Ra’ayi

Shin ya dace a taya daliban Kankara murnar sace su?

Shin ya dace a taya daliban Kankara murnar sace su?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYAWannan tambaya ce da ni marubuci na yi wa kai kuma na ke son ba da amsa da kai na. Da farko ma na so kai tsaye na radawa rubutun nan suna "Ina taya daliban Kankara murnar sace su!." Gaskiya zai iya yin ma'ana idan a ka ce sace 'yan makarantar nan da duk alamu ke nuna 'ya'yan talakawa ne ya jawo hankalin duniya ya koma kan su. Hatta mutan kudancin Najeriya sun ciccije sun koyi yanda a ke furta Kankara a jihar Katsina. Yanzu ka na shiga yanar gizo ka rubuta Kan...a injin bincike za…
Read More
Ciyaman Nda-Isaiah: Ba rabo da gwani ba…

Ciyaman Nda-Isaiah: Ba rabo da gwani ba…

Daga IBRAHIM SHEME Tun a ranar farko da na fara haduwa da Mista Sam Nda-Isaiah, cikin mintuna kadan, ya dauke ni aiki. A lokacin ya na fafutikar neman wani qwararre wanda zai nada editan sabuwar jaridar sa mai suna LEADERSHIP, har wani tsohon dan jarida ya ba shi suna na. Rannan ya je Sakkwato domin nuna wa Gwamna Attahiru Bafarawa jaridar tasa, sai su ka hadu da wani aboki na a ofishin da su ke jira a yi wa kowannen su iso, domin ba tafiyar su daya ba, ba su ma san juna ba. Su na labari, sai abokin nawa…
Read More
Abota ita ce auren zamani

Abota ita ce auren zamani

Tare da AISHATU GIDADO IDRIS Zai iya yiwuwa ku kan yi wani tunani irin nawa, na cewar yawancin lokaci idan mutane ba su samu dama ko sa'ar auren wadanda su ke so ba, su kan samu aqalla wadanda su su ka fi alheri a gare su. Haka abin yake! Domin sau da yawa wasu su kan yi qorafin cewa rayuwa ta juya masu baya idan su ka rasa abin da su ka fi da so. Ba haka ba ne kuma. Tabbas, ana yawan auren soyayya, amma kuma ana yawan aure na sa'a, dace ko auren sakamako a kan rasa wani…
Read More
Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Tare da Nasiru Adamu El-Hikaya Muhawar yawan xaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina da a ka sace ta zo qarshe tun da an gano yaran ko na ce an samu dukkan yaran har an ma miqa su ga iyayen su. Ba wata baquwar al’ada ba ce a Nijeriya a ba da labari da ya wuce kima ko ya gaza kima musamman hakan ya fi dogara ne ga yadda labarin ya shafi mai ba da shi. Hakanan a lokacin da gwamnati ko jami’an tsaro kan yi qoqarin rage kaifin labari don ta yiwu ya jawo tashin hankali ko zubar da…
Read More
Rikicin Addini: Salafiyya, Tijjaniya da Kadiriyya

Rikicin Addini: Salafiyya, Tijjaniya da Kadiriyya

Daga FATUHU MUSTAPHA A cikin makon da ya gabata ne, wasu manyan malaman salafiyya, wadanda suka hada da: Sheikh Muhammad bin Abdulwahab da Sheikh Dr. Mansur Sokkoto, suka yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kama shehin malamin nan na darikar Qadiriya: Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara. Wannan rigima dai ta samo asali ne, tun bayan da shi sheikh Abduljabbar ya fara wani tafsiri da ya kira Jauful Faraa. Tafsirin da mafiya akasarin malaman darikar ta Salafiya ke ganin ya saba qa’ida, ya na kuma wuce gona da iri. Wannan rigingimu dai ba yau aka fara fama da su, a…
Read More
Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Daga Ibrahim Sheme Alhaji Abdulqadir Balarabe Musa mutum ne “wani iri”. Ba a saba ganin irin sa ba. Mutum ne wanda idan an yi Yamma sai ya yi Gabas, idan kuma an yi Kudu shi sai ya yi Arewa. Wasu na kallon sa a matsayin murdadde, ba a yi tanqwasa shi a tattaunawar siyasa; wasu kuma na yi masa kallon mai sauqin kai, mai rungumar talakawa.Ko ma ta wace fuska mutum ya kalle shi, babu wanda zai ce maka ba nagartacce ba ne. Hatta mutanen da ya rayu ya na adawa da manufofin su sun yi ittifaqi da cewa ‘Bala…
Read More