Yaushe Musulunci ya zo ƙasar Hausa?

Daga INJINIYA AHMED MUHAMMED DAURA

Fahimtar takamaiman lokacin da Musulunci ya fara zuwa ƙasar Hausa abu ne mawuyaci, saboda da farko dai babu wani tarihin da ya bayyana wata ƙungiya ko ƙabilar da ta kawo jihadi ko wani yaƙin musuluntar da Hausawa. Bisa ga wannan dalilin za a karɓi Musulunci ya fara zuwa ƙasar Hausa daga ɗaiɗaikun mutane, watau baƙin Musulmai.

A nazarin baƙin Musulmai ya bada damar fahimtar abokan hulɗar ƙasar Hausa, wanda ya ƙunshi mashahuriyar cinikayyar Hausa da tsallaken hamada (Trans-Saharan Trade) kamar sassan Aljeriya da Libya na yanzu zuwa Rum da Turai, tsallaken tekun maditareniya. Hanyoyin sun ƙunshi:-

  1. Kano (Hausa) zuwa Agades zuwa Ghadames, Ghat daTripoli. Agades ta faɗa mulkin Daular Songhai wajen shekarar 1515. Har yanzu ana aiki da wannan hanyar.
  2. Hanya ta biyu wadda har yanzu ita ma ana aiki da ita, ita ce Hausa zuwa Tambutu zuwa Sijilmassa a Maroko, haka zuwa Agadez da Ghadames. Tambutu ta fara kafuwa tun wajen 5th century BC amma sai farkon qarni na 11 ta fara shahara kan kasuwanci da ilimin Islama kuma musamman zuwan Mansa Musa wajen 1325. Tambutu ta shiga Daular Mali farkon ƙarni na 14 daga baya ta koma qarqashin daular Songhai a 1468 kafin Maroko su qwace ta a shekarar 1591.
  3. Hanya ta ukku ita ce Hausa zuwa tsohuwar Barno zuwa Masar. Tsohuwar Barno na nufin daular Sayf (Saifawa) ta Njimi, arewacin Tabkin Chadi. Akwai wata tsohuwar hanya kuma babba watau Njimi zuwa Marzuƙ a sashen Fezzan wadda ta riƙi cinikayya tsakanin ƙasashen Africa ta Yamma (Songhai, da Hausa) da Africa ta tsakiya (Kanem-Barno) da sauran su zuwa Rom wajen 5th century BC zuwa 5th century AD. Akwai kuma hanyar cinikayya Njimi zuwa Masar. Daular Kanem-Barnu a ƙarƙashin ƙabilar Kanembu sun kafa hedkwatar su a Njimi kuma tun wajen 1300 AD su ka mulki Marzuƙ. Akwai tabbataccen bayanin Musuluntar Mai Umme (Ibn Abdul jalil) a ƙarshen ƙarni na 11.

To waɗannan hanyoyin ne da kuma al’ummar da Hausa ta yi hulɗa da su a cinikayya tun kafin Musulunci, kuma kasuwanci ya wanzu tun 500 BC zuwa 500 AD. Abu ne tabbatacce cewa wannan hulɗar ce ta bada damar zuwan Musulmai ‘yan kasuwa zuwa Hausa. Ta ina Musulunci ya fara zuwa (Tambutu? Agadas, ko Njimi?) shaƙaƙar magana ce.

A bayanan malaman baya (kamar su Malam Adamu Nama’aji da Nasiru Kabara) suna ganin Musulunci ya daɗe da zuwa Hausa tun zamanin Sahabbai. Fatihul Ilmu ya bayyana mana akwai zaton Sahabai sun zo Hausa kuma ana zaton kaburburan su a Tcafe. Abu ne mawuyaci a ture waɗannan bayanan kai tsaye. Magana mai gamsarwa, ɗaiɗaikun baqin Musulmai sun fara yaɗa Musulunci a ƙasar Hausa kuma ɗaiɗaikun mutane sun karɓi Musulunci.

Malam Laminu ya bayyana Sarkin Kano Ali Yaji (1349-1385) shine Sarkin Kano na farko da ya Musulunta ta hannun Wangarawa daga Mali. Bisa ga wannan shaidar dole mu karbi cewa Musulunci ya fara zama ‘state religion’ tsakar qarni na 14. Wannan ya nuna Kanem-Barnu ta riga Hausa karɓar Musulunci a ‘state religion’ da kamar shekara 300. Amma wannan bai ture maganar farkon zuwan musukunci ƙasar Hausa daga Njimi ba, haka daga Agadas ko daga Tambutu ba. Amma mawuyaci ne a karɓi farkon shigowar Musulunci ƙasar Hausa daga Ngazagarmu.

Mu na iya cewa shekara 300 lokaci ne mai tsawo, amma Njimi ita ma ai ta daxe ba ta karɓi Musulunci ba daga Masar, ganin Musulunci ya isa Masar cikin karni na 7 amma Sarakunan Njimi (Kanenbu) ba su karɓi Musulunci ba daga Masar tsawon shekaru 400 duk da hulɗar da su ke da Masar. Wannan ya nuna Wangarawa sun kawo Musilunci Kano babu mamaki ganin horon da Almurabbad’un (Almurabit) su ka yi musu, na yaɗa addini da yaƙi. Ma’ana Wangarawa sun horu a yaɗa addinin Musulunci saboda ba cikin ruwan sanyi suka samu Musuluncin ba. Ƙarin shaidar wannan batun shi ne ganin yawan Larabawan Maroko (kamar su Baba Ahmed a Zaria) da su ka zo Hausa musamman domin yaɗa addini sun fi Larabawan Masar yawa, horon Almurabbaɗun ya kawo hakan.

Wasu manazarta wataƙila sun kalli kusanci, saukin hulɗa, da yawan hulɗa, ya sa suka samu sauqin cewa ƙabilar Kanembu ne daga Njimi, su ka fara kawo Musulunci ƙasar Hausa. Shekara 300 ana huldar cinikayya ba karamin lokaci ba ne da za a kasa samun koyon al’ada ta addini ba. Ko me kenan, ina ganin Kanem-Barno ba ta riƙi jihadi ba na yaɗa Musulunci musamman ganin yadda su ka mamaye ƙasashen Hausa babu maganar addini face biyan kuɗin ƙasa (haraji). Mu dubi tarin ƙabilun da su ke cikin Daular Barno tun a wancan lokacin waxanda ba Musulmai ba ne, kuma Barno ba ta yaƙe su ba ko ta matsa musu su Musulunta ba, saɓanin aƙidar Almurabbaɗun.

Amma malaman Barno sun bada gagarumar gudummawa a havaka addini a Hausa. Daga baya a jihadin Fulani, Barno ta bada goyon bayan yaqar Sarakunan Hausa saboda ba su riqi addini sosai ba.
Sai ku yi haƙuri da gaganiyata, abin da nazarina ya ba ni kenan.

Injiniya Ahmed shine Galadiman Daura a Jihar Katsina.