Ya kamata gwamnati ta yaƙi yunwa a ƙasa

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke bai wa dillalan da ke shigo da shi cikin ƙasa, rayuwar ’yan Nijeriya ta canja, musamman sakamakon ƙaruwar farashin mai wanda ya ta’azzara farashin kusan duk wani abu da talaka ke mu’amala da shi a rayuwarsa. Kama daga farashin kuɗin motar haya zuwa farashin abinci a kasuwanni, kuɗin makarantar yara da sauran al’amura na yau da kullum.

Gwamnati tun a wancan lokacin ta yi ta ƙoƙarin ganin ta ɓullo da wasu tsare-tsare da za su sauƙaƙa halin da ake ciki, don a samu sassauci, amma sai shirin nata ya gamu da tasgaro. Domin kuwa halin mu na ’yan Nijeriya ya sa duk shirin da gwamnati ta yi ya tashi a banza, saboda son zuciya da rashin gaskiya da wasu suka sa cikin tsarin.

Jihohi da dama sun kasa raba abincin da shugaban ƙasa ya ba su kuɗaɗen da za su saya su raba da yawansu ya kai Naira biliyan 20. Amma sai aka koma rabon ’yan siyasa, sai wane da wane yake samu, shi ma ɗin ba yadda ya kamata ba. A maimakon buhun shinkafa, wasu sai mudu-mudu suka riƙa samu, da ƙullin gwangwanin man gyaɗa da taliya guda ɗaya. Abin da ko abincin yini ba zai ishi mutum da iyalinsa ba.

Muna sane da abin fallasar da Hukumar Bincike Kan Laifukan Almundahana ta EFCC ta bankaɗo na abubuwan rashin gaskiyar da tsohuwar Ministar Ma’aikatar Jinkai da Yaƙi da Talauci Betta Edu da takwararta ta lokacin gwamnatin Buhari, Sadiya Umar Farouk suka aikata, inda su da wasu muqarraban gwamnati suka yi sama da faɗi da wasu kuɗaɗe da ya kamata a ce an yi amfani da su ne don tallafawa raunanan al’ummar qasa da ke cikin halin ha’ula’i da fatara.

Abin da ya kawo har sai da gwamnati ta soke shirin bakiɗaya, tare da gudanar da bincike. Kodayake kawo yanzu an ce tsofaffin ministocin suna ba da haɗin kai a binciken da ake yi, har ma sun fara dawo da wasu kuɗaɗen, tare da fallasa wasu daga cikin makusantan fadar shugaban ƙasa da suke da hannu wajen wannan kashe-mu-raba da ake zargin an yi.

Binciken masana na nuni da cewa, iyalai da dama na rayuwa cikin yunwa da kwana ba tare da cin abinci ba. Yara da dama ba sa iya zuwa makaranta, masu fama da ciwon zuciya da hawan jini na ƙaruwa, saboda matsaloli masu nasaba da yawan tunani da damuwa. Ayyukan laifi da shaye-shaye na ƙaruwa, ’yan kasuwa na fama da rashin ciniki, da tsadar shigo da kayayyaki, sakamakon karyewar darajar Naira.

Tun bayan da wasu gungun mata da matasa a Jihar Neja suka fito kan titunan garin Minna suna zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa da yunwa da ake fama da ita, sauran ’yan Nijeriya ke ta bayyana goyon bayansu kan wannan abu da mutanen Neja suka yi, domin kowa a ƙasar nan na jin jiki sosai, musamman talakawa masu ƙaramin ƙarfi.

Wannan ana ganin shi ya harzuƙa mata masu sana’ar gasa gurasa a Kano da wasu jama’ar gari su ma suka ɗauki kwalaye suna zanga-zangar lumana domin bayyana damuwa game tsadar farashin fulawa da suka ce ya yi tashin gwauron zabi. A hankali wannan zanga-zanga ta cigaba da yaɗuwa zuwa wasu garuruwa, inda aka samu rahoton mata a Jihar Kogi ma sun fito titunan garin Lokoja suna bayyana damuwa game da wannan hali da talakawa suka samu kansu a ciki.

Hauwa Shehu wata marubuciya kuma ’yar kasuwa a Jihar Kano ta bayyana takaicinta game da yadda al’amura ke cigaba da taɓarɓarewa a ƙasar nan, ganin yadda rayuwa ke ƙara tsada, harkokin kasuwanci a ɓangaren maza da mata ke shiga cikin wani yanayi na rashin tabbas. Talakawa sun koma fafutukar neman na abinci, an manta da duk sauran buƙatu, abin da za a sa a bakin salati kawai ake nema shi ma ba ya samuwa yadda ake so. Cin abinci sau uku a gida ya fara zama tarihi a gidaje da dama.

