‘Yan bindiga sun kashe mutum 4 ciki har da ‘yan sanda, sun yi awon gaba da mutum 40 a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kashe wasu jami’an ‘yan sanda biyu haɗi da wasu mutum biyu kana suka yi awon gaba da aƙalla mutum 40 a wani hari da suka kai garin Kasuwa-Daji da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda.

Mazauna yankin sun ce, ‘yan fashin dajin sun kai harin ne da safiyar ranar Talata tare da harba bindiga a iska don razana jama’a.

Wani mai suna Abubakar Kaura ya faɗa wa jaridar News Point Nigeria cewa, ‘yan bindigar su mamaye garin ne ɗauke da manyan makamai ciki har da bindigar kakkaɓo jirgin sama.

Ya ƙara da cewa, ɓarayin sun shiga gidan tsohon Ciyaman ɗin ƙungiyar NURTW, Hamisu Kasuwar-Daji inda suka ɗauki ɗaya daga cikin matansa da jikokinsa.

Haka nan, ya ce sun shiga ofishin ‘yan sandan da ke kusa da gidan tsohon shugaban na NURTW inda suka ƙwace bindigoginsu sannan suka hallaka jami’ai biyu.

Har wa yau, wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce, ‘yan bindigar sun kashe wasu mutum biyu yayin harin.

Tare kuma da cewa, sun kwashi kimanin mutum 40 bayan da suka shiga gida-gida suna fitar da jama’a.

Kakakin ‘yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin ga majiyarmu, sai dai bai faɗi adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin ba.