Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa ya nemi a maida wa’adin Shugaban Ƙasa da gwamnoni zuwa shekara shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele ya bayyana aniyarsa ta gabatar da ƙudirin doka da ke neman a sauya wa’adin mulkin shugaban ƙasa da gwamnoni zuwa shekara shida ga kowane wa’adi.

Sanata Bamidele ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa na Abuja, ranar Litinin.

A cewarsa, tsarin wa’adi guda na shekaru shida zai iya rage yawan siyasar neman tazarce da kuma bai wa shugabanni damar mayar da hankali kan aiwatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaban kasa ba tare da damuwar sake neman zabe ba.

Idan ƙudirin ya samu amincewar majalisar dokokin ƙasa tare da cika sharuɗɗan gyaran kundin tsarin mulki, zai kawo gagarumin sauyi a tsarin mulkin Nijeriya inda a halin yanzu shugaban ƙasa da gwamnoni ke yin shekaru huɗu a wa’adi guda tare da damar sake tsayawa takara karo na biyu.

Sai dai har yanzu kudirin yana matakin shiri, wanda kuma zai buƙaci tattaunawa da goyon bayan ‘yan majalisa da jihohi kafin ya shuga cikin doka a hukumance.

By Babaji

Leave a Reply