Daga JOHN D WADA a Lafia
Shugaban ƙaramar hukumar Keffi Dr. Idris Mohammed Damagani da rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa sun musanta wata jita-jitar cewa jama’a sun rasa rayukan su da samun raunuka sakamakon wani mummunar farmaki da wasu ‘yan bindiga dake sace mutane suka kai unguwar Jaba dake ƙaramar hukumar Keffi.
A zargin dai, wakilin mu ya ruwaito cewa ance an raunata mutane da dama wasu an kashe kuma an sace mutane biyu duk a lokacin harin.
Sai dai daga bisani a cikin wasu sanarwa daban-daban, Dr. Damagani da ’yan sandan jihar Nasarawa sun buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu kada su yarda da rahotannin da za su iya haifar da firgici.
Dr. Damagani ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin.
“Nan take na sanar da sojoji da ’yan sanda kuma suka shiga yankin cikin gaggawa. Amma lokacin da suka iso wajen masu garkuwa da mutanen sun riga sun gudu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro suna aiki tuƙuru wajen gano da ceto wanda aka sacen a yanzu haka.
Shugaban ya jaddada cewa babu rahoton raunuka ko mutuwar da ta faru a lokacin lamarin.
“A matsayina na babban jami’in tsaro na ƙaramar hukumar ba mu natsu ba. Muna aiki tare da jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin tabbatar da an ceto wanda aka sace lafiya,” in ji shi.
Dr. Damagani ya kuma tabbatar wa mazauna Keffi tsaronsu tare da alwashin cigaba da haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a fadin yankin.
Haka nan a nasa ɓangaren jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa SP Ramhan Nansel ya tabbatar da bayanin shugaban ƙaramar hukumar inda ya ce bincike kan lamarin na cigaba da gudana a yanzu kuma ya musanta jita-jitar mutuwa da raunuka da aka danganta da harina anguwan Jaban shima.
“Babu wanda ya samu rauni balle a ce an mutu. ’yan bindigar sun shiga gida ɗaya ne kawai a anguwan Jaba a Keffi suka sace mace ɗaya. Sun shiga ta taga ne zuwa gidan da daddare,” SP Nansel ya tabbatar.
A ƙarshe shugaban ƙaramar hukumar da ’yan sanda sun roƙi mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa yaɗa bayanai marasa inganci waɗanda za su iya haifar da tsoro da ruɗani a tsakanin jama’a.
