Deputy Editor

35 Posts
Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Daga jaridar Manhaja Kwamishinoni masu wakiltar jihohi 36 na kasar nan hada da birnin tarayya Abuja, tare da Hukumar Kyautata Da'ar Ma'aikata ta Kasa (FCC) sun rubuta takardar korafi a kan shugabar hukumar FCC Dr. Muheeba Fraida Dankaka zuwa ga Hukumar Yaki da Rashawa da Laifuka Masu Alaka da Rashawa (ICPC) bisa zarginta da yin ba daidai ba da matsayinta. Takardar korafin mai dauke da kwanan wata 18/1/2021 wadda ta sami sa hannun Sir Augustine Wokocha da Abdul Wasiu Bawa-Allah, ta nuna yadda shugabar FCC ta mamaye komai na hukumar sannan ta karbe ayyukan kwamishinonin tana mika wa daraktocinta tare…
Read More
FCMB ya matse kaimi wajen tallafa wa kananan ‘yan kasuwa

FCMB ya matse kaimi wajen tallafa wa kananan ‘yan kasuwa

Daga jaridar Manhaja Kawo yanzu, bankin FCMB ya ci gaba da kokarin da yake yi na tallafa wa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa a fadin kasa. Idan dai za a iya tunawa, a kwanan nan ne aka zabi bakin FCMB a matsayin bakin da ya zarce kowane bakin a yankin Afirka mu'amala da 'yan kasuwa kanana da matsakaitansu. Lamarin da ya karfafa wa bankin gwiwa wajen tallafa wa mata masu kananan sana'o'i ta hanyar shirin nan nasa mai taken "SheVenture". Shirin SheVenture, shiri ne da bankin ya samar don bunkasa kananan 'yan kasuwa mata da kuma masu shirin soma kasuwanci,…
Read More
‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

Daga jaridar Manhaja 'Yan-bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Paikoro da ke Jihar Neja, inda suka hallaka mutum shida tare da yin garkuwa da mutum biyar sannan suka jikkata sama da mutum 20. Bayanai daga jihar sun nuna 'yan-bindigar sun soma ta'addacinsu ne daga Asabar da ta gabata zuwa washegari Lahadi da rana. Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da harin ya shafa mai suna Abubakar Azaido, ya shaida wa Manhaja ta tarho cewa sama da mutum 20 da suka jikkata a harin aka kai babbar asibitin Kafin Koro. Ya ce, akalla mutum 3000 ne suka tsere…
Read More
Miyetti Allah ta koka kan halin da Fulani ke ciki a Oyo

Miyetti Allah ta koka kan halin da Fulani ke ciki a Oyo

Daga jaridar Manhaja Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo Ibrahim Abubakar Jiji, ya yi korafin halin da ake ciki mambobinsu na zaman dar-dar ne a jihar biyo bayan harin da wasu matasa da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa Sarkin Fulani Salihu Abdulkadir a yankin Igangan, a Juma’ar da ta gabata. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Ondo ta bai wa Fulani makiyaya a jihar wa’adin kwana 7 a kan su fice mata daga dazuzzukanta. Gwamnatin Jihar Ondo ta ci gaba da kallon matakin da ta dauka a matsayin abin…
Read More
Za a yi zaben gwamnan Anambara ran 6 ga Nuwamba – INEC

Za a yi zaben gwamnan Anambara ran 6 ga Nuwamba – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 za a yi zaben gwamnan Jihar Anambara. Hukumar ta bayyana jadawalin ranar zaben da abubuwan da za a aiwatar ne a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Talata a Abuja. Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na hukumar, Mista Festus Okoye, wanda ya bada sanarwar, ya ce hukumar ta yi wani zama a ranar Talata inda ta tattauna kan zaben na Anambara. A cewar sa, za a yi zabubbukan share fage tare da warware duk wani sabani da ka iya…
Read More
Zaɓe: INEC za ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha kafin 2023

Zaɓe: INEC za ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha kafin 2023

Daga WAKILIN MU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta na nan ta na sake nazari kan hanyoyin fasaha da ta ke amfani da su a wajen zaɓuɓɓuka, da nufin shigo da waɗansu sababbi waɗanda za su inganta zaɓuɓɓukan da za a yi daga yanzu zuwa shekara ta 2023. Daraktan Wayar da kan Masu Zaɓe da kuma Sashen Yaɗa Labarai na INEC (VEP), Mista Nick Dazang, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taron ƙara wa juna sani na sashen nasu mai taken “Sake Duban Kundin Wayar da kan Masu Zaɓe na Ƙasa" wanda aka yi a garin…
Read More
Sadiya Umar Farouq na so a kula da naƙasassun Nijeriya kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen

Sadiya Umar Farouq na so a kula da naƙasassun Nijeriya kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa da naƙasassun da ke Nijeriya hanyoyin da za su riƙa bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin ƙasa da na mota da makarantu. Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Naƙasassu ta Ƙasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Hajiya Sadiya ta gode wa Shugaban Ƙasa saboda yadda ya amsa kiran naƙasassun…
Read More
Shugaban INEC ya buƙaci Majalisar Tarayya ta dage kan kwaskwarimar dokar zaɓe

Shugaban INEC ya buƙaci Majalisar Tarayya ta dage kan kwaskwarimar dokar zaɓe

Daga WAKILIN MU Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga 'yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la'akari da jam'iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Zaɓe garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zaɓe a ƙasar nan. Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwar ƙwararru na yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma'a. Kwamitin Haɗin Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Zaɓe da Al'amuran Zaɓe ne ya shirya taron tare da tallafin…
Read More