, daga wannan lokacin haskensa zai sake bayyana bayan fakuwarsa. Watan dai yana nan a sama, ba wai tafiya ya yi ba; hasken da ya ke karva ne babu, sai ya sake karva bayan kwana 29 ko 20, sannan ya sake bayyana.

Akwai abinda a kimiyyar taurari ake kira muqaranar rana da wata da kuma duniyarmu, wato ‘Earth’, shi a ke kira (Moon Conjunction). Duk wata wannan muqaranar tana afkuwa ne a lokaci guda kuma, a waje guda (constantly). Shi ne lokacin da wata ya ke samun haske daga rana da zai bayyana. Wata yana hagu da duniya, rana tana dama da duniya, duniya na tsakiya ta tare hasken rana daga wata. A daidai gaɓar da duniya ta ɗan gota yayin da take kewaye rana, ana samun hasken rana ya riski wani ɗan ɓangare na wata, a lokacin da ake samun wannan muƙarana babu wata ƙasa a duniya da za ta iya ganin hasken watan saboda ”illumination” ɗin 0% ne.

A lokacin da a ka samu wannan conjunction ɗin, shi ne lokacin da aka haifi jinjirin wata wanda kamawar sa ke kasancewa washe gari bayan ketowar alfijir. Sabon watan yana bayyana a ganshi idan anyi amfani da na’urori ƙara ganin abin nesa bayan wasu awanni a sanda rana ta faɗi, ana kuma iya ganin sa da idanu ba tare da na’ura ba a sanda ya kai awanni 18.

Haihuwar jinjirin watan Ramadan na 1442 ya auku da ƙarfe 3:32am na tsakar daren Lahadi agogon Nijeriya wayewar gari Litinin 12 ga Afrilu, 2021. Idan muka ɗauki jihar Kano dake Nigeria, Litinin 12 ga Afrilu, 2021 rana za ta faɗi da ƙarfe 6:38pm, kenan daga ”Conjuction” zuwa ”Newmoon”, sai muce da misalin ƙarfe 7:05pm sabon wata zai faɗi a yankin kano,wato minti 27 bayan faxuwar rana.

Lokacin faɗuwar rana a ran litinin ɗin sannan wata ya yi awa 15 da minti 6 da haihuwa (3:32am – 6:38pm). Kuma sannan hasken watan zai kai kashi 34 bisa 10,000. Zai yi wahala a iya ganin jinjirin watan da idon ɗan adam domin sai an samu aƙalla awa 18 kafin a iya ganin jinjirin wata da ido amma watan zai iya ganuwa da taimakon na’aura a awa 12 ko 13. Saboda haka a Nijeriya, ganin jinjirin watan Ramadan da magribar Litinin abu ne mai yiwuwa amma da taimakon na’urar hangen nesa.

Duk a saɓawar malamai a kan ingancin amfani da na’ura yayin kallon wata, amfani da na’ura ba zai canza haƙiƙar abinda ya ke faruwa ba, hasali ma tabbatar da abinda ya ke ƙasa ya ke. Tunda muna ƙarni na 21, kuma ƙarni ne da kimiyya ta wadata har ya zama komai yana tafiya ne a kimiyyance, addini ne, al’ada ne ko ɗabi’a, rungumar kimiyya zai taimaka matuƙa wajen daƙile rikici da saɓanin da a ke samu dan tabbatar da ganin jinjirin wata ko akasi.
Muna roƙon Allah ya fitar damu, Allah ya karɓi ibadun mu ya sanya mu cikin tsarkakkun bayin sa.