Ministan Labarai zai jagoranci babban taron NUJ kan tsaro a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ‘Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) ta sanar da cewa Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ne zai jagoranci babban taronta na kwana biyu akan tsaro da za a gudanar a Abuja.

Shugabar kwamitin shirya taron, Abimbola Oyetunde a wata sanarwa a Abuja ta bayyana haka, idna ya ce taron tsaron zai ƙunshi haɗin-gwiwa tsakanin ‘yan jarida da hukumomin tsaro domin masalaha ɗorewa al’amuran ci-gaban ƙasa.

Ta ce, an tsara gudanar da zaman ne a ranar 18 ga Yuni, 2026 mai taken “Media and Security Agencies as Partners in Nation Building”.

A cewarta, zaman babban fage ne na tattaunawa akan yadda ‘yan jarida da jami’an tsaro za su yi aiki tare bisa inganci domin ba wa ƙasar kariya da kuma gudanar da lamuran labarai yayin rikice-rikice.

Haka kuma, ta ce taron zai samu halartar manyan jami’an gwamnati, jagororin tsaro, editoci, ƙungiyoyin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki daga sassan Nijeriya.

Sanarwar ta ce, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu sune baƙi na musamman a taron.

Kazalika, ta ce wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke cigaba da fuskantar ƙalubalen tsaro, yaɗa labaran bogi da ƙamarin matsi da al’umma suka tsinci kansu a ciki.

By Babaji

Leave a Reply