Ummulkairi Abdulmumin Iliyasu wata malamar makaranta mai taimakawa da shawarwari kan zamantakewa a garin Jos ta koka sosai game da halin da mata da magidanta suka samu kansu a ciki a wannan lokaci. Tana mai cewa, matsalolin zamantakewar aure sai ƙaruwa suke yi, sakamakon yadda mazaje da dama ba sa iya sauke haƙƙoƙin da ke kansu saboda kasuwanci da harkokinsu sun tsaya, ba a samun ciniki, ɗan abin da suke bayarwa a gida na cefane babu inda yake kaiwa. Saboda tsadar suga yanzu hatta ruwan bunu na shayi da ake iya dumama ciki da shi, ba ya samuwa. A ganinta wannan matsala ƙirƙirarriya ce da ya kamata gwamnati ta tashi tsaye don ganin ta magance ta.

Kodayake hukumomi na musanta cewa halin da ake ciki a ƙasar nan bai kai yadda talakawa suke ta kururutawa ba, domin kuwa ’yan Nijeriya sun fi wasu ƙasashe da dama yin rayuwa mai sauki. Yayin da suke zargin ƙungiyoyin mata da na jama’a sa suka gudanar da zanga-zangar lumana a matsayin masu neman tayar da hankali da yi wa gwamnati zagon ƙasa.

Har ma mun samu rahotanni kan cewa jami’an tsaro sun kama waɗanda suka shirya zanga zangar Minna da Kano, saboda suna zargin abin da suka yi zai iya tunzura sauran ’yan ƙasa har a samu rashin tsaro da tashin hankali a wasu wurare.

Gaskiya ne, ba ma goyon bayan a samu lalacewar doka da oda ko tavarvarewar tsaro a ƙasa wanda zai iya sake mayar da hannun agogo baya, da jefa jama’a cikin halin qunci. Amma ya kamata gwamnati ta sani cewa ’yan Nijeriya na da ‘yancin shirya zanga-zangar lumana, don tunatar da shugabanni halin da talakawa suka samu kansu a ciki. Kuma hakkin hukuma ne ta basu tsaro da kariya don komai ya tafi cikin lumana.

Ba ma fatan ganin zanga-zanga ta cigaba a wasu garuruwa, amma maganin hakan shi ne mu ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa don shawo kan matsalar, yadda hankalin ’yan Nijeriya zai kwanta, kuma su gamsu cewa lallai gwamnati da gaske take yi za ta share musu hawaye.

Mun ga wani rahoto da ya fito daga fadar shugaban ƙasa na nuni da cewa, shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin lallai a hanzarta samar da tallafin abinci ga ’yan Nijeriya, domin magance matsalar ƙarancin abinci da tsadar rayuwa. Har ma mun ji gwamnatin tarayya ta bakin Ministan watsa labarai da wayar da kan ’yan ƙasa Muhammad Idris tana bayyana matuqar damuwarta game da halin da ’yan Nijeriya ke ciki, yayin da ta ce tana shirin yin duk abin da ya kamata don kawo musu sauƙin rayuwa a ƙasa bakiɗaya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, daga cikin matakan gaggawar da gwamnatin tarayya ta ɗauka har da ba da umarnin fitar da kayan abinci daga rumbunan gwamnati domin a rabawa talakawwan ƙasa, da kuma karya farashin kayan abinci a kasuwanni. Sannan kuma gwamnati ta ce za ta yi zama da ƙungiyoyin ’yan kasuwa da masu kamfanoni don a tattauna hanyoyin da za a samu sauƙin farashin kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida.

Da kuma samar da tallafin kuɗi ga masu samar da abinci a ƙasa, don a rage farashi a kuma samar da wadatar abinci a kasuwanni. Har wa yau kuma gwamnati za ta gudanar da bincike domin gano masu ɓoye kayan abinci da tsawwala farashin kayayyakin masarufi don haifar da tsadar kayan a kasuwanni.

Ko babu komai dai za mu ce gwamnati ta yi hovvasa, amma ba a nan gizo yake saƙar ba. Lallai ne a sa ido domin tabbatar da ganin tsarin da aka yi ya yi aiki, kuma waɗanda aka ɗora kan gudanar da ayyukan bincike da samar da sassauci a kasuwanni su ma sun yi abin da ya kamata.

Lallai a yi duk mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen wannan masifa da ta ke neman durƙusar da ƙasar nan, da jefa ta cikin halin da ba a san me zai faru ba.